Wednesday, 6 December 2017

SHI'AH DA AKEEDOJINTA 003

*GORON SALLAH*

*SHI'AH DA AKEEDOJINTA*

*_WALLAFAR:_* *Malam Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*

_Fitowa Na uku(003)_

```√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA MUSULMI DA DAULAR MUSULUNCI.

      Yana daga cikin akidar Shi’a shine tsananin adawa ga musulunci da daulolin musulunci tun daga zamanin halifofi har zuwa wannan zamanin. Ga kadan daga cikin misalan da suka faru: -
Abu Lu’uluatal Majusi (Mai bautar wuta) shi ya kashe Umar dan Khattab
Wanda ya kashe Usman bin Affan daya ne daga cikin mabiyan Abdullahi bin Saba Alyahudi
Ashe ba Ibn Alkami da Dusii bane suka shigo da tattara a bagdad, suka kashe miliyoyin musulmai ba?
Ashe basu bane a (2003) suka shigo da mayakan America a Bagdad suka kashe dubban mutane ba?
Ashe ba ‘Yan Shi’a bane a (1885) suka hada kai da Yahudawa suka kashe daruruwan Falasdinawa?
Bugu da kari, ‘Yan Shi’a ne suka kai hari a Makka suka kashe Alhazai, suka sace Hajarul Aswad ya cigaba da zama a hannun su tsawon shekara (20). ‘Yan Shi’a Fadimiyya ne suka kafa daula sukayi mulkin Misra da Yammacin Africa suka kashe malaman Fiqihu wadanda suka hana zagin Abubakar da Umar
Wadannan sune kadan daga cikin misalai dake nuna irin yanda Shi’a ke kiyayya ga daulolin musulunci da musulmai.

√ AKIDAR SHI’A DANGANE DA QUR’ANI.

       ‘Yan Shi’a sun qudurce cewa lallai Qur’ani karkatacce ne, suka ce Abubakar da Umar ne suka juyar da shi, suka shafe wasu surori da wasu ayoyi da ke nuna Aliyu shine Halifa bayan rasuwar manzon Allah. Suka ce Abubakar da Umar sun shafe Suratul Wilaya, ma’ana surar da ta nuna Aliyu ne Halifa bayan Manzon Allah, ga yan da surar take a wajen ‘Yan Shi’a
‘Yaku wadanda sukayi imani da Annabi da waliyyi (Aliyu) wadannan da muka aiko domin su shiryar da ku zuwa ga hanya madai-daiciya’
‘Yan Shi’a sun ce Abubakar da Umar sun juyar da Suratul Sharhi daga asalin ta wai asalinta shine:
‘Ashe bamu muka bude kirjin ka ba? Muka sanya Aliyu ya zama surukinka?
A shekara ta (1877) wani babban malamin Shi’a wanda ke zaune a garin Najib mai suna Alhaji Maimizan Hassan ibn Muhammad Takiyuddaini Addabaristi ya wallafa littafi mai suna:
“Rarrabe zance domin bayani akan juyar da littafin Ubangijin Halittu”. A cikin littafin yayi bayanin yanda Abubakar da Umar suka juyar da Qur’ani!
To mi ya rage ga musulmi? Idan har alqur’ani ya kasance anjuyar dashi a wajen wadan can bataccin? (Yan Shi’a) Ibn Hazm yayi jayayya da Kiristoci akan juyar da Bible sai suke ce shima Qur’ani ai anjuyar da shi kamar yadda Shi’a tace. Sai Ibn Hazm ya maida masu da raddi cewa lallai Shi’a ba musulunci bane a wurin mu ballantana har a kafa hujja da maganar su.

ZAMU CIGABA INSHA ALLAHU.

ALLAH YA SHIRYAR DAMU HANYA MADAIDAICIYA.

HAKKIN MALLAKA©
Hashim Sirajo Uba Tsamiya (ABU SINAN)
08064734911```

No comments: