*GAREKU YAN TIJJANIYYA, KU KARE ZANTUKANKU IDAN KUN KASANCE MASU GASKIYA*
*HUJJOJI NA HANKALI DA ZASU KORE QARYAR DA SHEIKH AHMADU TIJJANI (R.A) YA KWANTARA NA CEWA YA HADU DA MANZON ALLAH IDO DA IDO.*
_Fitowa na daya (001)_
```Farkon sabanin da aka fara samu a Musulunci tsakanin sahabbai ya Faru ne bayan rasuwar Manzon Allah s.a.w, a lokacin ne mutanen madina sukace ma mutanen Makkah (muhajirai) mu zamu Nada namu jagora, kuma Ku Nada naku. Haka akayi har tsawon kwana uku kafin a rufe manzon Allah s.a.w.
Tambaya; ya akayi manzon Allah s.a.w bai tashi ya kai karshen wannan cece-kuce da sahabbai keyi ba(ma'ana: yace wane ne Khalifa a baya na)?
Ya akayi manzon Allah s.a.w ya bar wannan al'amari na khalifanci mai girma ba tare da ya tashi yayi bayani ba???
Da ace manzon Allah s.a.w zaiyi magana da wani a farke bayan ya mutu, da sahabbanshi zaiyi magana dasu domin magance musu waccan jayayyar akan ace ya bayyana ga shehu tijjani. Bayan shi Tijjani sai da Manzon Allah s.a.w ya bar duniya da shekara dubu da Dari daya da hamsin(1150AH) ko makamancin haka sannan aka haifeshi. Toh ya akayi hakan ta kasance???
Yan Tijjaniyya muna bukatar amsar wannan tambayar!!!
Allah ka shiryar damu akan hanya madaidaiciya.
Copyright©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU-SINAN)
08064734911```
No comments:
Post a Comment