Friday, 8 December 2017

HUDUBAH MAI TAKEN RAMADANA DA ABUNDA YA KUNSA

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #FALALAR WATAN
RAMADAN DA ABUNDA YA KUNSA
Godiya ta tabbata ga ALLAH Wanda ya sanyawa
bayin sa alamomi da zasu zama alama garesu da
yin bauta a lokachin,
Tsira da aminci su tabbata ga wanda ALLAH Ya
aiko da gaskiya da iyalansa da sahabbansa da
dukkan wadanda suka biyo bayansa da
kyautatawa sallallahu alaihi wassalam,
Yan uwa musulmi muna fuskantar wani yanayi
mai matukar alfanu, Wanda yana kyau muci ribar
wadannan kwanuka mu yawaita taimakon kanmu,
Mu yiwa kawunan mu hisabi, Yakamata muyi
amfani da wannan dama wajen neman gafara da
yafiya daga ubangiji ALLAH,
Watan ramadana wata ne mai alfarma wanda
ALLAH Yasanya shi daga cikin rukunan
musulunci, Ramadana wata ne na tausayi da
rahama da taimakon juna.
A cikin watan ramadan akwai wata rana wadda
tafi dare dubu,
Yan uwa musulmi mu karrama wannan watan da
abubuwa guda biyu (2), Na daya ALLAH Ya ara
mana rayuwa ta kawuwa wannan watan, Sai
kuma zuwan watan na ramadan mai albarka,
Yan uwa musulmi akwai abubuwan da yakamata
mu aikata a cikin wannan watan mai kamawa,
Daga cikin su akwai;
-Mu roki ALLAH Ya yarda damu, Ya karbi dukkan
ibadun da mukayi, Duk wanda aka karbi ibadun
su a cikin watan ramadan to yayi murna yayi
farin ciki,
Lallai kololowar murna ita ce kayi murna da
zuwansa, Da kuma ni'imar halartar sa, Akwai
wanda yafara jin kanshin sa Amma ALLAH Bai
nuna masa ba, Baya daga cikin addini yin murna
walau ta samun matsayi ko dukiya kamar yadda
aya take cewa "GASUNAN SUNA FARIN CIKIN
DAN SAMUN DUNIYA ALHALI BA KOMAI BACE
IDAN KA KWATANTA DA LAHIRA"
-Kiyaye salloli na farilla a cikin lokachi, Idan har
baka sallah cikin jam'i to yakamata kayi amfani
da watan ramadan dan koya da yin sallah cikin
jam'i
-Kaucewa yin sabo, Kaucewa aikata sabo kowane
irin, Ba kauracewa ci da sha ne kurum azumi ba,
A'a harda kiyaye gabobi baki daya daga aikata
zunubai,
-Mai hankali baligi ya sanya a ransa zaiyi azumi
dan ALLAH, Dan kwadayin lada, Da kuma
kaucewa fadawa azabar ALLAH.
Muddin aka samu mutun kawai zai yi azumi dan
yazama dole, Dan kada ace wane baiyi to akwai
matsala, Yakamata a gyara dan samun ladar da
ake nema.
Azumin watan ramadan yana farawa ne da zarar
wata sha'aban yakai ashirin da tara idan ba'a ga
wata ba kuma yakai talatin, kamar yadda hadisi
daga manzo rahama na cewa "KUYI AZUMI IDAN
KUNGA WATA KU AJE IDAN KUNGA WATA"
Idan har mai alfarma sarkin Musulmi yabada
umarnin daukar azumi, To kada ayi wata wata
wajen dauka,
Idan aka bada umarni to akwai abubuwan da
yakamata ayi kamar;
-Kulla niyyah a zuciya, Ba ambatawa da baki ba,
-Sallar tarawihi, Ko a daren yau za'a iya fara
tarawihi dama ana bukatar a tari wannan watan
da aiyuka na alheri dan su zame ma jiki, Idan
watan yazo zaka iya,
>Yan uwa musulmi abunda ake cewa azumi shine
barin chi da sha da kame gabobi, ALLAH
Madaukakin sarki na cewa "KUCI KUSHA HAR
SAI BAKIN ZARE YA FITO DAGA ALFIJIR"
=Hakama yakamata ladanai kuji tsoron ALLAH
kada ladanai su kuskura su kira sallah kafin
lokachi yayi ko bayan lokachi, A yanzu muna
cikin yanayi na damina wanda gari ke laulayewa,
Jiya anan Tsafe anyi ruwa, Wasu ladanai sunyi
kiran sallah tun karfe 6:30pm, Maimakon
6:55pm.
Anan fa mutane uku ne keda laifi na daya Ladani
shi da ya kira sallah kafin lokachi yayi,
Sai kuma limani wanda shine jagora yaje yabada
sallah,
Sai kuma mamu wanda yakamata ku lura da
jadawali, Kafin sallah!
Anan jahar, Gwamnati tana raba jadawali a duk
wani massallaci komai yadda yake cikin lungu,
Kada kuma sai ladani yaci yakoshi har lokachi ya
wuce sannan yace zai kira sallah,
Idan ladani ya kira sallah lokachi baiyi ba, To
Ladani ne keda alhaki na karewar azumin su,
Alfijir na fitowa ne 04:55/6, Magrib 06:55, duk
yanayi n chanzawa, A kula sosai idan ladanai
sunyi kuskure mafita kurum a dinga diba
jadawalin da gwamnati ke kawo, Kowane lokachi
basai radaman ba.
-Tarawihi babbar sunnah ce dake nuna alamar
tsayawar ramadan, Ana samun falala a ciki.
Limamai aji tsoron ALLAH
Limamai aji tsoron ALLAH
Limamai aji tsoron ALLAH
Sau da yawa zakaga limamai na wulakanta
sallah, Ta hanyar yin qoton kurciya da yin ta
yadda aka ga dama,
Manzo rahama na cewa "KUYI SALLAH KAMAR
YADDA KUKAGA INAYI"
To sai ayita gwargwadon hali,
Wani mutun yazo yana sallah yagama yazo
wajen manzo ALLAH Sai manzo s.a.w yace ka
koma kayi sallah dan bakayi sallah ba, Sai da
akayi sau 3, Daga nan manzo s.a.w ya gwada
masa yadda zaiyi da kyau ta hanyar jeranta
kira'a da yi anatse da cikin ruku'u da sujjada,
=Yana da kyau a rage sautin amsa kuwa (Loud
speaker), Domin kada karatu na chan dana chan
su hade sai kaji duk abu ya rikice.
Wata rana Manzo s.a.w ya shigo massallaci ya
tarar kowa na sallar sa anan yahada su kan
limami daya wato Ubaiy bn Ka'af R.A
Hakama wajen yin tahujjud akiyaye.
Yan uwa musulmi manzo s.a.w ya kai karshe
komai game da ganin wata, Idan an samu rikici
to ko kaine ko wani ne ya rikice, Manzo rahama
s.a.w na cewa "IDAN KUKA DAUKA BA'A GANI
BA KU CIKA TALATIN"
Idan sarki musulmi ya bada sanarwar angani ka
sallama kawai ka dauka,
Kasar Saudiyya Yau watan su talatin yake amma
mu 29, Idan mungani zamu dauka anan Najeriya,
Yan uwa musulmi a cikin watan ramadana ana
bukatar taimakon juna, A taimakawa talakawa da
abinci koda koko da kosai ne, Domin wani ko
abincin buda baki baida shi, "Manzo s.a.w ya
kasance idan watan ramadan yazo yakan yawaita
alheri kai kace iska ne ya taso".
Ka taimaki yan uwa musulmi anan za'a gane
kana taimako.
Kuma taimako bawai sai masu kudi ba kowa
yasan wanda yafi sai ka taimaka masa, ALLAH
Madaukakin sarki na cewa "KU TAIMAKA A KASA
NI DAKE SAMA ZAN TAIMAKA MAKU"
Muna rokon ALLAH Sunayen kyawawa, Tsarkaka
ya biya mana bukatun mu, Yayi mana gafara da
rahama, Ya karbi ibadun mu wadanda mukayi da
wadanda zamuyi,
Ya ALLAH Yabaiwa shugaban kasa da Mai
martab emir na Tsafe lafiya, Yayi jagora ga
shuwagabanni mu, Ya shiryamu hanya madaidai
ciya.
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
29/Sha'aban/1438
26/05/2017.

HUDUBAH MAI TAKEN SABUBBAN DAKE SA A SHIGA ALJANNA

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan SABUBBAN DAKE
KAIWA ZUWA GA ALJANNAH DA KUMA CIKAWA
MAI KYAU DA KUMA MASU KAIWA ZUWA WUTA
DA CIKAWAR MARAR KYAU
Godiya ta tabbata ga ALLAH Muna gode masa
muna neman taimakon sa, Mune neman yakare
daga sharrin kawu nan mu,
Duk wanda ALLAH Ya shiryar babu mai batar
dashi, Duk wanda ALLAH Yabatar babu mai iya
shiryar dashi,
Tsira da amincin ALLAH Su kara tabbata ga
mafifin halittun manzo tsira, Da iyalan da
sahabban sa, Da dukan wadanda suka biyo
bayansu da kyautatawa.
Yan uwa musulmi muyi gaggawar tuba zuwa ga
ALLAH Dan neman yagafarta mana daga laifukan
da muke aikatawa,
Ibadar da muke aikata duka bata kara ALLAH Da
komai, Hakama Fandare mai bai ragesa da
komai, Kamar yadda yake fada cikin hadisul kudsi
cewa ''YAKU BAYINA IDAN ZAKU KURE WAJEN
BAUTA MANI BAZAKU KARANI DA KOMAI BA
KUMA IDAN KUKA KAFURCE MANI BAZAKU
RAGE NI DA KOMAI BA''
YAN UWA MUSULMI Hakika aikata ayyukan alheri
suke kai mutun ga samun aljannah, Kolololuwar
sune ayyukan zukata,
Sannan aiyukan jiki sune ke taimaka ma zuciya
hadisin sahihi ya tabbata cewa ''DUKAN AYYUKA
TARE DA NIYA SUKE TAFIYA''
Aiyukan marar sa kyau kama daga Cuta, zalunci,
Yaudara munafucci E.t.c suke haddasa halin da
muke ciki kamar yadda ayar Qur'ani take cewa
''BANNA TA BAIYANA A SARARI DA KUMA CIKIN
TEKU SABODA AYYUKAN DA HANNAYE KE
AIKATAWA''
Ya yan uwa musulmi yin bauta dan ALLAH Dayin
wasiyya ta kwarai na jagoranta zuwa ga aljannah
hadisin ingantacce na cewa ''ANA CIKA AYYUKA
DA AIKI NA KWARAI DA KUMA CIKI MUNANA
MUMMUNAN KARSHE''
Yan uwa musulmi muyi dukan mai yiwuwa wajen
ganin mun cika da kyawawan ayyukan da samun
tsira gobe kiyama, ALLAH Yana gargadar mu
cewa a suratu ali imran cewa '' KUJI TSORON
ALLAH KADA KU MUTU FACE KUNA MUSULMI''
Kunga kenan wajibi mu nemi yin ayyukan kirki,
Da neman yafiya dan haduwa dashi da imani!
Yaku yan uwa musulmi shagaltuwa da ayyuka na
alheri sa samun cikawa ta kwarai, Hakama
Annabawa kamar su Ibrahim A.S Da Yunus A.S
Sunyi wasiya ga ''Kada ku bautawa kowa in
banda ALLAH'' Kunga wasiya ce mai kyau,
Ababen dake sanya Cikawa mai kyau nada yawa
ga wasu daga ciki
1-KYAKYAWAR NIYA Niya mai kyau wajen aikata
aiyuka.
2-IHLASI wato yi dan ALLAH Kai tsaye
3-KULA DA TSARE LOKACHIN SALLOLI CIKIN
JAM'I wato yin sallah a lokacinta kuma cikin
mutane.
4-GYARA Jawo al'umma zuwa ga hanyar gyara
da zata taimaka masu wajen kara kusanci da
ALLAH Kamar yadda ayar Qur'ani ke cewa ''DUK
WANDA YAYI AIKI NA KWARAI BAI DA TSORON
LOKACHIN MUTUWA''
5-TSORON ALLAH FILI DA BOYE
6-LIZIMTAR SUNNAH DA KOYI DA MAGABATA
NA KIRKI
7-KYAUTAMA AL'UMMA Yi masu fara'a, Da
yawan yi masu kyauta, Da Sadaqah da kuma
yawan yi masu sallama, Duk yana cikin
kyautawa. ALLAH Yana cewa ''WADANNAN
MASU TAIMAKO A FILI DA BOYE TO BABU
TSORON RANAR MUTUWAR SU''
8-KAMEWA CUTAR DA AL'UMMA
9-YIN ADDU'A Kamar yadda ALLAH Ke cewa ''KU
ROKE NI ZAN KARBA MAKU WADANNAN MASU
GIRMAN KAI DA ROKON ALLAH ZASU SHIGA
JAHANNAMA''
10-ADDU'A GA JAMA'A Wato yin jam'in addu'a
ga kamar cewa ALLAH Ka yafe mana, kayi mana
rahama ka gafarta mana, Hadisi ya tabbata cewa
''AKWAI MALA'IKA WANDA DUK KAYI ROKO SAI
YACE KAIMA HAKA'' kunga kenan idan muka roki
ALLAH Da roko mai kyau ko marar kyau duka
zata iya dawowa garemu.
Yaku yan uwa musulmi muyi hattara tare da
kiyaye aikata miyagun aiyuka, Da zarar ka mutu
babu imani to haqira kayi babbar hasara,
Suna da matukar yawa amma ga wasu daga
cikin su.
1-MUNAFURCI Wanda yanzu yazama ruwan dare,
A tsakanin al'umma wanda yake kaiwa ga
mummunar makoma
2-TOZARTAR DA SALLAR FARILLA Tozarta salla
ta farilla yana kaiwa zuwa ga zuwa wuta.
3-JAHILCI Wato rashin karatun addini, Da kin
gaskiya.
4-RASHIN SALLAR JUMU'A Tabbas rashin sallar
jumu'a yana kaiwa kai tsaye zuwa ga wuta.
5-RASHIN JAM'I Sai kaga kawai mutun yaki zuwa
massallaci, Yayi zaune yana sallah a gida.
6-SATA
7-CHIN MUTUNCI
8-KARYA wadda yanzu ta zama kamar ado a
tsakanin mutane musamman matasa.
9-KARKATUWA ZUWA GA DUNIYA DA KIN
LAHIRA.
10-GABATAR DA SON DUNIYA BISA GA TA
LAHIRA.
11-CUTAR ZUCIYA cutar zuciya tana da fadi da
kuma yawa ga misalan ta kamar haka
-GIRMAN KAI Wanda hausawa ke cewa rawanin
tsiya ''DUK MAI GIRMAN KAI DAI DAI DA
KWAYAR ZAIRA BAYA SHIGA ALJANNAH''
-HASSADA Wadda itama kanta yanzu ta zama
ruwan dare, Da zarar wani yaga kafara samun
wani abun hannu to shikenan kyashi da hassada,
Zasu fara biyo baya.
-JI DA KAI
-YAUDARA
-MAKIRCI
-ALGUSSU
-KIN ABUNDA ALLAH KESO
-SON ABUNDA ALLAH BAYASO
Ranar kiyama Kudi da yaya basu da tasiri kamar
yadda Qur'ani ke cewa.
12-SABAMA IYAYE A wannan lokachin
musamman matasa, Suna sabawa iyayen su
wanda iyaye sune suka rene su, Suka bada
kudaden su wajen samar wa yayan su da ilmi,
Amma da zarar sun girma sai su fara wulakanta
su, Har wata rana zakaji iyaye na bidar yayan
alhali suna cikin garin, Matasa yakamata muji
tsoron Hadisi daga manzo tsira na cewa
''ALJANNAR MU NA KARKASHIN KAFAFUN
MAHAIFAN MU''
13-YANKE ZUMUNTA A wannan zamanin yanke
zumunta yana da matuqar yawa a tsakanin
al'umma, Zakaga wa da qane uwa daya uba
daya, Ko kuma uba daya ko uwa daya, Ko kuma
wata dangantaka ta jini suna gaba da juna babu
magana a tsakani, Wanda haka na jagoranta
zuwa ga mummunar makoma, Da kuma zuwa
Jahannama, ALLAH Ya karemu ALLAH
Madaukakin sarki na cewa A cikin aya mai
matukar ban tsoro ''KUJI TSORON YININ DA ZA'A
MAIDA KU WAJEN ALLAH ZA'A CIKAWA WA
KOWA DA ABUNDA YA AIKATA BAZA'A ZALUNCI
KOWA BA''
Daga karshe muna rokon ALLAH Ya gafartamana,
Ya yafe mana, Yayi mana rahama, Ya ALLAH
Muna tuwasulli da wannan aiki daya biya mana
bukatun mu, Ya gafarta ma mamatan mu, Ya
rage mana zafin nan na sama da kasa dana
Aljihu, Ya ALLAH Ka yiwa jagororin linzami ka
daukaka musulunci da musulmai, Ka kara
kasqanta kafurci da kafurai, Ya ALLAH Ka kawo
ma musulman kasar Somalia mafita akan bala'in
yunwar dake damuwar su.
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
25/Jimada Akhair/1438
24/03/2017.

HUDUBAH MAI TAKEN WATAN SHA'ABAN

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #WATAN SHA'ABAN
Godiya ta tabbata ga ALLAH madaukakin sarki,
Muna gode masa, Muna neman taimakon sa,
Muna kara gode masa da baiwar bamu Haske
(Qur'ani) daga garesa,
Na shaida annabi Muhammadu bawan ALLAH Ne
kuma manzo sane, Da iyalan sa da sahabbansa
da dukan wadanda suka biyo bayansu da
kyautatawa,
Yan uwa musulmi yau Khudbar mu zatayi
magana ne akan Watan sha'aban falalar sa da
kuma ayyukan da'ake bukata a aikata, Da kuma
wadanda yakamata a kaura cewa,
Watan sha'aban daya ne daga cikin watanin
musulunci, Kuma wata ne mai daraja, Wata ne
wanda ALLAH Yahada ya kasance kusa da watan
Ramadana mai alfarma!
Manzo tsira S.A.W Yana cewa ''LALLAI ALLAH
MADAUKAKIN SARKI YANA ZUBA WATA BAIWA
WATA NI'IMA A KOWANE WATA DAN HAKA MU
TASHI MU NEMETA A WATAN''
Yaku yan uwa musulmi Wannan hadisin mai
daraja yana koyar damu abubuwa guda biyu
kamar haka
1-Muyi kokari mu dinga rokon ALLAH Da dagewa
wajen bauta masa, Domin dacewa da lokachin da
ALLAH Ke raba wannan ni'imar,
Manzo S.A.W Yana yawaita azumin nafila a cikin
wannan wata mai daraja na Sha'aban! Har ma
Aisha R.A Tana cewa ''"KAI KACE YANA
AZUMTAR WANNAN WATAN NE BAKI DAYA
"" (Saboda yadda yakasance yana azumtar
wannan watan)!
Yan uwa musulmi yawaita azumtar wannan
watan zai sa dan Adam yaji sauki wajen yin
azumin farilla (Ramadana)!
2-Kowane bawa ya lizimci rokon ALLAH Kowane
lokachi, Dan dacewa da wannan lokachin, Dan
samun ingantuwar rayuwa mai albarka, Muna
Ya ALLAH Ya amintar damu tare da ruhin mu, Ya
kuma yarda damu Ameen!
A wani hadisi wanda Usama ya ruwaito yana
nuna mana muhimmancin dake tattare da azumi
a cikin wannan watan na sha'aban! Hadisin na
cewa "USAMA YANA CEWA YA MANZO ALLAH
S.A.W NAGA KANA YAWAITA AZUMI A WANNAN
WATAN (SHA'ABAN) SAI MANZO S.A.W YACE
EH NAGA MUTANE NA QIN AYYUKA A CIKIN
WATAN GASHI KUMA ANA DAGA AYYUKAN BAYI
A WATAN DAN HAKA NIKEYI DAN A DAGA
AYYUKANA AKWAI AZUMI A CIKI"
Yan uwa musulmi muyi kokari mu gyara zukatan
mu, Mu gyara ayyukan mu, Mu gyara taraiyar mu
ta yau da kullun!
Yaku yan uwa musulmi akwai wasu abubuwa
dake bijirowa a cikin addinin marar sa asali,
Wadanda shedar ke kawo mana, Daga cikin
akwai, Yana sanya mutane azumi a watan daya
gabata (Rajab), Wanda babu wani nassi
ingantacce dake magana akan haka,
Yan uwa musulmi wannan watan sunansa
Sha'aban larabawa sun kasance suna yawaita
ayyuka a ciki kama daga noma, Fatauci da kuma
komawa cikin yaqi, Saboda basu yaki a cikin
watan daya gabata!
Koda addinin musulunci yazo sai ya maida watan
sha'aban watan aiki, Amma na azumi,
Magabata na kiran wannan watan da suna watan
Qira'a, Ko kuma watan karatu, Saboda tanadi da
shiryawa zuwa watan Ramadan
Idan kai mai Qira'a ne ko tafsis yakamata kaci
gaba da yin gwaji karatun ka dan zuwan
Ramadana,
Yan uwa musulmi mu gyara bitar mu, Da tafsir
idan kai mai tafsir ne!
Ya ALLAH Ya gwada mana zuwan sa lafiya,
Watan sha'aban wata ne mai daraja kamar
manzo s.a.w yake cewa "WATAN SHA'ABAN
IDAN YAYI ALLAH NA GAFATARWA MUTANE
DUKA IN BANDA MAI GABA DA MAI SHIRKA"
Yan uwa musulmi kunji fa illar take tattare da
Shirka da kuma gaba, Dam haka duk mai shirka
ko gaba yakamata yayi gaugwar tuba,
Kada mu bari wannan garaba sar mai tarin yawa,
Mu gyara ayyukan mu ta hanyar bin abunda
musulunci yazo daci sau da qafa, Mu kiyaye
bidi'a kada muyi wa shedan biyyaya,
Akwai wasu karyayyaki da wai akwai wasu
sallalo da zikirai, Da wai akeyi a cikin wannan ,
Wanda wannan baida asali a musulunci!
Hanyoyi qalilan da aka amince a aikata a wannan
watan sune
-Tsayuwa a tauhidi
-Azumin nafila
-Yawaita rokon ALLAH
Yaku yan uwa musulmi mu fadawa iyalan mu, Da
yayan mu su sani cewa su ranka dukan azumi na
ramadana wanda ake bin su,
Dukkan wadanda keda matsala kama daga
matafiya, Mai jego, Mai haila da kuma marar sa
lafiya, Dasu ranka wadannan azumin da ake biyar
su, Domin akwai hadari ALLAH Yasamu bawa ana
binsa bashin azumi ga kuma wani ya taho,
Yaku yan uwa musulmi mu kiyaye daukar azumi
kafin kowa yadauka, Domin akwai masu daukar
azumi kafin kwana daya ko biyu, Wai da gudun
idan an samu matsalar lissafi bata shafe su ba,
To yakamata su sani cewa manzo s.a.w yana
cewa "DUK WANDA YAYI AZUMI YANA SHAKKA
YA SA6AMA BABBAN QASEEM S.A.W" Kunga
dole ne a dauka tare kuma a aje tare,
Hakama wani hadisin na cewa "AZUMIN DA
ALLAH KE KARBA SHINE WANDA AKA DAUKA
TARE KUMA AKA AJE TARE"
Musulmi kada muyi rigima, Ko bijerewa umarnin
shuwagabanin mu, Koda an samu karin bai wuce
kwana daya, Kuma akwai hadisin dake bayani kan
haka manzo s.a.w yana cewa "IDAN KUNGA
WATA KU DAUKI AZUMI IDAN KUKA DIBA BAKU
GANSA BA TO ANRUFE MAKU SHI TO KU CIKA
TALATIN"
Kungani yan uwa musulmi akwai umarni daga
manzo s.a.w! dan haka muyi biyayya ga
shuwagabanin mu dan tsira gobe kiyama,
Ya ALLAH Kabamu lafiya da zama lafiya, Kayiwa
shuwagabanin mu jagoranci, Kayi mana maganin
zafi na sama da kasa dan aljihu, Ka biya mana
bukatun mu.
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
08/Sha'aban/1438
05/05/2017.

HUDUBA MAI TAKEN WATAN RAJAB

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan WATAN RAJAB DA
HUKUNCIN SA.
Godiya ta tabbata ga ALLAH Madaukakin sarki,
Muna gode masa, Muna neman taimakon sa,
Muna neman ya kare daga sharrin kwunan mu,
Duk wanda ALLAH Ya shirya babu mai iya batar
dashi, Wanda kuma ALLAH Ya batar haqiqa babu
mai iya batar shi,
Na shaida ALLAH Shi kadai yake baida abokin
taraiya, Na shaida Annabi Muhammadu bawan
ALLAH Ne, Kuma manzon sa ne, Tsira da
amincin ALLAH Su kara tabbata gareshi da
alayen sa, Da sahabbansa da dukan wadanda
suka biyo bayan su da kyautatawa,
Yaku yan uwa musulmi muji tsoron ALLAH Kuma
mu sakankance cewa ALLAH Fa yana ganin mu a
duk abunda muke aikatawa,
ALLAH Madaukakin sarki ya zabi mala'iku a
matsayin yan aike, Hakama yafifita wasu
mutane, akan haka ya zabi wasu daga cikin
mutane a matsayin mazanni da Annabawa,
Hakama yana fifita gari kamar Makkah da
kowane gari, Hakama ya fifita wasu watanni
daga cikin sha biyu da muke dasu, Wadannan
watanni guda hudu ne sune-
Zhul hijja,
Rajab
Muharam,
Ramadan,
Wadannan watannin ALLAH Ya fifita su dan ana
ninki lada a ciki hakama ana ninka zunubi a ciki,
Ana bukatar kowane musulmi ya girmama
wadannan watanni,
Wadannan watanin ALLAH Ya karramasu kamar
yadda yake fada a cikin suratul taubah cewa
''LALLAI ADADIN WATANNIN SHA BIYU NE A
WURIN ALLAH KUMA AKWAI MAFIYA HUDU
DAGA CIKIN SU KADA SU ZALUNCI KAWUNAN
KU A CIKI''
Hakama manzon rahama yana cewa ''LALLAI
ZAMANI YANA YIN BAGA YANA TAFIYA''
Ya chanchanci kowane musulmi ya girmama su
ya kaucewa aikata duk wani sabawa ubangiji a
cikin su,
Masu hikima na cewa ALLAH Na lunka lada ga
zunubi a lokachi mai daraja (wato wadannan
watannin)
ALLAH Madaukakin sarki yana fada cewa ''SUNA
TAMBAYAR KA AKAN YIN YAQI CIKIN WATANNI
MASU DARAJA TO KAFADA MASU CEWA FADA
KISA KO FADA A CIKIN ABU NE MAI GIRMA''
Yan uwa musulmi mun shiga wata mai daraja
wato daya daga cikin wadancan watannin,
Yawaita azumi a cikin wannan watan a kullun
haramun ne,
Ibn asqalani ya rubuta littafi daya kawo karyakkin
da ake jingina hadisai wai daga annabi
Akwai hadisai na karya wadanda ake yadawa
kuma ga wasu daga cikin su.
-Annabi bai taba yin azumin watan biyu ba ajere
sune rajab da sha'aban, Wanda shima wannan
karya ne,
-Wai sunce yace falalar rajab da sauran watanni
kamas banbancin Qur'ani ne sauran littafan
annabawa wannan shima na karya ne
-Wai sunce Yace rajab watan ALLAH Shine
sha'aban, Rajab kuwa nawane, Ramadan kuwa na
al'ummata ne duk wanda yayi sallah raka'a biyu
a cikin daren farko da kuma sallar jumu'a ta
farko a cikin dare dan aljannah ne, Wannan shima
hadisin karya ne
-Hakama sunce wai manzo ALLAH Yace babu
wani da zaiyi azumi a ranar alhamis ta farko a
rajab, Sannao ya sallaci raka'a biyu za'a rubuta
mai ladar ibada ta shekara Dubu (1000), Wannan
shima na karya ne.
Ire iren su nada matukar yawa, Hakama ana
yada irin wadannan karyayyakin a shafukan sada
zumunta, Hakama dole ne a kiyaye saboda ba
kowane keda iya tsayawa ta tantance ba,
Yaku yan uwa musulmi aduk bakin dakaji
wadannan hadisan to dauka kaji bidi'a saboda
basu da asali ko kadan a cikin musulunci,
Musulmai na girmama magana wadda ta fito
daga bakin manzo ALLAH Saboda haka ne ake
fadar karya ake yadawa dan jahilai su dauka
ibadah ne su kama yi!
Idan kuka lura duk wadannan kalaman suna da
romo mai yawa wadanda ke kaiwa zuwa fadawa
bidi'ah!
Yaku yan uwa musulmi abunda akeso a sani
shine watan rajab daya ne daga cikin watanni
masu alfarma,
Mu kiyaye yada duk wadannan karyayyakin
musamman a shafukan sada zumunta,
Idan aka turo maka wadannan kalaman na karya
to kayi amfani da hadisin nan dake cewa ''DUK
WANDA YAGA ANA AIKATA WANI ABU MARAR
KYAU TO YA HAKA DA HANNUSA KO DA
HARSHEN KO KUMA YA NUNA KYAMA DA
ZUCIYAR SA, AMMA FA WANNAN SHINE
KARAMIN MATAKI NA IMANI''
Kada mu rudu da dukan abunda mukeji a daga
wajen malamai, Sannan yazama wajibi
shuwagabannin su tashi tsaye wajen hana
wandannan bidi'oin, Yakamata suyi koyi da
sayyidina Umar bn khaddab, Inda yake bi a ko'ina
dan hana masu azumtar wannan watan!
Dole ne gwamnatoci suyi koyi da hadisin nan
dake cewa ''DUKKANIN KU MAKIYAYA NE KUMA
ZA'A TAMBAYEKU KAN ABUNDA AKA BAKU
KIWO''
Yaku yan uwa musulmi shedan fa kamar
mahauniya yake ma'ana yana rikida, Ta kowace
fuska yana kokarin yaga dan adam ya mutu bai
tuba ba, Yana bullowa wa yan adam ta hanyoyi
da dama kamar su,
-Sallah Zakaga baligi yana takirus sallat idan yayi
wata ba yayin wata, ko kuma wani bayayi gaba
daya.
-Zakkah zakaga mai kudi ya tara su kamar suyi
magana amma baya fidda haqqi ALLAH, Ko kuma
yana badawa amma yana tafka kura kurai,
-Bidi'a, Ana shedan yana samun kafa dan ya
cusawa mutane wasu aiyuka wadanda a zahiri
zakaga kamar dai dai ne, Amma kuwa bidi'ah ce
subhannallah,
Yaku yan uwa musulmi shedan fa baya kyale dan
adam har sai yaga kabar duniya,
Ya ALLAH Ya azurtamu da kaucewa aikata
dukkan abunda musulunci ya haramta,
Amma babu laifi mai yin azumin litinin da
alhamis, ko kuma azumi ukku a wata yaci gaba a
wannan watan na rajab.
Daga Karshe muna rokon ALLAH Ya gafarta
mana yayi mana rahama, Ya ALLAH Ka karemu
daga aikata bidi'oi, Ya ALLAH Ka bamu lafiya da
zama lafiya, Ya ALLAH Ka karemu daga aikata
zunubai, Muna amfani da wannan damar muyi
addu'a ga mai martaba yandoton TSAFE Akan
ALLAH Ya bashi lafiya akan neman maganin da
yajeyi a kasar India, ALLAH Yasa asamu abunda
akaje nema, Muna rokon ALLAH Ya gafartawa
mamatan mu da wadanda suka samu hadarin
mota jiya da shekaran jiya da yau.
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
2/Rajab/1438
31/03/2017.

HUDUBAH MAI TAKEN JUMA'AH DA HUKUNCE HUKUNCENTA

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #RANAR_JUMU
'A_DA_HUKUKUNCE_HUKUNCETA
Muna godiya ga ALLAH Mai girman muna
godemasa a bisa ni'imar ta sanya mana ranar
Jumu'a a matsayin shugaban ranaku baki daya,
Sannam ya kebance mana ranar ta Jumu'a ga
al'ummar Manzo tsira a matsayio kyauta dan
muyi zikiri da ambaton ALLAH
Sallati da tsira su kasa tabbata ga mafificin
halitta Annabin mu Muhammad Sallallahu alaihi
wassalam.
YAKU YAN UWA MUSULMI Khudbar mu ta yau
tana magana ne akan Ranar JUMU'A
Yan uwa uwa musulmi ku sani ita ranar Jumu'a
rana ce ta musamman da ALLAH Ya bamu ita a
matsayin kyauta, Dan mu kara dagewa wajen
bauta masa, Saboda mune Al'umma datafi
kowace fifiko a wajen ALLAH
Hakika Hadisi ya tabbata daga Manzo tsira cewa
''MU WADANNAN AL'UMMAR MUNE NA KARSHE
KUMA MUNE NA FARKO A SHIGA AL'JANNAH''
Yahudawa Sun zabi ranar Assabar a matsayin
mafificiya, Su kuma Nasara sun zabi Lahadi A
matsayin mafifiyar rana!
Mu kuma Al'ummar Musulmi ALLAH Yazabar
mana Ranar Jumu'a a matsayin mafificiya.
Hakika ranar Jumu'a sama take ga kowace rana
daga cikin kwanaki bakwai.
Manzo tsira yana cewa a ''FIYAYYEN YINI DA
RANA KE FITOWA ITACE RANAR JUMU'A ''
YAN UWA MUSULMI Saboda girma da matsayi na
wannan ranar, A ranar ne aka halicci kakan mu
Annabi Adam (A.S),
Hakama A ranar ya shiga Aljannah, A kuma ranar
ya fita Aljannah,
YAN UWA MUSULMI Ranar Jumu'a ne za'ayi
tashin kiyama,
Idan ka cire mutun da Aljani to dukkanin halittu
suna cikin fargaba idan ranar Jumu'a tazo
saboda suna tsammanin a ranar kiyama zata
tsayu.
YAKU YAN UWA MUSULMI
Manzo tsira yana girmama wannan rana, Yana
yawaita salati ga kansa, Dan haka yazama Muma
wajibi garemu yawaita salati gareshi, Dan salati
Gareshi kamar Addu'a ce.
Daren Jumu'a nada matukar falala wato (Cikin
dare ranar Alhamis) Ana bukatar yawaita salati a
daren, Ana Bukatar kowane musulmi ya yawaita
neman lada a dare domin shirin zuwan ranar,
Kamar misali Daren Sallah ne da ake yin komai a
ranar Jajirbiri!
YAKU YAN UWA MUSULMI Akwai Wasu ayyuka
da Manzo tsira ya kasance yake aikata a cikin
dare da rana ta Jumu'a
1-Annabi na karanta surutul Sajada, Da kuma
Suratul kiyama, A cikin sallar asuba ta wannan
daren, Saboda wadannan surorin suna bayani
game da ranar kiyama,
Daren Jumu'a nada matukar falala, Kamar yadda
yazo a cikin hadisin sa ''MAFICIN SALLAH ITA
CE SAMUN SALLAR ASUBA A CIKIN JAM'I''
Yaku muminai kunji wannan falalar mai matukar
amfani wadda yakamata mukiyaye mu dinga
halarta sallar asuba cikin jam'i!
2-An so yawaita salati a ranar yana da kyau
takaita duk wata ibadah dan mukeyi a ranar dan
samun wannan garaba sar.
Domin salati kamar addu'a ce garesa,
Manzo Tsira da kansa yana fada cewa ''KUSANI
RANAR JUMU'A AKA HAIFI ADAM KUMA RANAR
ZA'A BUSA KAHO''
3-Anaso kowane musulmi yayi wanka, Yayi tsafta
yan sanya kaya mafi kyau, Ya sanya turare.
4-Aswaki
5-Zuwa massallaci da wuri
6-Inda hali kazo kasa.
Kamar yadda hadisi ya tabbata cewa ''BABU
WANI DA ZAIYI WANKA RANAR JUMU'A
SANNAN YAZO YA SALLACI SALLAR WAJIBI
FACE SAI AN GAFARTAMASA HAR ZUWA WANI
SATIN''
YAN UWA MUSULMI Ya chanchanta muzama
cikin masu zuwa da wuri saboda samun damar
zaunawa a massallaci dan yin salati, Sannan
kuma Mala'iku suna yiwa wanda ke zaune
massallaci addu'a.
To amma abun takaici wasu na kauracewa zuwa
da wuri, Zakaga wasu basu wuri sai anfara
khudbar, Wasu kuma sai anyi rabi wasu kuma sai
an gama, Wasu kuma sai Tada sallah, Kai wasu
ma sai an yi raka'a daya!
Shedan ya hana musulmi more ma wannan
romon!
Yaku yan uwa musulmi muji tsoron ALLAH .
Hadisi daga manzo tsira na cewa ''DUK WANDA
YAYI WANKA IRIN NA JANABA (Dama wankan
tsarki iri daya ne a musulmi) ZA'A BASHI LADAR
WANDA YABADA KYAUTAR RAKUMI, WANDA
YAZO NA BIYU ZA'A BASHI LADAR WANDA
YABADA SADAKAR SA, NA UKU KUMA ZAI SAMU
LADAR WANDA YABADA KATON RAGO NA HUDU
KUWA ZAI SAMU LADAR WANDA YABADA KAZA/
ZAKARA NA BIYAR KUMA ZAI SAMU LADAR
WANDA YABADA KWAI''
Wanda kuma sai da limamin yazo ba'a sanyi shi
cikin lissahi.
Akwai abubuwa guda biyar da ake saran da adam
zai dace da Aljannah a ranar jumu'a akwai,
1-Gaida marar lafiya (ranar jumu'a)
2-Zuwa jana'iza (ranar jumu'a)
3-Azuni
4-Zuwa Massallaci da wuri
5-Inta bawa ko baiwa, (Taimakawa wajen biyan
bashi)
Tafiya Kasa zuwa massallaci ranar jumu'a nada
matukar falala kamar yadda yazo a cikin hadisi
cewa ''DUK WANDA YATASO DAGA GIDA DA
KAFAFUNSA SUKAYI KURA (DAUDA) TO
KAFAFUN SUN HARAMATA SHIGA''
JUMU'A Nada sharadi kamar haka
Yin shiru a lokachin huduba, Kamar yadda ALLAH
Madaukakin sarki yake cewa ''IDAN ANA
KARANTA QUR'ANI KU SAURARA WATA QILA SU
SAMU RAHAMA'' Kunga kuma huduba ana kawo
ayoyin Qur'ani. Kai wajibi ne yin shiru idan ana
huduba!
Banda wasa, ko gaishe gaishe,
Ba hallata kayi tafiya dab da lokachin Jumu'a sai
inda ta zama wajibi, Saboda karamawa da
girmama wannan ranar!
Yana da kyau karanta suratul kahfi a ranar
Jumu'a, Saboda Annabi na cewa ''DUK WANDA
YAKARANTA SURATUL KAHFI RANAR JUMU'A
ALLAH ZAI HASKAKA MASA HAR WANI SATIN''
Muna rokon ALLAH Tare da tuwassalin da
wannan khudbar ka biya mana bukatun mu, Ya
ALLAH Ka baiwa Mai martaba Emir na Tsafe
lafiya, Kasa asamo abunda akaje nema a kasar
india, Ya ALLAH Kasanya garin mu Albarka ka
yafemana kayi jagora ga shuwagabbani mu Baki
daya, Ka jikan mamatan mu Baki dayan su.
ALHAMDULILLAH
©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
18/Jimada Akhair/1438
17/03/2017.

HUDUBAH MAI TAKEN KALMAR SHAHADA KASHI NA BIYU

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #KALMAR_SHAHADA
KASHI NA BIYU
Godiya ta tabbata ga ALLAH Madaukakin sarki,
Muna gode masa muna neman yakare mu daga
sharrin kawunan mu, Tsira da aminci su kara
tabbata ga Manzon rahama Muhammad S.A.W
da alayen sa da sahabban sa, Da dukkan
Wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, Har
zuwa ranar sakamako.
A makon daya gabata malan yafara khudba akan
kalmar shahada, Inda yakawo mana sharudda
hudu da cikin takwas na kalmar shahada,
To a wannan makon ma Insha Allahu zamuji
cikon hudun tare da jin karin bayani, Dan amfana
da kuma kara fahimta ga yan uwa musulmi,
YAKU YAN UWA MUSULMI
Ita fa wannan kalmar ta LA'ILA HA ILALLAH A
Halicci duniya ne dan baki daya ne dan ita,
Hakama An halicci mutane da aljannu kaf dan
wannan kalmar haka Sama da kasa baki daya
duk an haliccesu ne dan wannan kalmar!
Wannan kalmar da ita ake banbanta kafuri da
muminin musulmi,
Wannan kalmar tana da rukuni guda biyu.
1-Korewa
2-Tabbatarwa
Ma'anar Korewa shine LA'ILAHA Babu wanda ya
chanchanta da bauta kowanene
IL'LALLAH (Tabbatarwa) Sai Allah madaukakin
sarki.
Yakamata Ko kuma wajibi kowane musulmi ya
dinga hakaito wannan ma'anar a lokacin da yake
furta wannan kalmar,
Ma'anar kalmar gaba daya shine BABU ABUN
BAUTAWA NA GASKIYA SAI ALLAH
ALLAH S.W.T Yafada cikin Suratul hajj cewa
''LALLAI SHI ALLAH SHINE WANDA YA
CHANCHANCI A BAUTAW AL-ALIYU AL-KABIRU''
Dukkan wani abun bautawa a duniya gaba daya
bai cika Al-aliyu ba, kuma bai cika Al-kabiru ba,
Shi kuwa duk wanda bai cika da wadannan
matakan ba to bai chanchanci bauta ba,
Tauhidi baya taba cika har sai an san wannan
kalmar, Kuma an dabbaka ta.
Dukkan Annabawan da Allah ya aiko har da
Manzo S.A.W Sunzo ne dan jaddadda wannan
kalmar.
Ba'a bautawa kowa sai Allah, koda Annabi ne, ko
mala'ika, Ko malamai ko waliyai ko kabarin su
Domin suma Allah sukabi har suka zama waliyai!
YAKU YAN UWA MUSULMI
Ga chi gaban sharudda
5-Idan ka fadeta yakasance kanason ALLAH Har
a zuciya ba'a baka kawai ba,
Ana fadan tane kawai dan zikiri bawai dan sanyi
jin haushi ga wani ba, Idan ka fadeta da wata
niya to tabba baka da lada.
A cikin sahihul bukhari ya ruwaito daga Manzo
S.A.W Cewa duk wanda ya kammala wasu
abubuwa guda ukku zai samu dandano na imani,
Akwai son ALLAH Dakuma son Manzo S.A.W
Muddin kanason cikawa da imani kaso ALLAH
Fiye da komai Ka kuma son Manzo ALLAH S.A.W
Fiye da kowa.
ALLAH Madaukakin sarki na cewa ''IDAN KUN
KASANCE KUNA SON ALLAH TO KUBINI ALLAH
ZAI SOKU''
YAKU YAN UWA MUSULMI
Dole ne a matsayin mu na musulmi mu kasance
muna son Alqur'ani da Hadisai na Manzo ALLAH
A koda yaushe ka kasance kana karatun Qur'ani
Kana karatun Hadisi.
6-Dole ka mika wuya ga Kalmar
Dole a mika wuya ga Kalmar Ma'ana Bin duk
abunda ke halal, Da kuma kauracewa haram,
Biyayya ga duk abunda kalmar ta kunsa.
A cikin suratul Lukman ALLAH Na cewa ''DUK
WANDA YA MIKA WUYA HAKIKA YAYI RIKO DA
IGIYA MAI KARFI''
7-Ka karbi duk Abunda kalmar tazo dashi
Ma'ana yarda da ita, Da dukkan abunda ta kunsa
baki daya,
ALLAH Na cewa ''KAFURAI SUNA GIRMAN KAI
DA ITA(KALMAR SHAHADA) SUNA CEWA YANZU
ZAMUBAR ABUNDA MUKA GADA MU BAUTAWA
ABU DAYA TAK''
Wannan kuwa shine yasanya kafurai wuta ma'ana
kin yadda da ita.
8-Dolene kafurcema dagutu
Ma'ana duk wani abu da wasu ke bautawa ka
kaurace masa,
Allah na cewa ''DUK WANDA YA KAFURCEWA
DAGUTU YAYI IMANI DA ALLAH YAYI RIKO DA
WATA IGIYA MAI KARFI''
YAKU YAN UWA MUSULMI
Akwai hadisai da yawa daga Manzo rahama
S.A.W Wadanda ke koyar damu falalar wannan
kalmar
Manzo S.A.W Yana cewa ''DUK WANDA YAFADI
KALMAR LA'ILAHA ILLALLAH WAHADAHU LA
SHARI KALA LAHUL MULKU WA HUWA ALA
KULLI SHAI'IN QADEER'' Hakika za'a kankare
masa zunubansa koda sunyi girman dutsen uhud.
A wani hadisin kuma yana cewa ''FIYAYYEN
ABUNDA NAKE FADA SHINE ''DUK WANDA
YAFADI KALMAR LA'ILAHA ILLALLAH
WAHADAHU LA SHARI KALA LAHUL MULKU WA
HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER''
Duk wanda yafadi wannan a rana sau dari za'a
yafemai zunuban sa duka koda sunyi yawan
kunfar teku.
Duk wanda yafadi ''''DUK WANDA YAFADI
KALMAR LA'ILAHA ILLALLAH WAHADAHU LA
SHARI KALA LAHUL MULKU WA HUWA ALA
KULLI SHAI'IN QADEER'''' za'a kankare masa
zunubai dubu, kuma za'a basa lada dubu.
Hadisan nada yawa sosai wadannan misalai ne.
Daga karshe muna rokon Allah yasa kalmar mu
ta karshe ta kasance wannan kalmar, Ya gafarta
mana, Yajikanmu yayiwa jagororin ja gaba.
Ameen
ALHAMDULILLAH
©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
04/Jimada Akhair/1438
03/03/2017.

HUDUBAH AKAN KALMAR SHAHADA

HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #KALMAR_SHAHADA
Godiya ta tabbata ga ALLAH Muna gode masa
muna neman taimakom wanda ALLAH Yashiryar
Shine shiryayye, Wanda ALLAH Yabatar Babu mai
iya shiryar dashi,
Hudubar Yau tayi magana ne akan Wata
tsaddadiyar kalma wato KALMATUSH SHAHADA !
Ita wanman Kalmar mai girman ita ce mabudi na
shiga musulunci, Da kuma banbatawa tsakanin
kafurci da imani,
Wannan Aya ALLAH Madaukakin sarki ya shaida
kanta kamar yadda Yafada a cikin Suratul Ali
imran ALLAH YA SHAIDAR CEWA BABU WANDA
YA CHANCHANTA DA BAUTAWA SAI SHI
ANNABAWA SUN SHAIDA MALA'IKU SUN
SHAIDA MALAMAI MA SUN SHAIDA
Yaku yan uwa musulmi musulunci mutun baya
ingantuwa har sai ya yarda da kalmar,
Ita ce kalmar shahada ana ce mata KALMAR
YAKINI
Wannan kalmar ita ke banbamta kafurci da
musulunci
Hadisi yazo daga manzo tsira cewa DUK WANDA
YAFADI KALMAR SHAHADA YANA
SAKANKANCEWA DA ITA HAR YA MUTU ZAI
SHIGA ALJANNAH.
Annabawan da ALLAH Madaukakin sarki ya tura
zuwa ga jama'a dukansu dan jaddadda KALMAR
SHAHADA
Kamar yadda Aya tazo cewa HAKIKA MUN AIKA
DA KOWANE ANNABI ZUWA GA AL'UMMAR SA
DAN SU BAUTAWA ALLAH SU KAFURCEWA
DAGUTU''
Misalin ALLAH Madaukakin sarki ya aikawa
kafuran Al'umma da manzanni
Samudawa ALLAH Ya aika masu da Annabin
Salihu dan yayi kira akan tsaida kalmar Shahada
Hakama Annabin Shu'aib an aikasa ga mutanen
madiya Dan yayi kira akan kalmar shahada.
Annabawa da manzanni dukkansu an aiko su dan
isar da wannan Kalmar ta LA'ILAHA ILLALLAH.
Hatta mafificin halitta Manzo sallallahu alaihi
wassalam Yazo ne dan isar da KALMAR
SHAHADA
Yaku yan uwa musulmi Kusani wajibi ne ga
musulmi yasan fassarar ta, bawai fadin ta ba
kadai,
Kuskurene Fassar da hausawa kewa KALMAR
SHAHADA Cewa
-Babu sarki sai ALLAH
Ko kuma masu cewa
-Babu iko sai na ALLAH, Wanda duk wannan
Fassarar kuskure ne.
Yaku yan uwa musulmi KALMAR SHAHADA Tana
da sharudda guda Takwai 8
1-Dole ne kasan Ma'anar ta
Sanin Ma'anar ta na nufin Haddaceta da sanin
hakikan nin fassarar ta da abunda ta kunsa.
2-SAKANKANCEWA
Ma'ana yarda da duk abunda ta kunsa banda
shakku ko ko kwanto, Sau daya a wannan
zamanin wasu na walwale KALMAR SHAHADAR
Su ta hanyar kalaman su da ayyukansu, kamar
fadar wata kalmar shirka, ko kuma aikata shirka
kamar sihiri da tsafe-tsafe Da zuwa wajen yan
duba ko malaman tsibbo ko bokaye.
3-Dole ne kayi Zikiri da ita
Ma'ana fadar ta a matsayin zikiri wato ambaton
Dan yin zikiri Bawai fadar ta dan nishadi ba, ko
dan baiwa wani haushi ko kuma ana fadar ta ana
rawa, dukkan wannan kuskure ne, Hakama
hadata da wata daudar duniya Misali kaga wata
mota mai kyau sai kaji an fadi LA'ILAHA
ILLALLAH
Kunga wannan kuskure a hada daudar duniya da
wannan babbar kalmar ita fa duniya ALLAH YA
TSINE MATA DUK ABUNDA KE CIKINTA IN
BANDA AMBATTON ALLAH DA ZIKIRIN SA
4-Fadar ta da gaske
Ma'ana fadar ta gaske bada niyar wasa ba ko
kuma ganganci ko kuma karya kamar yadda
munafukai sukeyi a lokachin Annabi Kamar yadda
ALLAH Yafada a cikin Suratul munafikun ''IDAN
MUNAFUKAI SUNZO WAJENKA SUNA CEWA SUN
SHAIDA KAI MANZO ALLAH NE TABBAS ALLAH
YA SHAIDA KAI MANZO NE AMMA SU
MUNAFUKAI MAKARYATA NE''
5-Dole kaso kalmar
Ma'ana kaso kalmar har a zuciya ta hanyar son
tane zaka ki tare da kauracewa wanda baya
sonta.
8-Ka yarda da ita
Ma'anar yarda da ita da duk abunda ta kunsa
dan hakika duk wanda yafadeta amma bai yarda
da ita to hakika shima munafuki ne kuma za'a
hada shi da munafukai na lokachin magabata
ALLAH Madaukakin sarki yana cewa ''WANDA YA
KAFURCEWA DAGUTU YAYI IMANI DA ALLAH
HAKIKA YAYI RIKON DA WATA IGIYA MAI KARFI
WADA BATA YANKEWA''
Igiyar da mai karfi ita ce KALMAR SHAHADA
Yaku yan uwa musulmi duk wanda ya furta ta to
dole ne yasan ma'anar ta
ALLAH Madaukakin sarki yana cewa ''BABU
MASU SHIGA ALJANNAH SAI WANDA YA
SHAIDA DA KALMAR SHAHADA.
Ba makawa saika san ma'anar ta
Akwai kura kurai da wasu keyi na furta ta
bagatatan wasu zaka gansu suna furta ba kan
gado wanda duk abunda ke duniyar nan ta fishi
daraja a wurin ALLAH Idan da duniya nada daraja
wajen ALLAH Da kafuri ko ruwan sha bai samu,
Wani hadisi yana cewa ''DUKAN WANDA YA
MUTU YASAN MA'ANAR KALMAR SHAHADA ZAI
SHIGA ALJANNAN
Wata rana wani yazo ya tambayi manzo tsira
cewa Wanene zai samu cetonka sai manzo tsira
yayi shiru (dan yaji ta sahabbai) sai abi huraira
ya tambayi ANNABI Yaya,
Sai manzo tsira yace dama nasan kai zaka fara
magana ''NA SHAIDA CEWA NI MANZO ALLAH
NE KUMA NA YARDA DA ALLAH HAKIKA DUK
WANDA YA MUTU YA SHAIDA WANNAN KALMAR
ZAI SAMU CETONA''
Imam bukhari yayi babi na musamman daya
sanyawa suna babi Dan ya nuna muhimmancin
sani abu,
Mai ahadari na cewa ''Baya halatta kai aikata
wani aiki har sai kasan hukuncin ALLAH Akansa''
Ya ALLAH Kasamu daga cikin muminai, masu
imani, masana KALMAR SHAHADA, Ka shiryamu
tare da iyalanmu,
Ya ALLAH Ka taimaki musulunci da musulmai, ka
kasqanta kafurci da kafurai, ka yiwa
shuwagabbani jagoranci kabar mu mutu muna
musulmi masu imani.
ALHAMDULILLAH

©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
26 /05/1438
24/02/2017.