Wednesday, 6 December 2017

MATSAYAR SALAFIYYA KAN KASHE JIKAN MANZON ALLAH S.A.W

MATSAYAR SALAFIYYA KAN KASHE JIKAN
MANZAN ALLAH ALHUSSAIN ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ .......

Daga:Malam Abdurrazak Uba Musa

Shehin musulunci ibn taimiya yake cewa:-
ﻓﻼ ﺭﻳﺐ ﺃﻥ ﻗﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻣﻦ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﻭﺃﻥ ﻓﺎﻋﻞ
ﺫﻟﻚ ﻭﺍﻟﺮﺍﺿﻲ ﺑﻪ ﻭﺍﻟﻤﻌﻴﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﺴﺘﺤﻖ ﻟﻌﻘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ . @
‏(ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ٤ /٥٦٠ )
Babu makawa/shakka tabbas kashe Alhussain na
daga mafi girman zunubai,kuma Haqiqa Wanda
yayi kisan,da Wanda ya yarda da kisan,da Wanda
ya taimaka da wani Abu wajan kisan, duk sun
can-can ci azabar Allah.
Anan Shehin ya bayyana cewa:- kisan yana cikin
ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ mafiya girman zunubai.
Sannan ya bayyana cewa:- Wanda yayi da Wanda
ya taimaka da Wanda ya yarda,duk sun can-can
ci Allah ya azabtar dasu.
Shehin yakuma cewa :-
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﻘﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻓﻼ ﺭﻳﺐ ﺃﻧﻪ ﻗﺘﻞ
ﻣﻈﻠﻮﻣﺎ ﺷﻬﻴﺪﺍ ﻛﻤﺎ ﻗﺘﻞ ﺃﺷﺒﺎﻫﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻈﻠﻮﻣﻴﻦ ﺍﻟﺸﻬﺪﺍﺀ
ﻭﻗﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻤﻦ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺃﻋﺎﻥ
ﻋﻠﻰ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺭﺿﻰ ﺑﺬﻟﻚ @. ‏( ٤ /٥٥٠ )
Amma kisan Alhussain ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ babu
makawa tabbas An kashe Alhussain yana abin
zalunta kuma shaheedi,kamar yanda aka kashe
makamantansa suna ababan zalunta kuma
shahidai.
Kashe Alhussain Sabon Allah ne da manzo,ga
Wanda yai kisan ko ya taimaka kan kisan ko ya
yarda da kisan.
Anan kuma Shehin ya bayyana cewa :- Kashe
Alhussain zaluncine.
Sannan kuma ya bayyana cewa:- Alhussain
shahadace yayi.
Sannan Shehin ya bayyana cewa:- Mai kisan da
Wanda ya taimaka masa,da Wanda ya yarda,duk
sun sabawa Allah da manzan Allah.
Anyiwa shin musulunci tambaya hukuncin Wanda
ya kashe jikan manzan Allah Alhussain ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻪ, sai yace:-
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﻦ ﻗﺘﻞ " ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ " ﺃﻭ ﺃﻋﺎﻥ ﻋﻠﻰ ﻗﺘﻠﻪ ﺃﻭ ﺭﺿﻲ
ﺑﺬﻟﻚ ﻓﻌﻠﻴﻪ ﻟﻌﻨﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ ؛ ﻻ
ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﻪ ﺻﺮﻓﺎ ﻭﻻ ﻋﺪﻻ . @. ‏( ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ
١/٣٩٢ )
Amma Wanda ya kashe Alhussain, ko yataimaka
kan kisan ko ya yarda da kisan,to tsinuwar Allah
data mala'iku,data baki dayan mutane ta tabbata
akansa,kuma Allah bazai karbi farillarsaba da
nafilarsa.
Anan kuma Shehin ya bayyana cewa:- Wanda
yayi kisan da Wanda ya taimaka kan kisan da
Wanda ya yarda da kisan, duk tsinannune.
ALLAH TA'ALA KA QARA TABBATAR DA
AZABARKA GA MAKASAN JIKAN MANZAN
ALLAH DA WADANDA SUKA TAIMAKA WAJAN
KISAN

No comments: