Wednesday, 6 December 2017

ZUMUNTA A MUSULUNCI

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*_TATTARAWA:_*

*MALAM SANI LIMAN (ABU HURAIRAH) TSAFE*

_Fitowa Na biyu(002)_

```Bisimillahir-rahmanir-raheem, Alhamdulillah, bayan bayanin da ya gabata na ABUBUWAN DA WANNAN RUBUTU ya kunsa, yanzu zamu fada cikin bayanin Abu na farko.

MECECE ZUMUNTA???

  Ibn athir yana cewa zumunta tana nufin taimakawa yan uwa na bangaren dangantaka da sarakuta da kula da halayen SU koda kuwa suna zaune a wurare masu nisa koda kuma suna munana maka. A daya bangaren kuma, yanke zumunta yana nufin kishiyar abubuwan da aka ambata a baya.

DA WANE ABU AKE SADAR DA ZUMUNTA???

Ana sadar da zumunta da al'amura masu yawa kamar; Ziyartarsu, bibiyar halayensu, tambaya game dasu, aika masu da kyaututtuka da kuma saukar da kowannensu a matsayin da ya dace dashi(wato su yan uwan da ya kamata a sadar da zumunta garesu), sannan kuma ana Sadar da zumunta da bada sadaka ga fakirai daga cikin su da tausasama mawadatan su da girmama manyansu da kuma tausayama kananan su da masu rauninsu da yawan tambayar halin da suke ciki, ziyartar su da kanka ko ka aika wasika ko kayi amfani da wayar salula.

    Mafi girman abunda ake sadar da zumunta dashi shine; mutum yayi kwadayin kiransu((yan uwansa) zuwa ga shiriya ya umurcesu da aiki mai kyau ya kuma hana su aikata miyagun ayyuka.

   Haka nan zumunta bata da wani kayyadadden lokaci da aka kayyade don sadar da ita. Duk abunda al'ada ingantatta ta tabbatar a matsayin Sada zumunta, ana daukarshi a matsayin haka. Haka kuma duk abunda al'ada ingantatta ta tabbatar a matsayin yanke zumunta to ana daukarshi a matsayin haka.

   Zumunta tana bambanta gwargwadon kusanci da matsayi na wadanda ake sadar da zumuntar zuwa garesu, zumuncin da yake tsakanin uba da dansa ya sha bam-ban da Dan uwa na nesa.

   Bugu da kari, zumunta tana banbanta gwargwadon halayen da su wadanda za'a sadarmawa suke ciki, kamar sadar da zumunta ga marar lafiya da mabukaci ta bambanta da sadarwa ga waninsu. Haka kuma sadarwa ga babba ta banbanta da ta karami

    Haka nan sadar da zumunta yana banbanta ta fuskar bagire, Wanda yake zaune a cikin gari ya banbanta da Wanda yake zaune a wani gari wajen ziyartar shi da tambayar halinda yake ciki, da yimasa sallama ko aika mashi da sakonni.

Zamu tsaya a nan, sai wani lokaci idan Allah ya kaimu insha Allahu.

Allah ya bamu ikon sadar da zumunta gwargwadon iko Amiin.

A gaba zamuyi bayani akan FALALAR SADAR DA ZUMUNTA insha Allahu.

Allah yayi mana jagoranci.

Copyright©
MASJID ABU HURAIRAH TSAFE SOCIAL MEDIA```
+2348064734911

No comments: