Wednesday, 6 December 2017

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 002

*GORON SALLAH 1438/2017*

*_SHI’AH DA AKEEDOJINTA_*


_Wallafar:_  *_Malam Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)_*

*Fitowa Na biyu(00)2*



“`√ ASALIN SHI’ANCI.

     Shi’anci ya bayyana ne a lokacin
halifancin Usman bin Affan ta hanyar
Abdullahi bn Saba’a alyahudi alyamani
mai tsananin kiyayya da musulunci.
Hakika ya watsa a tsakanin musulmai
cewa Aliyu shine yafi cancanta da
halifanci kuma Abubakar da Umar zalunci
sukayi domin Aliyu ne Manzon Allah yayi
ma wasiyya kamar yanda annabi Musa
yayi ga Yusha’u bin Nun. Wannan
mummunar Magana ta watsu a tsakanin
sashen wasu jahilai, har suka wuce wuri
game da Aliyu har suka qudurce cewa
Aliyu Allah ne.
Malaman tarihi sun ambata cewa Aliyu ya
dinga kona su da wuta
Aliyu ya fada a cikin diwanin sa na
wakoki yace”
“Yayin da naga al-amarin al-amarine mai
muni sai na hura wuta na kira yarana”
Ma’ana: ya hura wuta ya kira yaransa ya
umurcesu dasu dinga sanya yan Shi’a a
ciki sai suka ce ai babu mai kona mutane
da wuta sai ubangijin wuta. Malamai sun
fada cewa daga cikin sabubban bayyanar
shi’anci shine keta da kiyayya da
kabilanci da farisawa (Mutanen Iran)
masu bautar wuta sukayi akan Larabawa
da Abubakar da Umar saboda sun karya
daular Farisawa
Yana daga cikin abun daya kamata mu
sani cewa Abu lu’uluata Majusin nan duk
da cewa ba musulmi bane bautar wuta
ya keyi mutanen Iran sun samar da wata
hubbare a kasar Iran a garin Kashan suna
yi masa dawafi domin girmamawa zuwa
gareshi akan abun da yayi masu na
kashe Umar. Wannan yana nunawa karara
cewa shi’anci kabilanci ne tsantsa ba
musulunci ba.
Shi’anci ya cigaba da yaduwa a lokacin
halifancin Aliyu bayan kashe Hussaini (R)
shi’anci bai gusheba yana girmama har
ya zama wata mazhaba da miliyoyan
mutane suke bi a matsayin addini, wajibi
ne muyi hattara da yaduwar shi’anci a
cikin duniya.


√ AKIDOJIN SHI’A.

Shi’a tana da akidu masu yawa zamu fadi
kadan daga cikin su domin takaitawa

1. KAMANCECENIYAR SHI’A DA
YAHUDAWA DA KIRISTOCI.

Akidar shi’a tayi kama da ta yahudawa da
kiristoci domin duk musibar da take a
cikin Shi’anci itace musibar da take a
cikin Yahudanci.

* YAHUDAWA; sun ce baza’ayi jihadi
domin daukaka kalmar Allah ba har sai
Dujal ya bayyana.

* YAN SHI’AH; su ma ‘Yan Shi’a su na
cewa baza’ayi jihadi domin daukaka
kalmar Allah ba har sai mahadi ya fito Ma’ana: a wajen yan Shi’a duk jihadin da
Manzon Allah yayi da Sahabbansa har
zuwa Sheik Usman bin Fodiyo duk
wahalar banza ce kuma shirme ne.

* YAHUDAWA;  suna jinkirta sallah har
zuwa fitowar taurari.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a suna
jinkirta sallar Magariba har zuwa lokacin
sallar Isha’i.

* YAHUDAWA; suna karkacewa daga
alqibla suma.

* YAN SHI’AH; ‘Yan Shi’a suna karkata
kansu daga alqibla.

* YAHUDAWA; sun juyar da Attaura.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a sun juyar
da Alqur’ani.

* YAHUDAWA; sun haramtawa kansu cin
kifi.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a sun
haramtawa kansu cin zomo.

* YAHUDAWA; basu yin shafa akan huffi.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a basu yin
shafa akan huffi.

*YAHUDAWA; suna kiyayya da Mala’ika
Jibril.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a suna
kiyayya da Mala’ika Jibril suka ce yayi
kuskuren kawo wahayi maimakon ya kai
shi ga Aliyu sai ya kai shi ga Annabi
Muhammad kaga anan suna tuhumar
manzancin Manzon Allah (SAW).

*KIRISTOCI; suna halatta auren mata ba
tare da sadaki ba.

* YAN SHI’AH; suma ‘Yan Shi’a sunayin
auren mutu’a.

Yahudawa da Kiristoci sunfi ‘Yan Shi’a da
dabi’o’i guda biyu.

* YAHUDAWA;  An tambayi yahudawa
suwa nene mafifita a cikin addinin ku?
Suka amsa da cewa sahabban Annabi
Musa.

* KIRISTOCI; suma kiristoci da aka
tambayesu suwaye mafifita a cikin
addinin ku? Sun amsa da cewa sahabban
Annabi Isah.

* YAN SHI’AH; Da aka tambayi ‘Yan Shi’a
suwa nene mafi sharri a cikin addinin ku?
sai suka amsa da cewa Sahabban Annabi
Muhammad(S.A.W).

An umurce su suyima sahabban Annabi
Istiqfari amma sai suka zage su.

Wannan yana nuna Yahudawa da kiristoci sunfi
‘Yan Shi’a girmama Annabawansu da
Sahabban su, kuma yana nuna irin yanda Shi’a ke nuna kiyayya ga Sahabban Annabi karara.

Wannan yana nuna cewa akidar Shi’a dai-
dai take da ta Yahudawa da Kiristoci.

ALLAH YA KARA SHIRYAR DAMU AKAN
HANYA MADAIDAICIYA, WADANDA KE
CIKIN WANCAN BATA KUMA ALLAH YA
SHIRYESU IDAN MASU SHIYUWA NE.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU.“`

HAKKIN MALLAKA©
*_Hashim Sirajo Uba Tsamiya
(ABU~SINÃN)_*
+2348064734911

No comments: