HANI KAN DUKAN JIKI KO TSAGA TUFA KO
IHOCE-IHOCE YAYIN WATA MUSIBA, BAFA CIKIN
LITATTAFAN SUNNAH KURUM YAZOBA, YA
TABBATA HATTA CIKIN LITATTAFAN
SHI'A.........
Daga: Malam Abdurrazak Uba Musa
Bari indan fitoda koda dozin dayane daga cikin
ruwayoyin :
ﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ . ( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ١٢ /٩١٥
ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /١٠٣ )
Ihoce-ihoce na daga aikin jahiliyya.
ﻧﻬﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﺮﻧﺔ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻤﺼﻴﺒﺔ ﻭﻧﻬﻰ ﻋﻦ
ﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ ﻭﺍﻻﺳﺘﻤﺎﻉ ﺇﻟﻴﻬﺎ . ( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ )
Annabi yayi hani ga daga sauti yayin kuka,da
ihoce-ihoce,da kuma jiyarda kukan yayin faruwar
musiba.
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ( ﺻﻮﺗﺎﻥ
ﻣﻠﻌﻮﻧﺎﻥ ﻳﺒﻐﻀﻬﻤﺎ ﺍﻟﻠﻪ ،ﺃﻋﻮﺍﻝ ﻋﻨﺪ ﻣﺼﻴﺒﺔ ﻭﺻﻮﺕ ﻋﻨﺪ
ﻧﻌﻤﺔ، ﻳﻌﻨﻲ " ﺍﻟﻨﻮﺡ ﻭﺍﻟﻐﻨﺎﺀ ) ( ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ
ﻟﻠﻨﻮﺭﻱ . ١/١٤٤ ، ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /١٠١ )
Sautika 2 ababen tsinewane,Allah baya sansu,
daga murya da kuka yayin wata musiba,da daga
murya yayin farinciki.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﻻ ﻳﺼﻠﺢ ﺍﻟﺼﻴﺎﺡ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ، ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻻ ﻳﻌﺮﻓﻮﻥ .
(ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣/٢٢٦ ، ﺍﻟﻮﺍﻓﻲ ١٢ /٨٨ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٦ )
Bai kyautuba kururuwa yayin mutuwa,bakuma ta
kamata ba,Amma kash 'yan Shi'a basu saniba.
}ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺇﻟﻰ ﺭﻓﺎﻋﺔ ﺑﻦ ﺷﺪﺍﺩ :{
ﻭﺇﻳﺎﻙ ﻭﺍﻟﻨﻮﺡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﺑﺒﻠﺪ ﻳﻜﻮﻥ ﺻﻮﺕ ﻟﻚ ﺑﻪ
ﺳﻠﻄﺎﻥ
( ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Rubutun sayyidi Ali zuwa ga rifa'a, yace dashi:-
Kashedinka ga kuka yayin mutuwa.
ﻋﻦ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ :
ﻣﻦ ﺿﺮﺏ ﻳﺪﻩ ﻋﻞ ﻓﺨﺬﻩ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻤﺼﻴﺒﺔ ﺣﺒﻂ ﺃﺟﺮﻩ .
( ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٤ )
Duk Wanda ya doki cinyarsa da hannunsa yayin
musiba,to ya rushe ladansa.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﺍﻟﺼﻴﺎﺡ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ ﺗﺸﻖ ﺍﻟﺜﻴﺎﺏ .
( ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣ /٢٢٥ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٦ )
Bai kamata ba kuka yayin mutuwa da kuma yaga
tufafi.
ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ﻟﻌﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺔ ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻤﻌﺔ . (ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
An tsinewa mai koke-koke da kuma mai jiyar da
kukan.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺟﻌﻔﺮ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﺃﺷـﺪ ﺍﻟﺠﺰﻉ ﺍﻟﺼﺮﺍﺥ
ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﺍﻟﻌﻮﻳﻞ ﻭﻟﻄﻢ ﺍﻟﻮﺟﻪ ﻭﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﺰ ﺍﻟﺸﻌﺮ ﻣﻦ
ﺍﻟﻨﻮﺍﺻﻲ، ﻭﻣﻦ ﺃﻗﺎﻡ ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﺔ ﻓﻘﺪ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﺼﺒﺮ، ﻭﺃﺧﺬ ﻓﻲ
ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ . ( ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ ٣/٢٢٣ ، ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ ،
ﺑﺤﺎﺭ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ٨٢ /٧٦ ) .
Duk Wanda ya tsayu ga koke-koke Haqiqa yabar
haquri,kuma yayi ruqo da hanyar da ba ta gaskiya
ba.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻤﻘﺪﺍﻡ ﻗﺎﻝ : ﺳﻤﻌـﺖ ﺃﺑﺎ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺃﺑﺎ ﺟﻌﻔﺮ
ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻳﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ }: ﻭﻻ
ﻳﻌﺼﻴﻨﻚ ﻓﻲ ﻣﻌﺮﻭﻑ { ( ﻗﺎﻝ : ﺇﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺁﻟﻪ
ﻟﻔﺎﻃﻤﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ : ﺇﺫﺍ ﺃﻧﺎ ﻣُـﺖ ﻓـﻼ ﺗﺨﻤﺸﻲ ﻋﻠﻲّ
ﻭﺟﻬﺎ ﻭﻻ ﺗﺮﺧﻲ ﻋﻠﻲّ ﺷﻌﺮﺍ ﻭﻻ ﺗﻨﺎﺩﻱ ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﻻ ﺗﻘﻴﻤﻦ
ﻋﻠﻲّ ﻧﺎﺋﺤﺔ، ﻗﺎﻝ : ﺛﻢ ﻗﺎﻝ : ﻫﺬﺍ ﻫﻮ ( ﺍﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ) ﺍﻟﺬﻱ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ (( ﻭﻻ ﻳﻌﺼﻴﻨﻚ ﻓﻲ ﻣﻌﺮﻭﻑ .
)) ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٢ /٩١٥ -٩١٦ ، ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Annabi yace da Nana Fadima : Idan nakoma ga
Allah kar kiyi kiran Na mutu na Lalace,kar kuma
kiyimin kururuwa.
ﻗﻮﻝ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻷﺧﺘﻪ ﺯﻳﻨﺐ : ( ﻳﺎ ﺃﺧﺘﺎﻩ
ﺃﻗﺴﻤﺖ ﻋﻠﻴﻚ ﻓﺄﺑﺮﻱ ﻗﺴﻤﻲ، ﻻ ﺗﺸﻘﻲ ﻋﻠﻲّ ﺟﻴﺒﺎ ﺟﻴﺒﺎ
ﻭﻻ ﺗﺨﻤﺸﻲ ﻋﻠﻲّ ﻭﺟﻬﺎ، ﻭﻻ ﺗﺪﻋﻲ ﻋﻠﻲّ ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﺍﻟﺜﺒﻮﺭ
ﺇﺫﺍ ﻫﻠﻜﺖ ) ﻣﺴﺘﺪﺭﻙ ﺍﻟﻮﺳﺎﺋﻞ ١/١٤٤ )
Imam Husain ya fadawa 'yar uwarsa zainab
cewa: idan nakoma ga Allah to karki keta
tufarki,karkiyi kyruruwar jahiliyya.
ﺃﻥ ﻋﻠﻴﺎً ﻋﻠﻴﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻣﻦ ﺿﺮﺏ ﻳﺪﻩ ﻋﻨﺪ
ﻣﺼﻴﺒﺔ ﻋﻠﻰ ﻓﺨﺬﻩ ﻓﻘﺪ ﺣﺒﻂ ﻋﻤﻠﻪ . (ﺍﻟﺨﺼﺎﻝ ﻟﻠﺼﺪﻭﻕ
ﺹ ٦١٢ , ﻭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ٣/٢٧٠ ) .
Sayyidi Ali yace: Duk Wanda wata musiba
tazomasa sai ya maka hannunsa kan cinyarsa,to
babu shakka ya rushe aikinsa.
BABBAN ABIN TAMBAYAR ANAN SHINE :-
WANNAN ABIN DA 'YAN SHI'A SUKEYI NA
AZABTAR DAKAI A INA SUKA SAMOSHI ??
ME YASA BASA AIKI DA WADANNAN
RUWAYOYIN DA DUKAI HANI KAN HAKA ??
No comments:
Post a Comment