ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. MU KOYI IBADA A SAUKAKE
Wednesday, 26 October 2022
02 NASIHAR BARKA DA SAFIYA
01NASIHAR BARKA DA SAFIYA
Tuesday, 13 September 2022
LADUBBAN TAMBAYA
Thursday, 29 July 2021
002 FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ﷺ
01 FARIN JEKADA ANNABI MUHAMMAD ﷺ
Tuesday, 30 March 2021
05 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA
04 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA
03 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA
Thursday, 25 March 2021
02 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI
001 HUKUNCE HUKUNCEN TA'AZIYYA A MUSULUNCI
Wednesday, 13 January 2021
MUSAN MALAMANMU NA SUNNAH - ALOSAIMI
Monday, 20 July 2020
WASU DAGA CIKIN AYYUKAN DA AKE SON MUSULMI YA AIKATA A GOMAN FARKO NA ZUL-HIJJAH
Tuesday, 14 July 2020
MAKABARTA GIDAN KOWA DA KOWA
Thursday, 20 February 2020
006 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe(ABU HURAIRAH)*
_006_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA*
Akwai abubuwa da yawa da suke taimakawa mutum wajan sadar da zumunta.
Ga kadan daga cikinsu kamar haka:
1. Yin tunanin manya-manyan darajoji da suka tabbata ga mai sadar da zumunta: Lallai sanin kyakykyawan sakamakon aiki da kuma hango kyakykyawan karshe dake samun mai sadar da zumunta yana taimaka maka wajen sadar da zumunta.
2. Nazari akan mummunan karshe ga mai yanke zumunta:
kula da abin da yanke zumunci yake janyowa na bakin ciki da damuwa da hasara, da nadama da sauransu, yana taimakawa mutun ya nisanci yanke zumunta ya kuma sadar da ita.
3. Neman taimakon Allah:
Wannan yana tabbata ne ta hanyar rokon Allah ya datar da kai ya kuma taimake ka bisa sadar da zumunta ga yan uwanka.
4. Maida mummuna da kyakykyawa:
Yana daga cikin abin da yake wanzar da soyayya da kuma kiyaye zumuncin dake tsakin yan'uwa shine musanya mummuna da kyakykyawa. Karbar uzurinsu idan sun yi kuskure da kuma basu uzuri. Yana daga mafi kyawon abin da zan fada acikin wannan shine abin da ya gudana tsakanin Annabi Yusuf da yan'uwan sa, hakika sun aikata abin da suka aikata amma yayin da suka bada uzuri ya karbi uzurinsu ya musu rangwame mai kyau, bama wannan kadai ba, har addu’a yayi musu kuma ya roki Allah ya gafarta musu.
5. Yi musu rangwame da kauda kai daga aibobansu koda basu baka uzuri ba:
Wannan yana daga cikin abin da yake nuna karamcin mutum da kuma girman himmarsa, mai hankali tatacce yana yin rangwame da kau da kai daga ambaton aiboban yan'uwansa, baya ambaton laifukan su ko da kuwa basu bada uziri ba.
6. Kan-kan dakai da saukin ma’amala:
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suke sanya soyayyar yan uwa ga dan uwansu kuma su kusance shi.
7. Nisantar husuma da yawan jayayya da jidali ko fada da yan uwa.
8. Barin yi masu gori da neman sai sun ran kamaka:
ya zama dole mutun ya bar yima yan'uwansa gori idan ya basu wani abu ko ya ziyarcesu, ko ya basu wata kyauta da dai sauransu.
10. Juriya da daukar duk wani aibantawa daga yan'uwa:
Lallai wannan yana daga cikin abubuwa mafi kyau, shine mutun ya kauda kai yayi hakuri da duk wata suka ko tsegumi da yan’uwansa suke mashi, saboda shedan na shige da fice don ganin ya haifar da matsala a tsakanin yan'wa.
11. Gaugawar aikawa da kyauta idan aka samu sabani a tsakanin yan’uwa:
Kyauta tana janyo Soyayya da kaunar juna, sannan kuma tana hana mummunan zato. Saboda Annabi (SAW) yace; ''KUYI KYAUTA KU SO JUNA''
12. Kwadayin kawo gyara da sulhu a tsakanin yan'uwa idan an samu sabani:
Yana daga cikin abin da ya kamata ga duk masu hankali da natsuwa shine su yi sauri su kawo gyara da sulhu idan wata matsala ta taso a tsakanin yan'uwa, domin idan ba’ayi haka ba sharrin yana iya game kowa.
13. Gaggauta rabon gado:
Ya kamata idan aka samu rasa rai a gida na uba ko na uwa a gaggauta raba gado domin kowa ya amshi rabonshi, wannan yana kawar da rigima da yawan neman sai anraba kuma wannan yana kara dankon zumunci a tsakain yan’uwa.
14. Shirya taro na wata-wata ko shekara-shekara:
Lallai ire-iren wadannan tarukka suna dauke da alherai masu yawa domin a nan ne za’a san juna a sadar da zumunta ga juna, a yima juna wassiya da dai sauransu.
15. Kaddamar da gidauniya ko kafa asusu:
Yana daga cikin abin da ke karfafa zumunta, shine samar da gidauniya ko wani asusu da za'a rika tara kudi duk wata ko shekara domin tallafawa yan'uwa. Da wannan gudunmawa da aka bada za'a iya tallafawa yan'uwa idan wasu matsaloli sun tunkaresu.
16. Kwamitin masu bada shawara:
Yana da kyau a samar da kwamito ta wadanda zasu rika bada shawara a karkashin kwamitin zumunta, kamar kwamitin ilimi, Kwamitin sulhu, da sauransu. Ta haka ne kowa zai san hakkinsa da kuma hakkin yan'uwansa a kansa.
17. Kula da halayensu da ba kowa matsayinsa:
Akwai daga cikin yan'uwa wanda yake yarda da kadan daga sadarwar da akayi masa, koda a shekara za’a ziyarceshi sau daya, koda ta wayar salula ne, wani ma ko da sakin fuskane da kuma Magana. Akwai wanda bai yarda da komai sai ziyara ako da yaushe. Duka wadannan a kula dasu saboda zumunta ta tabbata.
18. Sadar da zumunta don Allah:
Zumunta Ibada ce mai girma don haka ana sadar da ita ne don Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, kamar yadda Allah (SWT) yake fada: ''KUJI TSORON ALLAH DA KUKE ROQON JUNA DASHI, KUMA KU KIYAYE ZUMUNTA. [Nisa'i aya ta 1]
Hakikanin mai sadar da zumunta don Allah shine mai sadar da zumuntar sa ga yan uwanshi ko sun sadar mashi ko basu sadar mashi ba, kamar yadda Bukhari ya ruwaito cikin sahihin littafinsa, manzon Allah (SAW) yana cewa: ''BAI ZAMA MAI SADAR DA ZUMUNTA BA, WANDA SAI AN SADAR MASHI SANNAN YA SADAR, HAKIKANIN MAI SADAR DA ZUMUNTA SHINE WANDA IDAN AN YANKE MASHI SAI YAYI KOKARIN SADARWA''. [Bukhari 5991]
A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INSHA ALLAHU
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
Sunday, 9 February 2020
SUJADAR SAHU A SALLAH
*LIMAN NE YAKE SALLAH DA MUTANE, SALLAH MAI RAKA'A HUDU, BAYAN YA DAGO DAGA SUJADA TA BIYU A RAKA'A TA UKU SAI YA ZAUNA YANA ZATON A RAKA'A TA HUDU YAKE, SAI MAMU SUKAYI MASHI TASBIHI DA SAURI, SAI YA TASHI ZUWA RAKA'A TA HUDU DA SAURI, BAYAN WANCAN ZAMAN DA YAYI DAN KADAN(KAMAR ZAMAN JALSATIL ISTIRAHAH) ZAIYI SUJUDUS SAHAWY NE KO KUWA?*
*_AMSA_*
Idan liman ya zauna a Raka'a ta uku da mantuwa, zaiyi sujada biyu(kafin sallama). Saboda fadar Manzon Allah S.A.W cewa:
لكل سهو سجدتان
Ko wace mantuwa tana da sujada biyu, *Imamu Ahmad da Abu Daud suka fitar da hadisin*
Ibn Qudama Al-maqadisy(RH) a cikin *AL-MUGNY* yace: _Idan Liman ya zauna ba a wurin da ake tahiya ba kwatankwacin *JALSATIL ISTIRAHAH,* zaiyi sujada (kafin Sallama), duka dayane, koda zamu fadi cewa jalsatil istirahah Sunnah ce a cikin Sallah,(ko bamu ce ba) domin shi Mai sallar baiyi nufin cewa jalsatil istirahah yayi ba, yayi nufin waninta(zaton cewa Yana tahiya ta karshe ne) kenan ta zama mantuwa, koda bai yi sujada biyu kafin Sallama ba, sallar shi tayi, domin wani aiki ne yayi Dan kadan a cikin Sallah, shi Kuma aiki Dan kadan bai bata Sallah...._
Haka idan kuka duba a cikin:
كشاف القناع (1/395)
Ya kawo kwatankwacin wannan maganar, ya Kara da hadisin Abdullahi Dan Masa'ud dake cikin Muslim cewa:
فإذا زاد الرجل أو نقص في صلاته فليسجد سجدتين
Idan mutum yayi Qari ko ragi a cikin Sallah zaiyi sujada guda biyu.
Ash-Sheikh Muhammad bin Salih Almunajjid(Hafizahullah) yake cewa:
لكن إذا لم يسجد الإمام للسهو، ظنا منه أنه لا يلزمه السجود، أو نسيانا منه للسجود، فصلاته صحيحة.
Sai dai, idan Liman baiyi sujadar sahawun ba, ko yayi tunanin cewa ba dole bane sai yayi sujadar, ko Kuma ya manta, sallar shi ingantatta ce.
Wannan shine abin da yake na dai dai.
Allah yayi Mana muwafaqa a cikin Kyawawan ayyukan mu
#ABBAN_SINAN
+2348064734911
+2349030201868
Thursday, 30 January 2020
004 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_004_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.*
Idan kayi nazari akan sabubban dake janyo yanke zumunta zaka samu cewa akwai sabubba masu yawa. Ga kadan daga cikinsu
1. *JAHILCI:* Jahiltar mummunan sakamakon da mai yanke zumunta yake samu anan duniya da lahira, ko kuma rashin yin aiki da abin da mutum ya sani. An karbo daga Umar (R) ya kasance akan mimbari yana cewa: ku nemi sanin dangantakarku, sannan ku sadar da zumuntarku wallahi! Lallai zai kasance tsakanin mutum da dan uwansa wata rigima ta hadasu saboda rashin sanin juna, da yasan akwai zumunta tsakaninsu da wannan dalilin na alakar zumunta ya hanashi cin mutuncinsa *(Bukhari, Adabul mufrad 73)*
2. *KARANCIN TSORON ALLAH;*
Idan tsoron Allah yayi rauni sannan addini yayi saku-saku ba zai damu ba idan ya yanke abin da Allah yayi umarnin asadar, kuma baya kwadayin ladar da ake samu idan an sadar da zumunta kuma baya tsoran mummunan sakamakon da zai same shi a dalilin yanke zumunta.
An karbo daga sa’id bn sam’an, yace: Naji Abu Hurairah yana neman tsarin Allah daga shugabancin yara da wawaye (jahilai) sai aka ce masa mine ne alamar yin haka? sai yace dan za’a dinga yanke zumunta a kuma dinga yin da’a ga mai halakarwa a saba ma mai shiryarwa *(Adabul-mufad 66)*
3. *GIRMAN KAI;*
Sashen mutane idan mutum ya samu wani matsayi babba ko ya samu wata daukaka ko kuma ya zama babban dan kasuwa sai yayi girman kai ga yan'uwanshi, ya kyamaci ziyartarsu, kuma ya kyamaci zuwa garesu, yana ganin shi ke kan gaskiya kuma shi ya can-canta a ziyarta.
4. *YANKEWA MAI TSAWO;*
A nan akwai wanda yake yanke ma yan'uwansa lokaci mai tsawo al’amarin ya dore akan haka har ya kai ga yanke zumuntarshi dasu gaba daya, har ya saba da yankewa sai yayi nesa dasu. An karbo daga Mikdam, lallai yaji manzon Allah (SAW) yana cewa lallai Allah yana maku wasiyya da iyayenku mata sannan yana maku wasiyya da iyayenku maza, sannan yana maku wasiyya da yan'uwanku *(Adabul mufrad 60)*
5. *AIBANTAWA MAI TSANANI;*
Sashen wasu mutane idan dan'uwansu ya ziyarcesu bayan a baya ya yanke zumuntarshi dasu lokaci mai tsawo sai su yawaita zar ginshi har zargin yayi tsanani wanda wannan sai yasa shi kaurace masu saboda tsoron mummunan zargi da suke mashi.
6. *DORA MA RAI NAUYIN DAYA WUCE QA’IDA;*
A nan akwai wanda idan dan'uwansu ya ziyarcesu sai su dora ma kansu yin hidindimu da suka wuce karfinsu domin su ga cewa sun karrama dan'uwan nasu sama da karfinsu ko karancin abun hannunsu, wannan shi ke sanya yan'uwan nasu su dinga takaitawa da ziyartarsu domin tsoron kada su dora masu ire-iren wadannan nauye-nauyen. Saboda Annabi yace mafi karancin sadar da zumunci shine sallama mafi girman zumunta shine sadarma wanda ya yanke maka.
7. *KARANCIN KULA DA WADANDA SUKA KAWO MAKA ZIYARA;*
Akwai daga cikin mutane wanda idan yan'uwanshi suka ziyarceshi baya bayyanar da farin cikinsa akan ziyarar, bai tsayawa ya tattauna dasu ko ya sakar masu fuska, sai dai za ka ga yana bata rai yana kyamarsu, wannan yana zama sanadin yan'uwa ba zasu kara ziyartarshi ba dan tsoron irin wannan wulakancin.
Manzon Allah yace, kada ku wulakanta wani abu na alkhairi ko da sakin fuskane idan ka hadu da dan'uwanka.
8. *TSANANIN ROWA;*
Wasu daga cikin mutane idan Allah ya azurtasu da dukiya mai yawa ko wani matsayi zaka same su suna gudun yan'uwansu, ba wai dan girman kai ba a'ah! Domin jin tsoron kada yan'uwan suyi amfani da wannan damar domin bayyanar da bukatunsu zuwa garesu, ko kuma domin kada ya temakesu. Maimakon ya basu dama idan sun ziyarceshi yakarbi bakuncinsu, ya yalwata masu, yayi masu hidima gwargwadon halinsa,ko kuma ya basu uzuri akan abin da ba ya da ikon yi masu amma sai kaga yana kauda kansa, yana kaurace masu domin kada su rokeshi kamar yadda yake riyawa. Mine ne amfanin dukiya ko matsayi da mutum zai samu idan har zai haramta ma yan'uwansa amfana da ita.
9. *JINKIRIN RABON GADO;*
Hakika zaka samu wasu daga cikin mutane suna jinkirta rabon gado kodai domin kasala, ko kuma wani daga cikin magadan yana da wani mummunan kuduri game da yan'uwansa ko makamacin haka.
Duk lokacin da aka jinkirta rabon gado to kiyayya da adawa zata watsu tsakaninsu domin idan wannan yana da hali ko yafi karfin gadon wani shi kuma yana bukatar raba gadon domin bashi na shi kason ya samu ya bude kasuwanci ko makamanci haka.
10. *MUTUWAR AUREN ZUMUNCI;*
Hakika mutuwar auren zumunci yana haifar da matsaloli a tsakanin yan'uwa na bangaren miji dana bangaren mata musamman in akwai 'ya'ya a tsakaninsu ko kuma saboda wasu matsaloli da suka shafi sakin auren.
A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI CIGABAN *SABUBBAN DAKE JANYO YANKE ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
003 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_003_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *HADARIN DA KE CIKIN YANKE ZUMUNTA*
Hakika Allah (SWT) da manzonsa (SAW) sun tsoratar dangane da hadarin yanke zumunci, suka sanya matsayin yanke zumunci dai dai da Fasadi/barna a bayan kasa.
Allah (SWT) yace to shin kuna fatan idan kun juya daga (umarnin) zakuyi barna a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntarku? Wadannan sune wadanda Allah ya la'anesu, kuma ya kurmantar dasu, kuma ya makantar da ganinsu. *(Suratu Muhammad 22-23)*
An karbo hadisi daga Aisha (R) manzon Allah (SAW) yace zumunta tana rataye da al’arshin Allah. Tana cewa wanda ya sadar dani Allah ya sadar dashi, wanda ya yanke ni Allah ya yankeshi *(Muslim 2555)*
An karbo daga MUD’IM (R) manzon Allah (SWA) yace mai yanke zumunta baya shiga Aljanna *(Muslim 2556)*
Haka nan kuma, an karbo daga Abubakrata, Manzon Allah yace, Babu wani laifi daya can-canta Allah ya gaggauta ma ma'abocin sa uquba tun anan duniya tare da cewa yayi mashi tanadin uqubar a lahira kamar wanda ya yanke zumunta da kuma azzalimi *(Bukhari adabul mufrad 67)*
An karbo daga Abu Huraira; lallai wani mutum yace ya manzon Allah lallai ni ina da yan'uwa kuma ina sadar da zumuntarsu amman suna yanke mani, ina kyautata masu amma suna munana mani, ina yin hakuri dasu amma suna jahiltata? Sai Annabi yace, idan har ka kasance kamar yadda ka fada to lallai kamar kana zuba masu toka ce mai zafi, Allah ba zai gushe ba yana taimakonka akansu matukar ka dauwwama akan haka *(Muslim 2558)* Ma’ana: kamar kana ciyar dasu toka mai zafi saboda abin da suke haduwa dashi na laifi.
Haka nan kuma an karbo daga Abdullahi ibn Amru binul As, Manzon Allah (SAW) yace, bai zama mai sadar da zumunta ba wanda yake so aranka mashi, sai dai mai sadar da zumunta shine wanda idan an yanke mashi, shi yana sadarwa *(Bukhari 541)*
An karbo daga salmanu ibn Amir, Manzon Allah yace, yin sadaka ga miskinai sadakace kamar sauran sadakoki, amma yin sadaka ga dan'uwa tana da darajoji biyu (2) ladar sadaka da kuma ladar sadar da zumunci *(Abu Dawud 2555 da Tirmidhi 658)*
An karbo daga Abu Hurairah yace, lokacin da wannan ayar ta sauka,,, kayi gargadi ga yan'uwanka makusanta, Annabi (SAW) ya kira Quraishawa, suka hadu gaba dayansu, yayi musu wa’azi gaba dayansu kuma yayi ma dai-dai kunsu yace ya Fatima ki tsamar da kanki daga wuta, lallai ni bani wadatar daku a wurin Allah da komai sai dai lallai kuna da wata zumunta da sannu zan sadar da ita *(Muslim)*
ANAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI *SABUBBAN DAKE JANYO YANKE ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868
DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
KARATUTTUKAN MASALLACIN ABU HURAIRAH TSAFE
*MASJID ABU HURAIRAH TSAFE*
Wannan Masallaci karkashin kwamitin social media na masallacin sunyi kokarin tattara karatuttukan da *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)* yake gabatarwa a wannan Masallaci har kusan littafai *36* gasu kamar haka:
1. *Aqeedatud dahawiyya*
2. *Ahkamul idaini*
3. *Alfurqan baina auliya'allahi wa'auliya'ish-shaidan*
4. *Ahkamul uduhiyya*
5. *Al'imamu wa'af'alihi*
6. *Al'ilmam, bi'ahkami wadabus siyam*
7. *Aljawabul khafi*
8. *Alwajibatul mutahattimatul ma'arifah.*
9. *Bugyatul mushtak*
10. *Bulugul maram*
11. *Daura- akan Magunguna da ruqya*
12. *Daura- akan Maulidi*
13. *Hisnul Muslim*
14. *Hiqbatun minat-tarikh*
15. *Hudubobi guda 166*
16. *Imani haske*
17. *La'ilaha ilallah*
18. *Manasikul hajji*
19. *Mayatamayyazu bihil muslimu anil mushrik*
20. *Mu'amalatul hukkam*
21. *Muhadarori*
22. *Nabiyur Rahma*
23. *Qa'idatul jalila*
24. *Ru'usul aqlam*
25. *Riyadus saliheen*
26. *Ramadhan Tafseer, 2007,10,13,16,17,18, da 2019*
27. *Salatut Tarawih*
28. *Sahihul bukhari*
29. *Shama'ilul Muhammadiyya*
30. *Sifatu saumun Nabiyy, kala biyu*
31. *Tarbiyatul aulad, kala 3*
32. *Tafseer weekly na ibn Katheer*
33. *Tuhfatul iraqiyya*
34. *Usulul iman*
35. *Usulus salasa*
36. *Wasiyyatul kubrah*
37. *Aqeedatul wasidiyya na (ibn taimiyya).*
38. *Adabuzzifaf na (Albany)*
39. *Fadlul Islam na (Muhammad bn abdulwahab)*
40. *Nawaqidul Islam na(Muhammad bn Abdulwahab)*
41. *kitabuttauhid na (Muhammad bn abdulwahab)*
42. *kitabuttauhid na (sheikh salhul fauzan)*
43. *Albida'ah*
44. *Sharhin sunnah na (Barbahary)*
45. *Kama takunu yuwalla alaikum na (dr. Ramadani)*
46. *Jilbabul m ar'atil Muslima na (Albany)*
47. *Huququn da'at ilaiha fidra waqarrarat'ha shari'a na(sheikh uthaimin)*
48. *Siyamu Ramadan*
49. *Qiyamu Raman.*
50. *Ahkamul jana'iz na (Albany)*
51. *Tafsirul kalimatul shahada.*
52. *Sifatus salatin nabiyy na (Albany)*
53. *Sharhi masa'ilil jahiliyya na (Muhammad bn Abdul wahab)*
54. *Auradu ahlussunah.*
55. *Tabyini kazibul muftary bima nusiba ila ibn taimiyya na (M Kabir Maru).*
zamu cigaba da kawo wadan da muka tuna daga baya insha Allahu
Wannan kwamiti na Nan na kokari kafin zuwa Ramadan za'a gabatar maku da 16GB memory card Mai dauke da Wadannan karatuttukan da ma wasu wadanda bamu shigar ba a Nan.
Allah ya sakawa Malam da Alkhairi
#MABUHURAIRAHTSAFE_SOCIAL_MEDIA
005 ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
*ZUMUNTA A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wallafar: *Ash-Sheikh Muhammad Sani Liman Tsafe (ABU HURAIRAH)*
_005_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
✅ *CIGABA DA BAYANI AKAN SABUBBAN DA KE JANYO YANKE ZUMUNTA.*
11. *NISAN WURIN ZAMA DA KUMA KASALAR ZUWA ZIYARA*
Akwai daga cikin mutane wadanda idan gidan su ko garin su yana nesa sai a dinga jin kasalar zuwa ziyartarsu, wanda wannan sai ya nisantasu da yan'uwansu.
Nisan wuri bai kamata ba ya zama dalili na yanke zumunta, musamman wannan zamanin da ake da hanyoyin sadarwa daban daban, Allah ya bamu ikon kulawa da zumunta.
12. *MAKWABTAKA A TSAKANIN YAN UWA*
Da yawa Makwabtaka tana gadar da yankewar zumunta a tsakanin yan'uwa. Umar Dan khaddab yace ku umurci yan'uwanku su dinga ziyartar yan'uwansu amma kada suyi makwabtaka da juna a gidajensu, sannan sau dayawa kusanci a tsakanin gidajen yan'uwa yana haifar da sashen wasu matsaloli wadanda suke haifar da fada a tsakanin 'ya'yansu wanda wannan yakan zarce har zuwa ga iyayensu sai wannan ya haifar da gaba da yanke zumunci a tsakaninsu.
13. *KARANCIN KAUDA KAI DA HAKURI A KANSU:*
Sashen wasu mutane suna da karancin kauda kai da kuma hakuri akan abin da yan'uwansu suka yi masu. Wasu yan'uwan da an samu sabani tsakaninsu ko wani kuskure da ya afku sai su yanke zumunta, su kaurace ma yan'uwansu.
14. *HASSADA:*
Akwai daga cikin yan’uwa wanda Allah yake azirtawa da ilimi ko wani babban matsayi ko dukiya mai yawa sai ka same shi yana yima yan'uwansa hidima yana kyautata ma su, sannan ka samu sashen yan'uwansa suna nuna masa hassada da kiyayya da haifar da rikici tsakanin shi da su, suna cewa duk abin da yake yi masu ba domin Allah yake yi ba.
15. *YAWAN WASA:*
Lallai yawan wasa (da sunan wai abokin wasa) yana haifar da mummunan abu a tsakanin yan'uwa domin wani yana iya fadar kalma mai muni ga dan'uwansa ba tare da ya kula da hadarinta ba agare shi, wannan sai ya gadar da kiyayya da gaba a tsakaninsu a sanadiyyar wannan Kalmar.
16. *ANNAMIMANCI DA KARBAR GULMA:*
Akwai da yawa daga cikin yan'uwa wadanda dabi'arsu shine yawo da annamimanci a tsakanin yan'uwa domin su kawo rabuwar kai da gurbata tsakanin yan’uwa wanda wannan yana gadar da yanke zumunta, sai dai abu mafi muni shine karbar gulma da yadda da ita shi ke haifar da yankewar zumunta.
17. *SHAGALTUWA DA DUNIYA:* Shagaltuwa da duniya da son yawan tara abin duniya yana hana mutun sadar da zumunta, da kuma samun lokacin ziyartar yan'uwansa da nuna soyayyar shi zuwa gare su.
18. *MIYAGUN HALAYE NA MATAR SHI:*
Wasu daga cikin mutane ana jarabtarsu da muguwar mata mai mummunan dabi’a mai yawan sukar yan'uwansa, bata son yayi mu’amala da yan'uwansa ko wasu, tana dogewa wajan ganin ta raba shi da yan'uwansa tana hana shi ziyartarsu, da sadar da zumunta zuwa garesu, idan yan uwan sa suka ziyarceshi sai tayi ta fushi tana murtike fuska. Bugu da kari akwai mazajen da suke mika ragamar zumuncinsu ga matarsu sai wanda ta yarda dashi yake sadarmawa, wanda bata yarda da shi ba sai ya yanke ma sa.
19. *MANTAWA DA WASU YAN'UWA A LOKACIN WALIMA KO WATA HIDIMA:* Hakika wani daga cikin yan'uwa yakan shirya walima ko wata hidima ya gayyaci yan'uwansa sai ya manta da wani ko wasu, sai su da ba’a gayyata ba su munana masa zato, su nuna kamar an wulakantasu an zabi wasu wadanda suka fisu, wannan nasa ya kaurace masu da yanke zumunta a tsakaninsu.
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan dake janyo kauracewa juna da kuma yanke zumunta. Ya kamata a basu kulawa ta musamman da hattara da fadawa cikinsu.
A NAN ZAMU DAKATA SAI A LOKACI NA GABA INDA ZAKUJI *ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA WAJAN SADAR DA ZUMUNTA*
DOMIN CIGABA DA SAMUN WANNAN RUBUTU KUNA IYA AIKEWA DA SAQON WHATSAPP ZUWA GA: +2349030201868 DOMIN SHIGA GROUP DIN *MU KYAUTATA NIYYA*
#ABBAN_SINAN
https://fb.me/abbansinan
LADUBBAN NEMAN ILIMI DA BADA ILIMI
*KWAMITIN HARKOKIN ADDINI DA ZAMANTAKEWA NA MASALLACIN ABU HURAIRAH TSAFE*
*LADUBBAN NEMAN ILIMI DA BADA ILIMI*
✅ *IKHLASI:*
yi don Allah, mai neman ilimi da malamin dake bada ilimi ya zama dukan su sunayi don Allah, domin neman yaddar Allah. Rasulullahi (S.A.W) yace "Duk wanda ya nemi ilimi don neman yaddar Allah, daga baya ya canza niyarsa don neman duniya, ba zaiji kanshin Al-Janna ba" *(Abu Dawuud: 3664)*
✅ *NIYYAR DAUKE JAHILCI:*
Duk wanda zai nemi ilimi ko zai bada ilimi ya zamanto don ya dauke ma kansa jahilci da waninisa. Imam Ahmad Bin Hambali Yace "Shi ilimi babu abun dake dai-dai dashi ga daraja musamman ga wanda ya kyautata niyar sa". Dalibansa sukace kamar yaya? Yace "Wanda yayi da manufa (Niyar) ya dauke makansa jahilci ko waninsa"
✅ *NEMAN ILIMI DA MANUFAR KARE ADDINI:*
Ya kamata ga mai bada ilimi ko dalibi ya kasance da manufar ba addini kariya ya keyi, Rasulullahi (S.A.W) yace: "Yaku wanda sukayi imani ku kasance masu taimakon addinin Allah, *Q: Suratul Saffi;14".*
✅ *AIKI DA ILIMI:* Na daga cikin ladubban ilimi ga malami da dalibi aiki da ilimi Rasulullahi (S.A.W) yace Alqur'ani hujjane gareka ko akan ka” *(Muslim: 223)* hujjane gare ka in kayi aiki dashi kashiga Aljanna. Akan ka in bakayi aiki dashi ba ka shiga wuta.
✅ *HAKURI:*
Dole ne malami da mai neman ilimi suyi hakuri: malami yayi hakuri wajen bada ilimi, dalibi yayi hakuri wajen neman ilimi. Hakuri kan neman ilimi ya kasu gida ukku (3):
1. Hakuri da talauci da yinwa
2. Hakuri akan dagewa har sai ka samu
3. Rashin yanke kauna ga abin da kake nema
Imam Ahmad bin Hambali yace Na shekara tara (9) ina karatun *Kitabul Haid* har saida na gane shi
✅ *TAWALIU DA NISANTAR GIRMAN KAI:*
Ana son malami da dalibi su sanya tawali'u da nisantar girman kai ga abin da suke nema. Imam Mujahid yace Mai girman kai ko mai kunya baya samun ilimi.
✅ *TAFIYA DON NEMAN ILIMI:*
Wajibi ne ga malami ko dalibin ilimi da suyi tafiya don neman ilimi musamman ilimin da babu a inda suke. Rasulullahi (S.A.W) yace Neman ilimi wajibine ga dukkan musulmi” *(Muslim)*
✅ *RASHIN KARBAR ILIMI GA DAN BIDI'AH:*
Bai halitta ga dalibi ya nemi ilimi ga dan bidi'ah, yan bidi'ah sune wadanda suke saba ma gaskiya kuma suka kirkira abubuwan da musulunci bai zo dasu ba, kamar: Yan shi'ah, Khawarij, da sauran darikun Sufaye.
Muhd Bin Sirin yace: Kada ku kuskura ku zauna da yan bidi'ah kada kuyi karatu garesu kar ku sauraresu domin Ahlis-sunnah sunyi ittifaki a kaurace masu da kuma nesa dasu”.
Allah ya bamu ilimi Mai amfani Kuma Mai albarka 🤲🤲🤲
*MASJID ABU HURAIRAH TSAFE SOCIAL MEDIA COMMITTEE*
+2348064734911
https://fb.me/masjidabuhurairahtsafe