Wednesday, 6 December 2017

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 001


*SHI’AH DA AKEEDOJINTA*

WALLAFAR;  *_Malam Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)_*

*GABATARWA*

“`Godiya ta tabbata ga Allah, muna
godemasa, muna neman taimakonsa,
muna neman gafararsa, muna neman
tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da
munanan ayyukan mu, wanda Allah ya
shiryar babu mai batar dashi, wanda
kuma Allah ya batar babu mai shiryar da
shi.
Na shaida babu abun bauta na gaskiya
sai Allah, shi kadai yake baya da abokin
tarayya, kuma na shaida Annabi
Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa
ne
Bayan haka, mafi gaskiyar zance shine
littafin Allah, fiyayyar shiriya ita ce
shiriyar Manzon Allah, mafi sharrin
alamurra sune wadan da aka kir-kiro a
cikin addini, dukkan abunda aka kirkiro a
cikin addini bidi’a ce dukkan bidi’a bata
ce, dukkan bata makomarta ita ce wuta.
Dalilin rubuta wannan ‘Yar takaitacciyar
nasiha shine na gabatar da huduba a
Masallacin Juma’a na Abu Huraira dake
Area 2 a Garin Tsafe mai taken Shi’a da
Hadarorinta, sakamakon haka ne wasu
‘yan uwa suka nemi da in fassara ta
zuwa harshen Hausa domin amfanin yan
uwa musulmi
Ina rokon Allah (SWT) ya azurta ni da
ikhlasi a cikin wannan aiki, kuma ya
amfanar dashi ga yan uwa musulmi.
√ MICECE SHI’A???
Shi’a daya ce daga cikin kungiyoyin bata,
da ake kira da sunaye daban-daban, ana
cemata Rafida, ko Ja’afariyya, ko Isna
Ashariyya.
√ SUWAYE ‘YAN SHI’A???
‘Yan Shi’a sune masu kokarin jingina
kansu zuwa ga Aliyu bin Abi Dalib, suna
kudurce cewa, Halifanci da Imama suna
tabbata ne kadai ga Aliyu bin Abu Dalib
bayan Manzon Allah, basu yarda da
Halifancin Abubakar da Umar da Usman
ba. Cibiyoyin su ta duniya a yanzu tana
kasar Iran da Lebenon, da Iraki da Syria
da Afganistan, tana da rassa a wasu
kasashen Africa musamman Nigeria inda
Alzakzaki ke jagorancin ta.


Zamu cigaba insha Allahu.


HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya
(ABU SINAN)“`
+2348064734911

No comments: