Friday, 8 December 2017

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN ZUMUNTA A MUSULUNCI.

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallacin Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani
Liman(ABU HURAIRA)

Yayi Hudubar Sane Akan
Muhimmancin Rike # ZUMUNTA_KO_KUMA
_SADA_ZUMUNTA
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Haka Kuma ALLAH S.W,T Ya Wajabta Sada
Zumunta Tsakanin Yan Uwa Jini,
Sada ZUMUNTA Dai Bawai Kawai Ya Takaita Ga
Fada Cewa Wane Dan Uwa Nane, A.a, Dole Ne
Anga Wannan Kalma A Zahiri, Da Kuma
Aiwatarwa A Aikace,
Yaku Yan Uwa Musulmi Kusani Ana SADA
ZUMUNTA Ta Hanyoyi, Da Dama, Daga Cikin
Akwai Kyautatawa Ta Hamyar Basu Wani Ihsani,
Sannan Akwai Sakin Fuska, Akwai Jawo Su A
Jiki, Anan Akwai Gagarumar Matsala!
Sau Da Yawa Zakaga Wani Yana Kyautatawa Yan
Uwansa, Amma Baya Son Su Dinga Ziyatar Sa,
Ziyara Kuma Daya Ce, Daga Ciki Ko Kuma Itace
Ginshiki Wato PILLAR, Ta Zumunci!
Yan Uwa Musulmi Mu Jure Mu Yaki Shaidan A
Tsakanin Mu, Domin Shaidani Shine Babban
Wanda Ke Sanya Mana Dogon Lokaci Idan
Mukayi Niyar Zuwa Ziyara, Zakaga Kayi Niyar
Zuwa Ziyara Amma Shaidan L.A Sai Yace Maka
A.a Bari Ka Kara Samun Kudi, Wanda Babu
Ranar Dazaka Same Su, Muddin Kana Sanya
Rana Irin Haka!
Malamai Magada Annabawa Sunyi Mana Nasihohi
Kamar Haka,
1.DUK WANDA YA YANKE ZUMUNCI GAREKA TO
KA SADAR MASA
2.DUK MAI FUSHI DAKAI KAYI MASA MAGANA
KODA BAYA AMSAWA
3.YAWAN ZIYARA YANA KARA DANKON
ZUMUNTA
4.IDAN MA HAR BAKA SAMU DAMAR ZIYARAR
BA, TO KIRAN SU TA WAYA MA ZAI TAIMAKA
AMMA BAI WADATAR BA
5.A KALLA KA KIRA YAN UWANKA KODA SAU
DAYA NE BAYAN KWANAKI GOMA
6.JURIYA TARE DA HAKURI,TARE DA GANI
AMMA KAYI KAMAR BAKA GANI BA
Hadisi Yazo Daga Manzon Tsira Cewa ZUMUNTA
Tana Addu'a Kullun Tana Cewa YA ALLAH DUK
WANDA YASADA NI, KASADA SHI DA
RAHAMARKA, DUK WANDA YA KATSE NI, KA
KATSE SHI DAGA RAHAMARKA
Daga Karshe Muna Fatar Yan Uwa Zamu Gyara
Zumuntar Mu, Tsakanin Mu Dan Yan Uwan Mu.
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi

HUDUBAR JUMA'AH MAI TAKEN BIYAYYA GA IYAYE

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Masallacin Jumu'a Na
Ukku Dake  Area II Tsafe Sheik Sani
Liman(ABU HURAIRAH)
Yayi Hudubar Sane Akan
Muhimmancin #BIYAYYA_GA_IYAYE
Bayan Yin Salati ga Manzon Tsira Sallallahu
Alaihi Wassalam, Da Kuma Yin Yabo ga ALLAH
Madaukakin Sarki''
Sai Sheik Sani Ya Fara Da Cewa Yaku Yan Uwa
Ku Sani ALLAH Ya Halicci Bayi Sa Ne Don Kawai
Mu Bauta Mashi Ashe Kuwa Babu Wani Dalili
Dazai Sa Muyi Sakaci A Fagen Bautawa Mai''
Hakan Tasa Ya Umurci Bayin Sa , Dayimai
Biyayya,
Sai Kuma Yasanya Biyayya Ga Iyaye Tare Da
Tasa, Yin Biyayya Ga Iyaye Dole Dole Dole Ne,
Ana Yiwa Iyaye Biyayya Akowane Halli in Banda
idan suka umarce ka da Sabon ALLAH''
Ana Fifita yiwa uwa biyayya fiye da uba kamar
yadda daya daga cikin hadisan annabin rahama,
ya nuna mana,
Zakalika annabi rahama yafada a wani hadisin
cewa YAR DAR ALLAH TANA TARE DA YARDAR
IYAYE HAKAMA FUSHIN ALLAH YANA TARE DA
FUSHIN IYAYE''
Akwai Wani nauyi wanda iyaye keda shi kan
mutun idan sun rassu , daga cikin wadannan
nauyin akwai, Yi Masu Addu'a Bayan Basu
duniya, Sada zumuntar da suke sadawa idan su
nan, girmama yan uwansu da abonkasu, da dai
saurasu,
Yaku Yan Uwa Musulmi Ku Sani duk wanda ya
mutu iyayensa basajin dadin sa, to TABBAS
BAYA SHIGA
Yaku yan uwa kunji wata babbar magana!
Daga karshe ina fatar kowa zai kara gyara
zamantakewar sa da iyayens, wanda kuma nasa
basanan zai bi waccan hadisin daya gabata,
muna rokon ALLAH Yagafarta masu gaba daya,
Nima Mahaifina Ya Rassu Ina roko masa gafarar
ALLAH,Game da kurakurar daya gabatar a
rayuwar sa,
NA SADAUKAR DA WANNAN RUBUTUN DA
NIYAR ALLAH YAKAI LADARSA GA MAHAIFINA,
Da Fatar Zamuyi Salati Ga Wanda Na Bada
Fansa Raina Data Iyayena A gareshi
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA
ALI MUHAMMADIN WASSALIM

©®DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA

11/Safar/1438

11/11/2016.

Wednesday, 6 December 2017

HANI KAN TSAGA JIKI DAGA LITTAFAN SHI'AH

HANI KAN DUKAN JIKI KO TSAGA TUFA KO
IHOCE-IHOCE YAYIN WATA MUSIBA, BAFA CIKIN
LITATTAFAN SUNNAH KURUM YAZOBA, YA
TABBATA HATTA CIKIN LITATTAFAN
SHI'A.........

Daga: Malam Abdurrazak Uba Musa

Bari indan fitoda koda dozin dayane daga cikin
ruwayoyin :
ﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ . ‏( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ١٢ /٩١٥
ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /١٠٣ )
Ihoce-ihoce na daga aikin jahiliyya.
ﻧﻬﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﺮﻧﺔ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻤﺼﻴﺒﺔ ﻭﻧﻬﻰ ﻋﻦ
ﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ ﻭﺍﻻﺳﺘﻤﺎﻉ ﺇﻟﻴﻬﺎ . ‏( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ )
Annabi yayi hani ga daga sauti yayin kuka,da
ihoce-ihoce,da kuma jiyarda kukan yayin faruwar
musiba.
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏( ﺻﻮﺗﺎﻥ
ﻣﻠﻌﻮﻧﺎﻥ ﻳﺒﻐﻀﻬﻤﺎ ﺍﻟﻠﻪ ،ﺃﻋﻮﺍﻝ ﻋﻨﺪ ﻣﺼﻴﺒﺔ ﻭﺻﻮﺕ ﻋﻨﺪ
ﻧﻌﻤﺔ، ﻳﻌﻨﻲ " ﺍﻟﻨﻮﺡ ﻭﺍﻟﻐﻨﺎﺀ ‏) ‏( ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ
ﻟﻠﻨﻮﺭﻱ . ١/١٤٤ ، ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /١٠١ )
Sautika 2 ababen tsinewane,Allah baya sansu,
daga murya da kuka yayin wata musiba,da daga
murya yayin farinciki.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﻻ ﻳﺼﻠﺢ ﺍﻟﺼﻴﺎﺡ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ، ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻻ ﻳﻌﺮﻓﻮﻥ .
‏(ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣/٢٢٦ ، ﺍﻟﻮﺍﻓﻲ ١٢ /٨٨ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٦ )
Bai kyautuba kururuwa yayin mutuwa,bakuma ta
kamata ba,Amma kash 'yan Shi'a basu saniba.
}ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺇﻟﻰ ﺭﻓﺎﻋﺔ ﺑﻦ ﺷﺪﺍﺩ :{
ﻭﺇﻳﺎﻙ ﻭﺍﻟﻨﻮﺡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﺑﺒﻠﺪ ﻳﻜﻮﻥ ﺻﻮﺕ ﻟﻚ ﺑﻪ
ﺳﻠﻄﺎﻥ
‏( ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Rubutun sayyidi Ali zuwa ga rifa'a, yace dashi:-
Kashedinka ga kuka yayin mutuwa.
ﻋﻦ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ :
ﻣﻦ ﺿﺮﺏ ﻳﺪﻩ ﻋﻞ ﻓﺨﺬﻩ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻤﺼﻴﺒﺔ ﺣﺒﻂ ﺃﺟﺮﻩ .
‏( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٤ )
Duk Wanda ya doki cinyarsa da hannunsa yayin
musiba,to ya rushe ladansa.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﺍﻟﺼﻴﺎﺡ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ ﺗﺸﻖ ﺍﻟﺜﻴﺎﺏ .
‏( ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣ /٢٢٥ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٦ )
Bai kamata ba kuka yayin mutuwa da kuma yaga
tufafi.
ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ﻟﻌﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺔ ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻤﻌﺔ . ‏(ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
An tsinewa mai koke-koke da kuma mai jiyar da
kukan.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺟﻌﻔﺮ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﺃﺷـﺪ ﺍﻟﺠﺰﻉ ﺍﻟﺼﺮﺍﺥ
ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﺍﻟﻌﻮﻳﻞ ﻭﻟﻄﻢ ﺍﻟﻮﺟﻪ ﻭﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﺰ ﺍﻟﺸﻌﺮ ﻣﻦ
ﺍﻟﻨﻮﺍﺻﻲ، ﻭﻣﻦ ﺃﻗﺎﻡ ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﺔ ﻓﻘﺪ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﺼﺒﺮ، ﻭﺃﺧﺬ ﻓﻲ
ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ . ‏( ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣/٢٢٣ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ ،
ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /٧٦ ) .
Duk Wanda ya tsayu ga koke-koke Haqiqa yabar
haquri,kuma yayi ruqo da hanyar da ba ta gaskiya
ba.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻤﻘﺪﺍﻡ ﻗﺎﻝ : ﺳﻤﻌـﺖ ﺃﺑﺎ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺃﺑﺎ ﺟﻌﻔﺮ
ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻳﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ }: ﻭﻻ
ﻳﻌﺼﻴﻨﻚ ﻓﻲ ﻣﻌﺮﻭﻑ { ‏( ﻗﺎﻝ : ﺇﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺁﻟﻪ
ﻟﻔﺎﻃﻤﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ : ﺇﺫﺍ ﺃﻧﺎ ﻣُـﺖ ﻓـﻼ ﺗﺨﻤﺸﻲ ﻋﻠﻲّ
ﻭﺟﻬﺎ ﻭﻻ ﺗﺮﺧﻲ ﻋﻠﻲّ ﺷﻌﺮﺍ ﻭﻻ ﺗﻨﺎﺩﻱ ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﻻ ﺗﻘﻴﻤﻦ
ﻋﻠﻲّ ﻧﺎﺋﺤﺔ، ﻗﺎﻝ : ﺛﻢ ﻗﺎﻝ : ﻫﺬﺍ ﻫﻮ ‏( ﺍﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ‏) ﺍﻟﺬﻱ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ (( ﻭﻻ ﻳﻌﺼﻴﻨﻚ ﻓﻲ ﻣﻌﺮﻭﻑ .
)) ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ -٩١٦ ، ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Annabi yace da Nana Fadima : Idan nakoma ga
Allah kar kiyi kiran Na mutu na Lalace,kar kuma
kiyimin kururuwa.
ﻗﻮﻝ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻷﺧﺘﻪ ﺯﻳﻨﺐ : ‏( ﻳﺎ ﺃﺧﺘﺎﻩ
ﺃﻗﺴﻤﺖ ﻋﻠﻴﻚ ﻓﺄﺑﺮﻱ ﻗﺴﻤﻲ، ﻻ ﺗﺸﻘﻲ ﻋﻠﻲّ ﺟﻴﺒﺎ ﺟﻴﺒﺎ
ﻭﻻ ﺗﺨﻤﺸﻲ ﻋﻠﻲّ ﻭﺟﻬﺎ، ﻭﻻ ﺗﺪﻋﻲ ﻋﻠﻲّ ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﺍﻟﺜﺒﻮﺭ
ﺇﺫﺍ ﻫﻠﻜﺖ ‏) ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Imam Husain ya fadawa 'yar uwarsa zainab
cewa: idan nakoma ga Allah to karki keta
tufarki,karkiyi kyruruwar jahiliyya.
ﺃﻥ ﻋﻠﻴﺎً ﻋﻠﻴﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻣﻦ ﺿﺮﺏ ﻳﺪﻩ ﻋﻨﺪ
ﻣﺼﻴﺒﺔ ﻋﻠﻰ ﻓﺨﺬﻩ ﻓﻘﺪ ﺣﺒﻂ ﻋﻤﻠﻪ . ‏(ﺍﻟﺨﺼﺎﻝ ﻟﻠﺼﺪﻭﻕ
ﺹ ٦١٢ , ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٣/٢٧٠ ) .
Sayyidi Ali yace: Duk Wanda wata musiba
tazomasa sai ya maka hannunsa kan cinyarsa,to
babu shakka ya rushe aikinsa.
BABBAN ABIN TAMBAYAR ANAN SHINE :-
WANNAN ABIN DA 'YAN SHI'A SUKEYI NA
AZABTAR DAKAI A INA SUKA SAMOSHI ??
ME YASA BASA AIKI DA WADANNAN
RUWAYOYIN DA DUKAI HANI KAN HAKA ??

MATSAYAR SALAFIYYA KAN KASHE JIKAN MANZON ALLAH S.A.W

MATSAYAR SALAFIYYA KAN KASHE JIKAN
MANZAN ALLAH ALHUSSAIN ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ .......

Daga:Malam Abdurrazak Uba Musa

Shehin musulunci ibn taimiya yake cewa:-
ﻓﻼ ﺭﻳﺐ ﺃﻥ ﻗﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻣﻦ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﻭﺃﻥ ﻓﺎﻋﻞ
ﺫﻟﻚ ﻭﺍﻟﺮﺍﺿﻲ ﺑﻪ ﻭﺍﻟﻤﻌﻴﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﺴﺘﺤﻖ ﻟﻌﻘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ . @
‏(ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ٤ /٥٦٠ )
Babu makawa/shakka tabbas kashe Alhussain na
daga mafi girman zunubai,kuma Haqiqa Wanda
yayi kisan,da Wanda ya yarda da kisan,da Wanda
ya taimaka da wani Abu wajan kisan, duk sun
can-can ci azabar Allah.
Anan Shehin ya bayyana cewa:- kisan yana cikin
ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ mafiya girman zunubai.
Sannan ya bayyana cewa:- Wanda yayi da Wanda
ya taimaka da Wanda ya yarda,duk sun can-can
ci Allah ya azabtar dasu.
Shehin yakuma cewa :-
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﻘﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻓﻼ ﺭﻳﺐ ﺃﻧﻪ ﻗﺘﻞ
ﻣﻈﻠﻮﻣﺎ ﺷﻬﻴﺪﺍ ﻛﻤﺎ ﻗﺘﻞ ﺃﺷﺒﺎﻫﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻈﻠﻮﻣﻴﻦ ﺍﻟﺸﻬﺪﺍﺀ
ﻭﻗﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻤﻦ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺃﻋﺎﻥ
ﻋﻠﻰ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺭﺿﻰ ﺑﺬﻟﻚ @. ‏( ٤ /٥٥٠ )
Amma kisan Alhussain ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ babu
makawa tabbas An kashe Alhussain yana abin
zalunta kuma shaheedi,kamar yanda aka kashe
makamantansa suna ababan zalunta kuma
shahidai.
Kashe Alhussain Sabon Allah ne da manzo,ga
Wanda yai kisan ko ya taimaka kan kisan ko ya
yarda da kisan.
Anan kuma Shehin ya bayyana cewa :- Kashe
Alhussain zaluncine.
Sannan kuma ya bayyana cewa:- Alhussain
shahadace yayi.
Sannan Shehin ya bayyana cewa:- Mai kisan da
Wanda ya taimaka masa,da Wanda ya yarda,duk
sun sabawa Allah da manzan Allah.
Anyiwa shin musulunci tambaya hukuncin Wanda
ya kashe jikan manzan Allah Alhussain ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻪ, sai yace:-
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﻦ ﻗﺘﻞ " ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ " ﺃﻭ ﺃﻋﺎﻥ ﻋﻠﻰ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺭﺿﻲ
ﺑﺬﻟﻚ ﻓﻌﻠﻴﻪ ﻟﻌﻨﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ ؛ ﻻ
ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﻪ ﺻﺮﻓﺎ ﻭﻻ ﻋﺪﻻ . @. ‏( ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ
١/٣٩٢ )
Amma Wanda ya kashe Alhussain, ko yataimaka
kan kisan ko ya yarda da kisan,to tsinuwar Allah
data mala'iku,data baki dayan mutane ta tabbata
akansa,kuma Allah bazai karbi farillarsaba da
nafilarsa.
Anan kuma Shehin ya bayyana cewa:- Wanda
yayi kisan da Wanda ya taimaka kan kisan da
Wanda ya yarda da kisan, duk tsinannune.
ALLAH TA'ALA KA QARA TABBATAR DA
AZABARKA GA MAKASAN JIKAN MANZAN
ALLAH DA WADANDA SUKA TAIMAKA WAJAN
KISAN

AQEEDUN YAN TIJJANIYYA

AQEEDU GOMA DAGA AQEEDUN TIJJANIYYA!! ANYI WALQIYA.....!!;> AQEEDA TA FARKO ...................................... SHEIKH AHMADU TIJJANI ACIKIN CONSITUITION DIN TIJJANIYYA WATO JAWAHIRIL MA,ANIY YACE: ﺇﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻮﺭﺩ ﺍﺩﺧﺮﻩ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻲ ﻭ ﻟﻢ ﻳﻌﻠﻤﻪﻷﺣﺪ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ( – ﺇﻟﻰ ﺃﻥ ﻗﺎﻝ :- ) ﻟﻌﻠﻤﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﺘﺄﺧﻴﺮ ﻭﻗﺘﻪﻭﻋﺪﻡ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﻦ ﻳﻈﻬﺮﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺪﻳﻪ WANNAN WURIDIN ANNABINE YA ADANA MINI SHI BAI SANAR DA KOWA BA DAGA ­SAHABBANSA-----­
SABODA ANNABI YASAN LOKACINSA BAIZOBA SABODA BABU WANDA ZAI IYA BAIYANASHI AWANCAN LOKACIN!!!

DUBI YANDA YA JINGINAWA MANZON ALLAH BOYE ILIMI BAYAN ALLAH YANA CEWA: : ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝﺑﻠﻎ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﺇﻟﻴﻚ ﻣﻦ ﺭﺑﻚ SURATL MA IDA: 67 DUBI YADDA YA FIFITA KANSA AKAN ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN DA ALI DA AHLUL BAITI DA SAURAN SAHABBAI DUK ANNABI BAI KOYA MUSU WURIDIN TIJJANIYYA BA SABODA BAZASU IYA KOYAWA MUTANE BA SAI BAYAN ANNABI YABAR DUNIYA SAMA DA SHEKARA DUBU! AKA HAIFI TIJJANI SAI ANNABI YA DAWO DUNIYA YA BASHI WANNAN WURIDI!!!!!

YANZU YA KAMATA MAI LAFIYAYYEN  HANKALI YA YARDA DA WANNAN?

AQEEDA TA BIYU ------------------- AHAMADU TIJJANI YACE: ﺇﻥ ﺍﻟﻤﺮﺓ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪﺓ ﻣﻦ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻔﺎﺗﺢ ﺗﻌﺪﻝ ﻛﻞ ﺗﺴﺒﻴﺢ ﻭﻗﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﻮﻥ ﻭﻛﻞ ﺫﻛﺮ ﻭﻛﻞ ﺩﻋﺎﺀ ﻛﺒﻴﺮ ﺃﻭ ﺻﻐﻴﺮ ﻭﺗﻌﺪﻝ ﺗﻼﻭﺓ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺳﺘﺔ ﺁﻻﻑ ﻣﺮﺓ " SALATUL FATI DAI DAI YAKE DA KOWANE IRIN TASBIHI DA AKAI ABAYAN QASA, HAKA KOWACE ADDU,A BABBA DA QARAMAR TA KUMA YIN SALATIL FATI DAYA DAI DAI YAKE DA SAUKE ALQUR,ANI SAU DUBU SHIDA!!! duba jawahiril ma,ani: shafi:96 bugun attaqaddumul,ilmiyya. Bugu na farko. Dubi yanda wannan mutum ya fifita salatilfati akan qur,ani mai girma!!!!

ﺇﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻔﺘﺮﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﺬﺏ ﻻﻳﻔﻠﺤﻮﻥ ﻣﺘﺎﻉ ﻗﻠﻴﻞ ﻭﻟﻬﻢ ﻋﺬﺍﺏ
ﺃﻟﻴﻢ{ ] ﺍﻟﻨﺤﻞ 116 117].

AQEEDA TA UKU ------------------- AHAMDU TIJJANI YACE: ﻗﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻹﻓﺎﺩﺓ : ) ﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﻌﺘﻘﺪﺃﻧﻬﺎ – ﺃﻱ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻔﺎﺗﺢ – ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻟﻢ ﻳﺼﺐ ﺍﻟﺜﻮﺍﺏ ﻓﻴﻬﺎ ( " ﺹ 80 ".

DUK WANDA BAI YADDA SALATIL FATI ITAMA QUR,ANI BACE KO YAYI BASHI DA LADA!!! duba ifadatul ahmadiyya shafina:80
TO INA MASU SALATIL FATI? KODAI KU YADDA SALATIL FATI QUR,ANI CE WALLAHI IN KUKA FADI KUNYI RIDDA! KO KUMA BAKU YADDABA TO ANAN KUMA KUDA TIJJANI TUNDA GA ABINDA YA FADA: BAKU DA LADA!!! ZAKUJI SAURAN INSHA ALLAHU AKAN AQEEDA TA HUDU IN SHA ALLAH

ﻭﻻ ﺗﻘﻮﻟﻦ ﻟﺸﻲﺀ ﺇﻧﻲ ﻓﺎﻋﻞ ﺫﺍﻟﻚ ﻏﺪﺍ . ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﺸﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺫﻛﺮ ﺭﺑﻚ ﺇﺫﺍ ﻧﺴﻴﺖ ﻭﻗﻞ ﻋﺴﻰ ﺃﻥ ﻳﻬﺪﻳﻨﻲ ﺭﺑﻲ ﻷﻗﺮﺏ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ ﺭﺷﺪﺍ

ALLAH YA QARA KAREMU DAGA WADANNAN AQEEDUN NA SUFAYE!!!

MU'AWUYA BN ABU SUFYAN

*BABU MAI ZAGIN MU'AWUYYA SAI KAFIRI FASIQI MUNAFUKI!!!*

```GA KADAN DAGA CIKIN TARIHINSHI DA
NASABARSHI DA KHALIFANCISA!!!
.
.
.
Nasaba Da Sarakutar Mu’awiya binu Abi
Sufyan(RA).

Shi ne Mu’awiya dan Abu Sufyan (sunansa
Sakhar) dan Harb dan Umayya.

   Ya fito daga
gidan Banu Umayya, dangin Sarkin Musulmi
Usmanu(RA). Mahaifinsa Abu Sufyan ya jagoranci
mushirikan Makka a cikin adawarsu ga
Musulunci da yaqoqansu ga Annabi(SAW).

Ya
musulunta shi da mahaifinsa bayan bude Makka
kuma ya halarci yaqin Hunain tare da Annabi
(SAW).

Ya kasance daga cikin marubutan
Annabi(SAW) kuma Manzo(SAW) ya auri ‘yar
uwarsa Ummu Habiba Ramla diyar Abu
Sufyan, Allah ya yarda da ita.

    Mu’awiya(RA) mutum ne da ya laqanci qulle-
qullen siyaa.

Umar binul
Khaddab ya nada shi a kan wani bangare na
qasar Sham kuma Usmanu binu Affan ya game
masa mulkin Sham baki daya. Mu’awiya ya ja
da Sarkin Musulmi Ali(RA) a lokacin da ya qi
ya yi mubaya’a sai har Ali ya zaqulo wadanda
suka kashe Usmanu daga cikin rundunarsa ya
hukunta su. A sakamakon haka, yaqin Siffain
ya auku tsakanin Ali da Mu’awiya. Bayan da
aka samu qiqi-qaqa a qarshen wannan yaqin,
Mu’awiya ya yi amfani da iya janhurunsa na
siyasa ya yi qarfi, a yayin da Ali ya yi rauni,
kuma rundunarsa ta wargaje a sakamakon
ficewar Khawarijawa daga cikinta. Ali(RA) ya
shagala da yaqar Khawarijawa, abinda ya
qara masa rauni, a lokacin da shi kuma
Mu’awiya ya qara qarfi da kama qasa a cikin
lamarinsa. Ana cikin haka ne Khawarijawa
suka shirya maqarqashiyar kashe Ali da
Mu’awiya, Allah ya yarda da su, wai domin su
hade kan Musulmi kuma su yi maganin fitina.
Amma Mu’awiya ya tsallake wannan
maqarqashiya da qaddarar Allah; shi kuwa sayyidina Ali(R.A)
da aka qaddara masa qarar kwana ya yi
shahada. Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Ali
(RA), magoya bayansa sun yi mubaya’a ga
dansa Hassan(RA) wanda ya zama khalifa na
tsawon wata shida.
Hassan binu Ali(RA) ya yi tunanin ya kai
qarshen jayayya da Mu’awiya wacce ya gada
daga mahaifinsa. Don haka ya dauki matakin yin
sulhu da Mu’awiya kuma ya sakar masa lamarin shugabancin al’umma
domin tsai da zubar da jinin Musulmi a
junansu. Da wannan ne Mu’awiya ya zama
Sarkin Musulmi kuma dukkan bangarori suka
shiga qarqashin da’arsa, in banda
Khawarijawa wadanda suka ci gaba da yaqar
sa. Kuma da wannan sulhu ne aka kai
qarshen zamanin Khulafa’ur Rashidun kuma
aka fara zamanin khalifofin Banu Umayya.
Wannan ya faru a shekara ta 40 bayan hijira,
shekarar da akewa laqabi da Amal Jama’a,
watau shekarar hadin kai, saboda haduwar
al’umma a kan Mu’awiya(RA).
Mu’awiya binu Abi Sufyan ya yi shekara
ishirin yana gwamnan Sham, kuma ya shekara
ishirin yana khalifa. Ya rasu a shekara ta 60
bayan hijira, yana da shekaru saba’in da
takwas a duniya.
Sarkin Musulmi Mu’awiya ya auri Fakhitatu
diyar Qurza, ta haifa masa Abdurrahman da
Abdullahi. Haka nan, ya auri Maisun diyar
Badajal wacce ta haifa masa dansa Yazid
wanda ya gaje shi a matsayin khalifa. Mun
gabatar da bayani cewa gidan su Mu’awiya,
Banu Umayya, surukan Annabi(SAW) ne. Ya
aurar da diyansa mata uku ga ‘ya’yan wannan
gida. Su ne Zainab ya aurar da ita ga Abul
Aas binu Rabi da kuma Ruqayya da Ummu
Kulthum ya aurar da su ga Usmanu binu
Affan. Kamar yadda shi kuma ya auri ‘yar
uwar Mu’awiya, watau Ramla wacce akewa
alkunya da Ummu Habiba, Allah ya yarda da
su baki xaya.```

Copyright©
*ABU-SINAN*

SAKO ZUWA GA YAN TIJJANIYYA 001

*GAREKU YAN TIJJANIYYA, KU KARE ZANTUKANKU IDAN KUN KASANCE MASU GASKIYA*

*HUJJOJI NA HANKALI DA ZASU KORE QARYAR DA SHEIKH AHMADU TIJJANI (R.A) YA KWANTARA NA CEWA YA HADU DA MANZON ALLAH IDO DA IDO.*

_Fitowa na daya (001)_

```Farkon sabanin da aka fara samu a Musulunci tsakanin sahabbai ya Faru ne bayan rasuwar Manzon Allah s.a.w, a lokacin ne mutanen madina sukace ma mutanen Makkah (muhajirai) mu zamu Nada namu jagora, kuma Ku Nada naku. Haka akayi har tsawon kwana uku kafin a rufe manzon Allah s.a.w.
Tambaya; ya akayi manzon Allah s.a.w bai tashi ya kai karshen wannan cece-kuce da sahabbai keyi ba(ma'ana: yace wane ne Khalifa a baya na)?

Ya akayi manzon Allah s.a.w ya bar wannan al'amari na khalifanci mai girma ba tare da ya tashi yayi bayani ba???

Da ace manzon Allah s.a.w zaiyi magana da wani a farke bayan ya mutu, da sahabbanshi zaiyi magana dasu domin magance musu waccan jayayyar akan ace ya bayyana ga shehu tijjani. Bayan shi Tijjani sai da Manzon Allah s.a.w ya bar duniya da shekara dubu da Dari daya da hamsin(1150AH) ko makamancin haka sannan aka haifeshi. Toh ya akayi hakan ta kasance???

Yan Tijjaniyya muna bukatar amsar wannan tambayar!!!

Allah ka shiryar damu akan hanya madaidaiciya.

Copyright©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU-SINAN)
08064734911```