Friday, 8 December 2017

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN ADALCI.

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA
UKKU DAKE TSAFE
ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon
Limamin Massallaci
Jumu'a Na Ukku Dake
Unguwar Area2, Tsafe
Sheik Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #ADALCI Godiya ta
tabbata ga
ALLAH Wanda yayi
umarni Da adalci yayi
hani ga cuta koda kuwa
ga kafurai ne, Na shaida
cewa babu Annabi Muhammad Bawan
ALLAH Ne kuma
manzon sa.
Yan uwa Musulmi muji
tsoron ALLAH Wanda
yayi umarni da ADALCI Yana fada a cikin
suratul nahali ''YANA
UMARNI DA ADALCI
YA HANA ZALUNCI
Hakama ALLAH
Madaukakin sarki yana cewa A cikin suratul
hujirat ''KUYI ADALCI
GA JUNNANKU''
Yaku Yan uwa musulmi
yin adalci tsakanin mu
mafita tare da mafi chan chanta ga rayuwar mu,
A cikin magabatan
malamai wani daga cikin
su yana cewa ADALCI
Shine asa komai dai dai
inda ya dace, Babban malamin tauhidin
nan Ibn taimiyah yace
karshen zalunci shine
tabewa, Karshen
ADALCI Shine aza
komai inda yake tare da aza komai inda
yakamata.
kusani ALLAH Baya
taimakon Azzulumai!
Imam muslim ya ruwaito
a Cikin Wani hadisin yana cewa Manzo
sallallahu Alaihi
wassalam yana cewa
''MASU ADALCI
SUNE A SAMAN
HASUMIYA MAI HASKE A RANAR
KIYAMA''
Yaku yan Uwa musulunci
ku kasance masu adalci
tsakanin matan ku.
Manzo sallallahu alaihi wassalam yace mutun
uku
zasu shiga aljannah
1-Shugaba mai
adalci:Wanda yake
adalci tsakanin
talakawan sa, yake sauke nauyin da ke kansa
yaji
tsoron ALLAH
Madaukakin sarki
2-Mai taushin zuciya
:wanda yake wadata da
abunda ALLAH Ya bashi ya sauke nauyin
iyalin sa, ya shayar da su
halal duk da yana da
matsi
3-Mai kame kai:mai
kame kai daga duk abunda ALLAH Yayi
masa iyaka dashi
Yaku yan Uwa musulmi
manzo tsira ya fada a
cikin hadisi cewa Mutun
Bakwai ALLAH Zai sanya su cikin inuwa
ranar da babu wata sai
ita a ciki akwai
''SHUGABA MAI
ADALCI''
Shi adalci nau'i nau'i ne 1-Adalci ga rayuwa
2-Yima wasu adalci
Kamar yadda ALLAH
Madaukakin sarki ya ce
''LALLAI ALLAH NB
UMARNI KU BADA HAKKI GA MASU
SHI KU TSAIDA
GASKIYA''
Alkali yayi adalci ga
wadanda yake wa shari'a
yayi adalci tsakanin bangori guda biyu
ALLAH Madaukakin
sarki Yana cewa ''KAYI
HUKUNCI
TSAKANIN
MUTANE DA ADALCI KADA KABI SON
RAYUWAR KA.
3-Adalci tsakanin yaya,
sau da yawa zaka ga
wasu na nuna banbanci
tsakanin yan wancan dakin dana wancan
yakamata muji tsoron
ALLAH Yaku yan uwa
musulmi
A wani hadisi wani
mutun yazo wajen Manzo Sallallallahu yace
''WANNAN
DANDANA NE ZAN
BASHI KYAUTA INA
SO KAYI SHAIDA SAI
MANZO SALLALLAHU
ALAIHI WASSALAM
YACE KANA DA
WASU YAYAN YA CE
EH, SAI YACE
KABASU KYAUTAR SAI YACE A'A Daga
nan MANZO
SALLALLAHU
ALAIHI WASSALAM
YACE BANA SHAIDA
AKAN ZALUNCI'' 3-ADALCI Ga magana
ALLAH Yana cewa
''IDAN ZAKUYI
MAGANA KUYI
ADALCI KODA
(ADALCIN) ZATA KASANCE KAN YAN
UWANKU''
4-ADALCI Tsakanin
mata yakamata magida
suyi adalci domin ya
tabbata a hadisi cewa ''RANAR KIYAMA
WANI ZAI TASHI
BANGAREN JIKINSA
YA SHANYE (Wannan
mai nuna son zuciya ne ga
iyalinsa) Hakama ALLAH
Madaukakin sarki yana
cewa ''IN KUNJI
TSORON BAKU
ADALCI TO KU AURI
DAYA'' 5-ADALCI Ga makiya
yin adalci ga makiya
shima nau'i ne na adalci
Yaku yan uwa musulmi
kusani adalci shine ya
tsaida sama da kasa, Hakama Dazarar babu
adalci to za'a shiga
musiba
Musulunci yana cike da
adalci kamar yadda
wannan ayar ke nunawa ''KALMOMIN
UBANGIJI SUN CIKA
DA ADALCI ''
Yaku yan uwa musulmi
tillas ne kuma wajibi
muyi adalci ga kawunan mu, da matanmu da yan
uwa mu, kai harma da
makiyan mu
Ya ALLAH Muna
rokonka da girman ka da
matsayin ka bamu ikon yin adalci
Yaku yan uwa musulmi
kusani ADALCI
Matattarar tsoron
ALLAH Babban Gida a
ADALCI Shine Tauhidi hakama babban zalunci
shine shirka da ALLAH!
Ya ALLAH Muna
rokonka da girman ka da
matsayin ka bamu ikon
yin adalci,Ka daukaka musulunci da musulmai,
ka kaskanta kafurci da
kafurai kayi garin mu
Albarka Ka kyautata
Karshen mv
Subhakalla humma waabiihammdik ash hadu
an la'ila ha illa antta
astagfirka wa'atubu
ilaik
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE
ZAMFARA
19/05/1438
17/02/2017.

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN HALAYE NA KWARAI

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #HALAYE_NA_KWARAI
Bayan Godiyb Ga ALLAH Masarrafin Lamura Da
Yabo Tare Da Kirari Ga Mafi Soyuwa A Wurin
ALLAH Madaukakin Sarki, Wato Annabin Rahama
Tsira Da Amincin ALLAH Suka, Kuma Sunan Kan
Tabbata A Garesa,
Yaku Yan Uwa Musulmi Kusani Musulunci Addini
Ne, Da Yake Da Tsari Kammlallen!
Kyawawan Halayen Ko Kuma Ince Dabi'u, Na
Wani Babban Jigo Na Cikar Mutun Musulmi,
Mumini!
Kamar Yadda Hadisi Ya Tabbatar ''KYAKYAWAN
HALAYEN NA DAGA CIKIN CIKAR ADDININ DAN
ADAM''
Haka Zalika Rayuwar Manzo S.A.W Itace Ci
Kikakkiyar Abun Koyi Kamar Yadda Aya Daga
Cikin Alqur'ani Ta Tabbatar ''KUMA KAI (ANNABI)
KANA HALAYE MASU GIRMA''!
Yaku Yan Uwa Musulmi Kusani Musulmi Baya
Zama Cikakken Mumini Sai Ya Zama Mai
Kyakkyawan Halaye,
An Tambayi Imamul Hasanul Basary Minene
Kyawawan Halaye Sai Yace Abubuwa Uku Ne,
Na Daya Akwai Kiyaye Addini Sau Da Kafa,
Na Biyu Akwai Yawan Kyauta Da Sadaqa,
Na Uku Akwai Sakin Fuska.
Sannan Kuma An Tambayi Imamul Baihaqi Cewa
Minene Halaye Na Kwarai?, Sai Yace Ai Halayen
Kwarai Sune Abubuwa Guda Uku...
Na Daya Kiyaye Haram
Na Biyu Kiyaye Cin Halal
Na Uku Sakin Fuska Ga Kowa.
Yan Uwa Musulmi Akwai Kuma Abubuwan Dake
Sanya Halaye Mummuna Su Baiyana A Garesa
Gasu Kamar Haka,
1-ROWA
2-SHAN TOKA
3-BIJEREWA ZAMA DA AL'UMMA
4-YAWAN SABON ALLAH
5-YAWAN SURUTU
6-KAZANTA
7-GIRMAN KAI (RAWANIN TSIYA)
Wadanda Abubuwan Duk Suna Mayar Da Rayuwar
Dan Adam, Da Halayen Sa Su Zamo Munana,
Dan Haka Yaku Yan Uwa Musulmi Mu Tabbbar
Mun Kiyaye Wadannan Abubuwa Dan Gyara
Halayen Mu.
A Wani Hadisi Yana Cewa ''KYAWAWAN HALAYE
SUNE MAFI RINJAYE A CIKIN MIZANI''
Dan Haka Yan Uwa Sai Mu Kiyaye Aikata
Munaman Halaye, Da Kuma Aikata Kyawawan
Halaye Dan Tsira Ranar Da Dukiya Da Yaya Basu
Da Amfani
ALHAMDULILLAH
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM

©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
+2347064282182

14/Rabi'u Alkhair (04)/1438
13/01/2017.

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN MAI ZAN AIKATA LOKACIN SANYI.

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #LOKACHIN_SANYI
_DA_ABUBUWAN_DA_YAKAMATA_AKIYA
YE_DA_KULA_DASU
Bayan Sallama Ga Yan Uwa Musulmi, Da Salati
Ga Abul Kasim S.A.W, Da Yabo Ga ALLAH S.W.T,
Sheik Yafara Da Cewa Yaku Yan Uwa Musulmi
Kusani Addini Ya Tanadi Komai, Wanda Yazamo
Jagora Garemu Da Kuma Hanya Wace Idan Muka
Kiyaye Zata Kaimu Ga Hanyar Tsira Gobe
Kiyama,
TSARKI Wani Na'u Ne, Na Addinin Musulunci
Wanda Idan Babu Tsarki Babu Alwallah,
ALWALLAH Kuma Mabudi Ga Ibadah, Musamman
Ibadah Ta Sallah,
Yadda Ake ALWALLAH Shine
Fara Yin Bismilla, Sannan Wake Hannuwa Zuwa
Guiwar Hannu, Sannan Wake Fuska Gaba
Dayanta Tun Daga Mafita Gashin Kai Har Zuwa
Kasan Gemu, Sau Ukku, Sannan Sai Wanke
Hannu Na Dama Zuwa Karshen Guiwar Hannun
Na Dama Sau Ukku, Sannan Kayi Haka Sau Ukku
Ga Hannun Hagu, Sai Shafar Kai Daga Mafitar
Gashi Zuwa Kasan Kai, Jewa Da Dawowa,
Sannan Kwalkwalar Kunne, Daga Karshe Sai
Wanke Kafafu, Farawa Da Kafar Dama, Ka
Tsittsefe ta Gaba Daya, Hakama Kafar Hagu!
MANZO S.A.W YACE DUK WANDA YAYI IRIN
WANNAN ALWALLAR AN GAFARTA MASA
ZUNUBANSA''
ALWALLAH Nada Wani Tasiri A Fuskar Dan
Adam Musulmi, Idan Musulmi Ya Tashi Ranar
Alkiyama Gabobin ALWALLAR Sa Zasu Dinga
Haskakawa, Daga Nesa Zaka Ganesa, ALLAH
Yasanya Mu A Cikin Su,
Yaku Yan Uwa Musulmi Hakika Muna Cikin Wani
Yanayi Na Sanyi, Wanda Amfani Da Ruwa Yana
Da Nauyi Sosai,
''MANZO S.A.W YACE ALWALLAH A LOKACHIN
SANYI TAFI LADA BISA GA LOKACHIN ZAFI''
Haka Zalika ALLAH Madaukakin Sarki Yace
''MUSULUNCI NA NUFIN SAUKI GA AL'UMMA BA
TSANANI BA''
A Wannan Lokachin Akwai Wadanda Idan Sukayi
Amfani Da Ruwan Sanyi Zai Zama Illa Garesu,
A Musulunche Babu Laifi Ka Dafa Ruwan Zafi,
Kayi Amfani Dasu Dan Alwallah, Domin Addini
Sauki Garai,
MANZO S.A.W Yana Amfani Da Wani Kyalle,
Bayan Yayi Alwallah Yana Goge Ruwa,
Kunga Babu Laifi Mu Goge Ruwa Bayan Anyi
Alwallah,
Yan Uwa Musulmi Mu Kyautata Alwallar Mu, A
Wannan Lokachin Dan Samun Karin Lada Ga
ALLAH Madaukakin Sarki,
Mu Daure Kuma Mu Jure Wallahi Idan Muka
Kiyaye Zamuyi Mamaki A Ranar Da Dukiya Da
Yaya Basu Da Amfani!
Idan Akace Kaza Sunnah Ne To Murike Da
Gasken Gasken, Wani Abunda Da Yakara Burgeni
Da Musulunci Shine Zaka Aikata Wani Abun Kai
Kanka Bakasan Yana Da Lada Ba, Amma Idan Ka
Aikata Zaka Samu Lada,
Mu Godewa ALLAH Dayayo Mu Musulmi, Sannan
A cikin Al'ummar Annabi, Da Kuma Yayo Mu
Ahlissunnah,
ALHAMDULILLAH
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM
©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
+2347064282182
30/Rabi'u Auwal/1438
30/12/2016.

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN HARAMCIN MURNAR SABUWAR SHEKARA.

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallacin Jumu'a Na
Ukku Dake Area II, Tsafe Sheik Sani
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan
#KAUCEWA_KOYI_DA_YAHUDAWA_TARE
_KAUCEWA_MURNAR_SABUWAR_SHEKARA
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Haka Kuma ALLAH S.W,T
Hakika Addinin Musulunci Shine Cikakken Addini
Kuma Karbarben A Wurin ALLAH Madaukakin
Sarki, Haqiqa Addinin Musulunci Yana Dokoki Da
Kowane Musulmi Yazama Wajibi Yakiyaye Su,
Musulunci Yayi Mana Gata, Ya Bamu Yanci Kuma
Ya Gindiya Mana Sharudda Wadanda Aka
Haramta Mana,
Musulunci Yana Da Watanni Har Guda Goma Sha
Biyu Kamar Yadda ALLAH Yafada Mana, A Cikin
Alqu'arni Mai Tsarki Cewa ''LALLAI WATANNI A
WURIN ALLAH SUNE GUDA GOMA SHA BIYU
DAGA CIKIN SU AKWAI HUDU MAFIYA ALBARKA
KADA KU CUCI KAWUNAN KU A CIKINSU''
Yan Uwa Musulmi Idan Muka Lura Da Wannan
Ayar Ta Nuna Mana Cewa Watanni Musulunci
Sha Biyu Ne, Sun Fara Daga Muharram Zuwa
Zhul Hijja,
Addinin Musulunci Kammalallen Addini Ne Kamar
Yadda Alqur'ani Yafada ''A YAU NA KAMMALA
MAKU ADDININKU NA TABBATAR MAKU DA
NI'IMAR KU(MUSULUNCI) NA WAJABTA MAKU
ADDININ MUSULUNCI YA ZAMA ADDININ''
Mai Ahdari Ya Fada Cewa BAI HALLATA GA
MUTUN YA AIKATA WANI AIKI FACE YASAN
HUKUNCIN ALLAH AKAN WANNAN AIKIN''
Addinin Musulunci Yazo Da Komai Kuskure
Jahilcine Wani Ya Fada Cewa Babu Siyasa A
Addini,
Musulunci Nada Komai,
A Wannan Lokaci Da Muke Ciki Arna Na Shirin
Fara Chrismat!
Wanda Abun Ban Takaici Zakaga Musulmai Wai
Suna Taya Arna Murnar Zagayowa Wannan Rana,
Ita Ranar Christmat Rana Ce Da Aka Haifi Annabi
Isah A.S
Shehul Islam Ibn Taimiyah Yafada Cewa
Hawwariyun Wato Wadanda Suka Taya Annabi
Isah Isar Da Sako Basayin Wannan Bikin, Kunga
Idan Kun Lura Suma Kansu Bidi'a Ce Suka Qago
Wa, Kansu,
Bayan Haka Akwai Wani Kuskure Da Zai
Jagoranci Fitar Mutun Musulunci Wato NEW
YEAR
A Wajen Musulunci Bikin NEW YEAR Haramunne,
A Wajen Arna Kuwa Suna Murna Haihuwar
Annabi Isah, Wanda Suke Dangantawa Wai
Dandan ALLAH A uzu Billahi Iyaza, Ameen,
Kunga Kenan Idan Ka Taya Arna Murnar NEW
YEAR Ko Kuma Christmat Kamar Ka Taya Su
Wancan Shirkar Dana Gaza Sake Rubutawa, A
Uzubillah,
Yaku Yan Uwa Musulmi Idan Muka Girmama
Addinin Mu Hakika Duniya Zata Girmama Shi,
Idan Muka Wofintar Dashi Kazalika Duniya!
Yana Da Kyau Mu Fara Gabatar Da Kwanan Wata
n Musulunci Kafin Nasu,
Yakamata Idan Yazama Wajibi Muyi Amfani Da
Sunayen Watanni Mu Fada Da Hausa, Misali
January Sai Muce Watan Daya,
Bawaye Bane Kuma Ba Gwaninta Bane Wai Ace
Mu Duk Daya, Ai Duk ALLAH Muke Bautawa
Wanda Wannan Kuskure Ne, Basason Mu Kuma
Basason Addinmu Ta Yaya Za'a Ce Mana Wai
Daya Muke?
Baka Tabajin Arne Ya Fadi Hijra Musulunci Ba,
Yaku Yan Uwa Musulmi Duk Abunda Aka Baku
Naci Ko Na Sanyawa Da Sunan Christmat
Haramun Ne,
Ku Tuna Suna Danganta ALLAH Dai Haihuwa Fa
A'uzubillah, ALLAH Kuma Ya Karyatasu A Wajaje
Da Dama Kamar Su Suratul Ikhlas Da Sauransu,
Hakama ALLAH Ya Fada Cewa'' SAMA NA SON
TSAGEWA KASA NA SON TSAGEWA DUWATSU
NA SHIRIN TSEREWA TA DALILIN DANGANTA
WA ALLAH DANDA''
''TA YAYA AKE DANGANTAWA ALLAH DA? BAYA
TABA YIWUWA ALLAH YA RIKI DA'''
'
'
Mu Kiyaye Yan Uwa Idan Kwadai Da Wulakanci,
Hakama Inda Kwadaiyi Akwai Jahannama
Manzo S.A.W Yace ''WANDA YAYI KAMA DA
MUTANE HAKIKA YANA CIKINSU''
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM

©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
+2347064282182

23/Rabi'u Auwal/1438
23/12/2016.

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN DOGARO GA ALLAH.

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan
Muhimmancin #DOGARO_GA_ALLAH
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Haka Kuma ALLAH S.W,T Ya Halicci Kome Da
Kowa Hakika Shine Maqagin Komai Da Kowa,
ALLAH S.W.T Cikin Hikimar Sa Ya Halicci Dan
Adam, Da Aljani Da Dabbobi Da Tsuntsaye, Da
Ruwa Da Iska, Da Abunda Na Kawo, Da Wanda
Ban Kawo Ba, Ya Halicci Abunda Muka Sani Ya
halicci Wanda Bamu Sani Ba,
ALLAH S.W.T Ya Qagi Wata Abu Da Ake Kira
Dogaro Ga Rai,
Hausawa Na Cewa Dogaro Ga ALLAH Jari,
Kwarai Kuwa Wannan Maganar Haka Take,
''ALLAH S.W.T Yace WANDA YAJI TSORON
ALLAH ZAI BASHI MAFITA KUMA ZAI
ARZIRTASA TA HANYAR DA BAYA TSAMMANI''
Yan Uwa Musulmi DOGARA GA ALLAH Ba Yana
Nufin Wai Kayi Kwance Yajira Wai ALLAH Zai
Kawo Masa Taimako, A'a Katashi Ka Nema Ka
Dogara ALLAH WALLAHI ALLAH Zai Taimakeki,
Akwai Abunda Ake Kira Musabbab, Ma'ana
Sanadi,
Manzo S.A.W Ya Fada Cikin Wani Hadisi Idan
Annabi S.A.W Yace ''TSUNTSAYE ZASU KWANA
BASU DA KOMAI AMMA ZASU KAI MARAICE
CIKIN SU, A CIKE''
Wannan Hadisin Ya Nuna Mana Cewa Tabbas
Idan Ka Dogara Ga ALLAH Zai Baka Mafita,
Kuma Ya Nuna Mana Cewa Ba'a Kwance Ashe
Wai ALLAH Kawo Mani,
Idan Muka Koma Kan Magana Ta Sanadi, Tana
Nufin Ka Tashi Ka Nema, Mai Da Kayanka Ga
ALLAH, Yarda Babu Mai Kawo Hasara Ko Riba
Sai ALLAH,
Kissar Annabi Yunusa Tazo A Cikin Alqur'ani Mai
Girma Cewa Lokachin Da KIFI YA HADEYASA YA
KOMA GA ALLAH INDA YAKAMA FADIN ''TSARKI
YA TABBATA GAREKA KAI KADAI, TSARKI YA
TABBATAR MAKA LALLAI NI NA ZALUNCI
KAINA''
Kunga Wannan Kisar Ta Nuna Mana Yadda
Annabi Yunusa Ya Maida Dogaron ALLAH Kuma
ALLAH Yabasa Mafita Ta Hanyar Fitar Dashi
Daga Bakin Kifin, Amma Duk Da Haka Yana Iya
Kokarinsa,
Yaku Yan Uwa Musulmi Idan Mukayi La'akari Da
Halin Da Muke Ciki A Wannan Zamanin Tabbas
Mafi Yawancin Mu, Mun Rasa Dogaro Ga ALLAH.
Yan Uwa Musulmi Wasu Daga Cikin Mu, Na Dora
Ko Kuma Aza Halin Da Muke Ciki Da Shugaban
Kasa Buhari!
Wanda Wannan Kuskure, Wallahi Sahabban
Annabi Sallallahu Alaihi Wasalam Sun Shiga Hali
Wanda Yafi Nanu Nesa Nesa, Ba Kusa Ba, Amma
Sun Maida Kayansu Ga ALLAH Kuma Yafitar
Dasu A Matsin Da Suka Tsinci Kansu,
A Yakin Badar Musulmi Sun Fito Su Dari Ukku Da
Sitti Wata Ruwaya, Arna Kuma Sun Kai Dubu Da
Wani Abu A Wata Ruwaya, Musulmi Qalilan Ne
Ke Saman Dawakai, Amma ALLAH S.W.T Ya
Basu Nasara Akan Kafurai Suna Ragargazasu
Suka Kore Su,
Duk Irin Hali Na Dadi, Ko Akasin Haka Mu Daina
Dangantawa Ga Mani Mu Maida Lamuran Mu Ga
ALLAH
YAN UWA DA FATAR KUN WUNI LAFIYA
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM

©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA

18/Rabi'u Auwal/1438
18/12/2016.

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN ZUMUNTA A MUSULUNCI.

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallacin Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani
Liman(ABU HURAIRA)

Yayi Hudubar Sane Akan
Muhimmancin Rike # ZUMUNTA_KO_KUMA
_SADA_ZUMUNTA
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Haka Kuma ALLAH S.W,T Ya Wajabta Sada
Zumunta Tsakanin Yan Uwa Jini,
Sada ZUMUNTA Dai Bawai Kawai Ya Takaita Ga
Fada Cewa Wane Dan Uwa Nane, A.a, Dole Ne
Anga Wannan Kalma A Zahiri, Da Kuma
Aiwatarwa A Aikace,
Yaku Yan Uwa Musulmi Kusani Ana SADA
ZUMUNTA Ta Hanyoyi, Da Dama, Daga Cikin
Akwai Kyautatawa Ta Hamyar Basu Wani Ihsani,
Sannan Akwai Sakin Fuska, Akwai Jawo Su A
Jiki, Anan Akwai Gagarumar Matsala!
Sau Da Yawa Zakaga Wani Yana Kyautatawa Yan
Uwansa, Amma Baya Son Su Dinga Ziyatar Sa,
Ziyara Kuma Daya Ce, Daga Ciki Ko Kuma Itace
Ginshiki Wato PILLAR, Ta Zumunci!
Yan Uwa Musulmi Mu Jure Mu Yaki Shaidan A
Tsakanin Mu, Domin Shaidani Shine Babban
Wanda Ke Sanya Mana Dogon Lokaci Idan
Mukayi Niyar Zuwa Ziyara, Zakaga Kayi Niyar
Zuwa Ziyara Amma Shaidan L.A Sai Yace Maka
A.a Bari Ka Kara Samun Kudi, Wanda Babu
Ranar Dazaka Same Su, Muddin Kana Sanya
Rana Irin Haka!
Malamai Magada Annabawa Sunyi Mana Nasihohi
Kamar Haka,
1.DUK WANDA YA YANKE ZUMUNCI GAREKA TO
KA SADAR MASA
2.DUK MAI FUSHI DAKAI KAYI MASA MAGANA
KODA BAYA AMSAWA
3.YAWAN ZIYARA YANA KARA DANKON
ZUMUNTA
4.IDAN MA HAR BAKA SAMU DAMAR ZIYARAR
BA, TO KIRAN SU TA WAYA MA ZAI TAIMAKA
AMMA BAI WADATAR BA
5.A KALLA KA KIRA YAN UWANKA KODA SAU
DAYA NE BAYAN KWANAKI GOMA
6.JURIYA TARE DA HAKURI,TARE DA GANI
AMMA KAYI KAMAR BAKA GANI BA
Hadisi Yazo Daga Manzon Tsira Cewa ZUMUNTA
Tana Addu'a Kullun Tana Cewa YA ALLAH DUK
WANDA YASADA NI, KASADA SHI DA
RAHAMARKA, DUK WANDA YA KATSE NI, KA
KATSE SHI DAGA RAHAMARKA
Daga Karshe Muna Fatar Yan Uwa Zamu Gyara
Zumuntar Mu, Tsakanin Mu Dan Yan Uwan Mu.
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN BIYAYYA GA IYAYE

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Masallacin Jumu'a Na
Ukku Dake  Area II Tsafe Sheik Sani
Liman(ABU HURAIRAH)
Yayi Hudubar Sane Akan
Muhimmancin #BIYAYYA_GA_IYAYE
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Hakan Tasa Ya Umurci Bayin Sa , Dayimai
Biyayya,
Sai Kuma Yasanya Biyayya Ga Iyaye Tare Da
Tasa, Yin Biyayya Ga Iyaye Dole Dole Dole Ne,
Ana Yiwa Iyaye Biyayya Akowane Halli in Banda
idan suka umarce ka da Sabon ALLAH''
Ana Fifita yiwa uwa biyayya fiye da uba kamar
yadda daya daga cikin hadisan annabin rahama,
ya nuna mana,
Zakalika annabi rahama yafada a wani hadisin
cewa YAR DAR ALLAH TANA TARE DA YARDAR
IYAYE HAKAMA FUSHIN ALLAH YANA TARE DA
FUSHIN IYAYE''
Akwai Wani nauyi wanda iyaye keda shi kan
mutun idan sun rassu , daga cikin wadannan
nauyin akwai, Yi Masu Addu'a Bayan Basu
duniya, Sada zumuntar da suke sadawa idan su
nan, girmama yan uwansu da abonkasu, da dai
saurasu,
Yaku Yan Uwa Musulmi Ku Sani duk wanda ya
mutu iyayensa basajin dadin sa, to TABBAS
BAYA SHIGA
Yaku yan uwa kunji wata babbar magana!
Daga karshe ina fatar kowa zai kara gyara
zamantakewar sa da iyayens, wanda kuma nasa
basanan zai bi waccan hadisin daya gabata,
muna rokon ALLAH Yagafarta masu gaba daya,
Nima Mahaifina Ya Rassu Ina roko masa gafarar
ALLAH,Game da kurakurar daya gabatar a
rayuwar sa,
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM

©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA

11/Safar/1438

11/11/2016.