Wednesday, 6 December 2017

MU'AWUYA BN ABU SUFYAN

*BABU MAI ZAGIN MU'AWUYYA SAI KAFIRI FASIQI MUNAFUKI!!!*

```GA KADAN DAGA CIKIN TARIHINSHI DA
NASABARSHI DA KHALIFANCISA!!!
.
.
.
Nasaba Da Sarakutar Mu’awiya binu Abi
Sufyan(RA).

Shi ne Mu’awiya dan Abu Sufyan (sunansa
Sakhar) dan Harb dan Umayya.

   Ya fito daga
gidan Banu Umayya, dangin Sarkin Musulmi
Usmanu(RA). Mahaifinsa Abu Sufyan ya jagoranci
mushirikan Makka a cikin adawarsu ga
Musulunci da yaqoqansu ga Annabi(SAW).

Ya
musulunta shi da mahaifinsa bayan bude Makka
kuma ya halarci yaqin Hunain tare da Annabi
(SAW).

Ya kasance daga cikin marubutan
Annabi(SAW) kuma Manzo(SAW) ya auri ‘yar
uwarsa Ummu Habiba Ramla diyar Abu
Sufyan, Allah ya yarda da ita.

    Mu’awiya(RA) mutum ne da ya laqanci qulle-
qullen siyaa.

Umar binul
Khaddab ya nada shi a kan wani bangare na
qasar Sham kuma Usmanu binu Affan ya game
masa mulkin Sham baki daya. Mu’awiya ya ja
da Sarkin Musulmi Ali(RA) a lokacin da ya qi
ya yi mubaya’a sai har Ali ya zaqulo wadanda
suka kashe Usmanu daga cikin rundunarsa ya
hukunta su. A sakamakon haka, yaqin Siffain
ya auku tsakanin Ali da Mu’awiya. Bayan da
aka samu qiqi-qaqa a qarshen wannan yaqin,
Mu’awiya ya yi amfani da iya janhurunsa na
siyasa ya yi qarfi, a yayin da Ali ya yi rauni,
kuma rundunarsa ta wargaje a sakamakon
ficewar Khawarijawa daga cikinta. Ali(RA) ya
shagala da yaqar Khawarijawa, abinda ya
qara masa rauni, a lokacin da shi kuma
Mu’awiya ya qara qarfi da kama qasa a cikin
lamarinsa. Ana cikin haka ne Khawarijawa
suka shirya maqarqashiyar kashe Ali da
Mu’awiya, Allah ya yarda da su, wai domin su
hade kan Musulmi kuma su yi maganin fitina.
Amma Mu’awiya ya tsallake wannan
maqarqashiya da qaddarar Allah; shi kuwa sayyidina Ali(R.A)
da aka qaddara masa qarar kwana ya yi
shahada. Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Ali
(RA), magoya bayansa sun yi mubaya’a ga
dansa Hassan(RA) wanda ya zama khalifa na
tsawon wata shida.
Hassan binu Ali(RA) ya yi tunanin ya kai
qarshen jayayya da Mu’awiya wacce ya gada
daga mahaifinsa. Don haka ya dauki matakin yin
sulhu da Mu’awiya kuma ya sakar masa lamarin shugabancin al’umma
domin tsai da zubar da jinin Musulmi a
junansu. Da wannan ne Mu’awiya ya zama
Sarkin Musulmi kuma dukkan bangarori suka
shiga qarqashin da’arsa, in banda
Khawarijawa wadanda suka ci gaba da yaqar
sa. Kuma da wannan sulhu ne aka kai
qarshen zamanin Khulafa’ur Rashidun kuma
aka fara zamanin khalifofin Banu Umayya.
Wannan ya faru a shekara ta 40 bayan hijira,
shekarar da akewa laqabi da Amal Jama’a,
watau shekarar hadin kai, saboda haduwar
al’umma a kan Mu’awiya(RA).
Mu’awiya binu Abi Sufyan ya yi shekara
ishirin yana gwamnan Sham, kuma ya shekara
ishirin yana khalifa. Ya rasu a shekara ta 60
bayan hijira, yana da shekaru saba’in da
takwas a duniya.
Sarkin Musulmi Mu’awiya ya auri Fakhitatu
diyar Qurza, ta haifa masa Abdurrahman da
Abdullahi. Haka nan, ya auri Maisun diyar
Badajal wacce ta haifa masa dansa Yazid
wanda ya gaje shi a matsayin khalifa. Mun
gabatar da bayani cewa gidan su Mu’awiya,
Banu Umayya, surukan Annabi(SAW) ne. Ya
aurar da diyansa mata uku ga ‘ya’yan wannan
gida. Su ne Zainab ya aurar da ita ga Abul
Aas binu Rabi da kuma Ruqayya da Ummu
Kulthum ya aurar da su ga Usmanu binu
Affan. Kamar yadda shi kuma ya auri ‘yar
uwar Mu’awiya, watau Ramla wacce akewa
alkunya da Ummu Habiba, Allah ya yarda da
su baki xaya.```

Copyright©
*ABU-SINAN*

No comments: