📜📜📜
SIFFOFIN MACE TAGARI📜📜📜
Shaikhul Islam Ibn Taimiyya yace"mace ta gari tana kasancewa tare da miji nagari tsawon shekaru masu yawa.
Ita ce jindadin sa Wanda manzon Allah(saw) ya fada a cikin hadithi yace"ita duniya wani Dan jindadi/amfani ne kuma mafi alkhairin amafani/jindadin ta ita ce mace mumina wadda idan ka kalle ta sai ta burgeka, idan kabata umarni sai ta yi maka da'a, idan kafita kabarta zata kiyaye ka ga kanta(ba zata ci amarnarka ba).
Itace wadda manzon Allah yayi umarni da ita a cikin zancen sa lokacin da muhajiruna suka tambaye shi:wace dukiya ya kamata murika? Sai yace: "harshe mai yawan ambaton Allah, da zuciya mai yawan godiya, da MACE TAGARI mai taimakon dayanku bisa imani"
(📚Timidhi ya Ruwaito shi saga Salim ibn Abilja'ad daga Sauban).
Ita ce wadda kauna/soyayya da tausayi yake tabbata da ita kamar yanda Allah (SWT) ya fada a cikin Alqr'an, radadin rabuwa da ita yafi tsanani sama da na mutuwa,wani lakacin ma yafi tsanani sama da kariyar arziki, yafi tsanani sama da barin wurin zama(gida) musamman idan akwai alaqa a tsakanin su (zumunta) ko kuma suna da 'ya 'ya a tsakanin su wadan da rabuwar zata jefasu cikin yanayi na kunci da tozarta da kuma gurbacewar dabi'un su"
(📚majmu'ul fatawa 35/299)
🕌🕌COMMITTEE FOR SOCIAL MEDIA MASJID ABU HURAIRA TSAFE ZAMFARA STATE (07039140450)
No comments:
Post a Comment