Friday, 8 December 2017

HUDUBA MAI TAKEN HARAMCIN CAMFI

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A DAGA MASJID
ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE


A wannan makon limamin Massallacin Jumu'a na
Abi Hurairah dake unguwar Area2, Tsafe Sheik
Sani Na Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #CHAMFI
Godiya ta tabbata ga ALLAH Wanda ya halicci
duniya da abunda ke cikinta, Godiya ta tabbata
ga ubangiji daya ubangijin rana da wata, Godiya
ga wanda kagemu ya bamu ikon gudanar rayuwa.
Tsira da amincin ALLAH Su tabbata ga mafi
soyuwa wajen ubangiji, Annabi Muhammad s.a.w
da iyalansa da sahabban da duk wadanda suka
biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako muna rokon ya shiryar damu hanya
madaidai ciya ameen.
Yan uwa musulmi masu albarka a yau Khudbar
tamu zatayi magana ne game da #CHAMFI!!!
#CHAMFI wato ana nufin danganta faruwa ko
afkuwar wani abu na rayuwa ko mako bayan ta,
Ga lokachi ko zamani ko kwana ko wata ko
shekara ko dan Adam, Ko aure ko mutuwa da
sauransu!!
Bayan Manzo s.a.w yafa mana cewa "Duk wanda
ke #CHAMFI to ya tabbatar yayi shirka"
Shirkar kuwa zata iya kasancewa rakama ko
kuma babbah!!
Jingina faruwar wani abu ga aure ko shugaba
duk wani musulmi mai tauhidi yasan babban
kuskure ne.
Wasu kuma da danganta rashin lafiya da
#CHAMFI da kuma masu danganta duk wani
abunda yasame da #CHAMFI!!
Yan uwa musulmi masu albarka
Babu inda ya halatta ga musulmi yayi #CHAMFI
sai a wuri daya shine kayi #CHAMFI ga kanka
wato duk abunda yasameka a rayuwa ka dauka
cewa daga laifukan da kake aikatawa na rayuwa!
Shi #CHAMFI tsohon abu ne dake da tsohon
tarihi wato ba daga hausawa ne aka fara yin
#CHAMFI ba, Bari muji kadan daga wasu
al'ummah dake aikata #CHAMFI-
Yahudawa sun # CHAMFA Annabi Salihu (a.s)
domin yazo ya isko su cikin bata da shirka,
Yafara yi masu wa'azi ba dare ba rana, Da suka
qi yin imani sai ALLAH Ya jarabce su da musibu!
To sai suka fara yin #CHAMFI cewa Annabi
Salihu (A.S) yakawo masu!
Mushrikai na Makkah suma sun #CHAMFA
Manzo (s.a.w) domin ya isko su cikin kafurci da
bata, Yayi masu wa'azi da suka qi karba sai
ALLAH Ya jarabce su da talauci da rashi!
Suma sai suka #CHAMFA Manzo (s.a.w) cewa
kafin yazo suna cikin arziki, Amma da yazo sun
fara fadawa talauci!
Idan muka diba rayuwar mu ta Najeriya zamu ga
cewa kwatan kwacin rayuwar nan ta same mu, A
baya yan kasa na cikin wadata amma a yanzu
talauci wane hali muke ciki??
To nan yakamata yayi tauhidi yayi amfani,
Garemu.
Yan uwa musulmi masu albarka, Yakamata mu
kara sani talauci da arziki da komai da komai duk
suna hannu ubangiji, Amma sai mu dora laifi kan
shugabanin mu, Shin mu manta cewa akwai yan
Najeriya masu aikata Shirka wanda sune
kolulowar laifi ga ubangiji.
Mun manta fadar ALLAH s.w.t daya fada cewa
"DUK ABUNDA YASAME KU DAGA ALLAH DA
AYYUKAN DA AIKE AIKATAWA"
Hakama madaukakin sarki na cewa "DUK
ABUNDA YASAMU KU MAI KYAU DAGA ALLAH
MARAR KYAU KUMA DAGA ABUNDA KUKE
AIKATAWA NE"
Shi #CHAMFI inkari ne tauhidin rububiya.
Yan uwa musulmi masu albarka, Akwai abunda
jahilai keyi na #CHAMFA Watan safar wato
watan da muke ciki, Ma'ana wata na biyu a
musulunci, Jahilai sun kasance suna kauracewa
aikata ayyuka kamar aure da tafiya da sauransu!!
Sai Manzo s.a.w yace "Babu komai a watan
Safar, Wata ne kamar saura"
Akwai masu alaqanta cuta da #CHAMFI, a yanzu
turawan yamma na farfaganda ta cewa suna
cuta kamar ta sauro da sauransu, Wai sai suce
sun karar da ita, Hakika ita cuta tana samuwane
da iko da iznin ALLAH.
A cikin ayyukan turawa akwai tuka da warwara.
A cikin wannan watan akwai musulmi da suke
cewa wai ALLAH Na saukar da annoba dubu
ashirin da uku (23, 00.000) wai suna cewa ayi
nafila raka'a 4 da fatiha kafa 7 idan kagama za'a
rubuta 'Salamun ala nuhin' a rubuta a sha.
To wannan baida asali a musulunce kuma bidi'ah
ce!
Su duka al'amura da faruwa ne da ikon Allah.
Babban tabi'i imam alhambali yace "Kebance
wani lokachi dan a aiyana cuta garesa kuskure
ne"
Wani fasihin mawaki na cewa 'Muna ta dorawa
zamani laifi mun manta mune ke aikata laifin ba
zamani ba'
Yan uwa musulmi masu albarka, A kowane
lokachi mu zama masu imani domin bamu san
inda ajalin mu yake ba!
A takaice dukan wani abu da ake aikata wato
#CHAMFI shirka ne kuma bata ne!!
ALLAH Yabiya bukatun mu ya gafarta mana yayi
rahama garemu, Yabamu zaman lahiya mai
dorewa.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 13-Safar1439 AH
Saturday 03-November-2017

No comments: