Friday, 8 December 2017

HUDUBA MAI TAKEN TASU'A DA ASHURA

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #AZUMIN_TASU
'A_DA_ASHURA_DA_BIDI_OIN_DA_AK
A_QAGO_ACIKI
Godiya ta tabbata ga ALLAH Madaukakin sarki
muna gode masa muna neman taimakon muna
neman gafarar sa, Muna neman yakare mu daga
miyagun aiyuka!!
Wanda ALLAH Ya shiryar shine shiryayye babu
mai iya batar dashi, Wanda kuma ALLAH Yabatar
babu mai iya shiryar dashi!
Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai
ALLAH, Kuma na shaida annabi Muhammad
bawan sa ne kuma manzon sa.
Bayan haka, Yan uwa musulmi masu albarka
muna cikin sabuwar shekarar musulunci kuma
watan farko na shekarar, Wata mai albarka mai
falala..
Watan muharram wata ne da ALLAH Ya girmama
ya kuma karrama, kamar yadda yake fada cewa
"LALLAI ADADIN WATANIN 12 NE A WURIN KU
KARRAMA SU KADA KU ZALUNCI KAWUNAN KU
A CIKI"
Ashe kuwa duk abunda ALLAH Ya karrama to
wajibin mu muma mu karrama su,
An karbo daga Aisha r.a tace 'Mutanen jahiliya
sun kasance suna girmama watan Muharram har
suna kiransa da suna Muharram watan ALLAH
Kuma sun kasance suna kauracewa aikata sabo
a cikin '
Yana da kyau mu yawaita azumi a cikin watan
Muharram, Har ma an ruwaito daga Manzo s.a.w
cewa 'Mafificin azumin bayan na watan
ramadana shine azumin watan muharram'
Ibn Rajab yayi sharhi watan Muharram wata ne
falala da ake bukatar yawaita ibadu da
kauracewa zunubi,
Yan uwa musulmi bayan mun azumci kwana
goma a watan Zhul hijja (Watan karshe), Yanzu
kuma sai mu azumci kwana biyu a watan
muharram (Watan farko) za'a rubuta mana ladar
mun fara shekara da ibadah kuma mun kammala
ta da ibadah, Daga hakanan sai a sanyamu cikin
bayi na kirki.
Lallai an mustahabanta muna azumtar wannan
rana domin dinbin falalar dake ciki, An ruwaito
daga Manzo s.a.w cewa 'Azumin 10 ga watan
Muharram ina da yaqinin ALLAH Yagafarta
abunda yagabata'.
Jabir r.a ya ruwaito cewa 'Ban taba ganin manzo
s.a.w na kirdadar zuwan wani azumi ba kamar na
goma ga muharram'
Harma kuraishawa kafin zuwan Manzo s.a.w
suna azumtar wannan rana.
Hakama sadda Manzo yayi hijra zuwa Madina ya
tarar yahudawa nayin wannan azumin, Sai ya
tambaye su miyasa kuke azumtar wannan ranar?
Sai suka ce munayi dan murnar nasarar da
ALLAH Yabaiwa annabi Musa A.s akan fir'auna,
Sai Manzo s.a.w yace 'Ai mune muka fi
chanchanta muyi domin Musa dan uwan mu'
Amma tun yana Makkah yana wannan azumi ya
tambaye su dan yaji hujjar da suka dogara da ita.
Azumtar wannan lokachin nada falala da dama
ga wasu daga cikin.
*Manzo s.a.w yayi, Kenan yasamu falala daga
Manzo s.a.w
A yanzu munyi sa'a kasancewa gobe ne tara ga
wata sai mu tashi da tasu'a jibi muyi ashura.
ABUBUWAN DA AKA KIRKIRO A WANNAN
WATAN
Wasu na shafa kwalli, Wasu na lalle wasu na
dinki da dafe dafen abinci!
Wasu kuma baqin ciki a wannan rana, Har suna
koke koke da saran jikin juna da sauransu!
To a maganar gaskiya wannan baida asali daga
kowane magabaci na kwarai, Wasu kuwa na
cewa awadata gida da abinci wai saboda
shekarar zata kasance ma da kyau.
Wadanda sukeyi wannan kirkiren sune suka
kashe sayyidina Aliyu r.a suka kashe Hassan r.a
kuma suka kashe Hussaini R.a.
Su kuwa nawasib sune suke murna saboda sune
suka kashe ahlul baiti.
Yan shi'ah sune suka kashe sayyidina Hussani
r.a a Karbala kuma sun kashe mahaifinsa Aliyu
R.a, Dukkansu sunyi shahada.
Yan shi'ah sun tanadi ranar ashura a matsayin
ranar baqin ciki, Har suna yanka jikin su da
aikata rashin imani ga yara, Wannan yasabawa
musulunci da kuma lafiyayen hankali, Kuma
babbar alama ce dake nuna yadda addinin Shi'ah
yayi hannu riga da musulunci kuma yana nuna
cewa Shi'ah addini ne mai zaman kansa.
Annabi Zakariya A.s, Da Hassan r.a, Da Umar r.a
da Aliyu r.a duk kashe su akayi amma miyara
basu baqin cikin kashe su??
A musulunci babu wata rana da aka tanada dan
baqin ciki, Idan ma za'a sanya to ranar data fi
chanchanta itace ranar da Manzo s.a.w yabar
duniya. Domin Manzo s.a.w yace 'Duk wanda
wata musiba ta sama ko ta rashi to yayi hakuri
domin rashina shine babbar musiba'' !!!!
Shari'ah ta yarda idan akayi maka rassuwa kayi
jimami har da kuka tsawon kwana 3, Amma
abunda yafaru shekaru dubu daya da wani abu
da ya gabata.
Lallai muyi tsayin daka waje yakar shi'ah a
gidajen mu da yayan mu.
A ranar Ashura yan shi'ah nayi babbar bajakoli
da izgili da zagin sahabbai, Alhali Manzo s.a.w
yace "Kada ku zagi sahabbai na domin wallahi
koda dayanku yaciyar da kwatankwacin dutsen
uhudu na zinare bazai kai muddunsu daya ba, Kai
koda rabinsa!"
Wannan na nuna wallahi koda duk mutanen
duniya zamu bi ALLAH Da ibadah har tsawon
shekara bazamu kai nasu da kwana daya ba!! Ko
da rabi ma..
To mutane masu daraja irin haka kuma sune za'a
zaga??
Yan shi'ah na ziyartar makabartu har suna
ziyartar kabarin Hussaini r.a suna cewa' wai duk
wanda ziyarci kabarin sau daya yafi aiki hajji sau
ashirin' Kunj4 wani cin mutunci!!
A ranar ne suke aikata auren mutu'a!!
Lallai babban dalilin yin azumin shine ranar ne
ALLAH Ya halakar da fir'auna.
Yan uwa musulmi masu albarka an samu sabanin
lissafi inda wasu ke cewa yau tara ga wata, A'a
yau ne takwas ga wata kuma a kasar Saudiyya
yau tara ga wata, Sai dai zamuyi amfani da
abunda ke kasar mu!!
Muna rokon ALLAH Yabamu zaman lafiya, Yayi
jagora ga mai martaba Emir na Tsafe, Da kuma
gafarta margayin daya rassu, Ya ALLAH Yayi
salati ga Manzo rahama da iyalansa da
sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da
kyautata, Ka rahama mana ka biya mana bukatun
mu.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Yau Jumu'a 8-Al-Muharram 1439 AH
Friday 29-September-2017

No comments: