FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #FALALAR WATAN
RAMADAN DA ABUNDA YA KUNSA
Godiya ta tabbata ga ALLAH Wanda ya sanyawa
bayin sa alamomi da zasu zama alama garesu da
yin bauta a lokachin,
Tsira da aminci su tabbata ga wanda ALLAH Ya
aiko da gaskiya da iyalansa da sahabbansa da
dukkan wadanda suka biyo bayansa da
kyautatawa sallallahu alaihi wassalam,
Yan uwa musulmi muna fuskantar wani yanayi
mai matukar alfanu, Wanda yana kyau muci ribar
wadannan kwanuka mu yawaita taimakon kanmu,
Mu yiwa kawunan mu hisabi, Yakamata muyi
amfani da wannan dama wajen neman gafara da
yafiya daga ubangiji ALLAH,
Watan ramadana wata ne mai alfarma wanda
ALLAH Yasanya shi daga cikin rukunan
musulunci, Ramadana wata ne na tausayi da
rahama da taimakon juna.
A cikin watan ramadan akwai wata rana wadda
tafi dare dubu,
Yan uwa musulmi mu karrama wannan watan da
abubuwa guda biyu (2), Na daya ALLAH Ya ara
mana rayuwa ta kawuwa wannan watan, Sai
kuma zuwan watan na ramadan mai albarka,
Yan uwa musulmi akwai abubuwan da yakamata
mu aikata a cikin wannan watan mai kamawa,
Daga cikin su akwai;
-Mu roki ALLAH Ya yarda damu, Ya karbi dukkan
ibadun da mukayi, Duk wanda aka karbi ibadun
su a cikin watan ramadan to yayi murna yayi
farin ciki,
Lallai kololowar murna ita ce kayi murna da
zuwansa, Da kuma ni'imar halartar sa, Akwai
wanda yafara jin kanshin sa Amma ALLAH Bai
nuna masa ba, Baya daga cikin addini yin murna
walau ta samun matsayi ko dukiya kamar yadda
aya take cewa "GASUNAN SUNA FARIN CIKIN
DAN SAMUN DUNIYA ALHALI BA KOMAI BACE
IDAN KA KWATANTA DA LAHIRA"
-Kiyaye salloli na farilla a cikin lokachi, Idan har
baka sallah cikin jam'i to yakamata kayi amfani
da watan ramadan dan koya da yin sallah cikin
jam'i
-Kaucewa yin sabo, Kaucewa aikata sabo kowane
irin, Ba kauracewa ci da sha ne kurum azumi ba,
A'a harda kiyaye gabobi baki daya daga aikata
zunubai,
-Mai hankali baligi ya sanya a ransa zaiyi azumi
dan ALLAH, Dan kwadayin lada, Da kuma
kaucewa fadawa azabar ALLAH.
Muddin aka samu mutun kawai zai yi azumi dan
yazama dole, Dan kada ace wane baiyi to akwai
matsala, Yakamata a gyara dan samun ladar da
ake nema.
Azumin watan ramadan yana farawa ne da zarar
wata sha'aban yakai ashirin da tara idan ba'a ga
wata ba kuma yakai talatin, kamar yadda hadisi
daga manzo rahama na cewa "KUYI AZUMI IDAN
KUNGA WATA KU AJE IDAN KUNGA WATA"
Idan har mai alfarma sarkin Musulmi yabada
umarnin daukar azumi, To kada ayi wata wata
wajen dauka,
Idan aka bada umarni to akwai abubuwan da
yakamata ayi kamar;
-Kulla niyyah a zuciya, Ba ambatawa da baki ba,
-Sallar tarawihi, Ko a daren yau za'a iya fara
tarawihi dama ana bukatar a tari wannan watan
da aiyuka na alheri dan su zame ma jiki, Idan
watan yazo zaka iya,
>Yan uwa musulmi abunda ake cewa azumi shine
barin chi da sha da kame gabobi, ALLAH
Madaukakin sarki na cewa "KUCI KUSHA HAR
SAI BAKIN ZARE YA FITO DAGA ALFIJIR"
=Hakama yakamata ladanai kuji tsoron ALLAH
kada ladanai su kuskura su kira sallah kafin
lokachi yayi ko bayan lokachi, A yanzu muna
cikin yanayi na damina wanda gari ke laulayewa,
Jiya anan Tsafe anyi ruwa, Wasu ladanai sunyi
kiran sallah tun karfe 6:30pm, Maimakon
6:55pm.
Anan fa mutane uku ne keda laifi na daya Ladani
shi da ya kira sallah kafin lokachi yayi,
Sai kuma limani wanda shine jagora yaje yabada
sallah,
Sai kuma mamu wanda yakamata ku lura da
jadawali, Kafin sallah!
Anan jahar, Gwamnati tana raba jadawali a duk
wani massallaci komai yadda yake cikin lungu,
Kada kuma sai ladani yaci yakoshi har lokachi ya
wuce sannan yace zai kira sallah,
Idan ladani ya kira sallah lokachi baiyi ba, To
Ladani ne keda alhaki na karewar azumin su,
Alfijir na fitowa ne 04:55/6, Magrib 06:55, duk
yanayi n chanzawa, A kula sosai idan ladanai
sunyi kuskure mafita kurum a dinga diba
jadawalin da gwamnati ke kawo, Kowane lokachi
basai radaman ba.
-Tarawihi babbar sunnah ce dake nuna alamar
tsayawar ramadan, Ana samun falala a ciki.
Limamai aji tsoron ALLAH
Limamai aji tsoron ALLAH
Limamai aji tsoron ALLAH
Sau da yawa zakaga limamai na wulakanta
sallah, Ta hanyar yin qoton kurciya da yin ta
yadda aka ga dama,
Manzo rahama na cewa "KUYI SALLAH KAMAR
YADDA KUKAGA INAYI"
To sai ayita gwargwadon hali,
Wani mutun yazo yana sallah yagama yazo
wajen manzo ALLAH Sai manzo s.a.w yace ka
koma kayi sallah dan bakayi sallah ba, Sai da
akayi sau 3, Daga nan manzo s.a.w ya gwada
masa yadda zaiyi da kyau ta hanyar jeranta
kira'a da yi anatse da cikin ruku'u da sujjada,
=Yana da kyau a rage sautin amsa kuwa (Loud
speaker), Domin kada karatu na chan dana chan
su hade sai kaji duk abu ya rikice.
Wata rana Manzo s.a.w ya shigo massallaci ya
tarar kowa na sallar sa anan yahada su kan
limami daya wato Ubaiy bn Ka'af R.A
Hakama wajen yin tahujjud akiyaye.
Yan uwa musulmi manzo s.a.w ya kai karshe
komai game da ganin wata, Idan an samu rikici
to ko kaine ko wani ne ya rikice, Manzo rahama
s.a.w na cewa "IDAN KUKA DAUKA BA'A GANI
BA KU CIKA TALATIN"
Idan sarki musulmi ya bada sanarwar angani ka
sallama kawai ka dauka,
Kasar Saudiyya Yau watan su talatin yake amma
mu 29, Idan mungani zamu dauka anan Najeriya,
Yan uwa musulmi a cikin watan ramadana ana
bukatar taimakon juna, A taimakawa talakawa da
abinci koda koko da kosai ne, Domin wani ko
abincin buda baki baida shi, "Manzo s.a.w ya
kasance idan watan ramadan yazo yakan yawaita
alheri kai kace iska ne ya taso".
Ka taimaki yan uwa musulmi anan za'a gane
kana taimako.
Kuma taimako bawai sai masu kudi ba kowa
yasan wanda yafi sai ka taimaka masa, ALLAH
Madaukakin sarki na cewa "KU TAIMAKA A KASA
NI DAKE SAMA ZAN TAIMAKA MAKU"
Muna rokon ALLAH Sunayen kyawawa, Tsarkaka
ya biya mana bukatun mu, Yayi mana gafara da
rahama, Ya karbi ibadun mu wadanda mukayi da
wadanda zamuyi,
Ya ALLAH Yabaiwa shugaban kasa da Mai
martab emir na Tsafe lafiya, Yayi jagora ga
shuwagabanni mu, Ya shiryamu hanya madaidai
ciya.
ALHAMDULILLAH
©®IBRAHIM RABILU TSAFE ZAMFARA
29/Sha'aban/1438
26/05/2017.
No comments:
Post a Comment