Friday, 8 December 2017

HUDUBA MAI TAKEN LAYYA DA HUKUNCE HUKUNCENTA

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA


DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #LAYYA_DA_SALLAR
_IDI_DA_ABUBUWAN_BUKATA_A_WANN
AN_WATAN_DA_KYAWAWAN_HALAYE_A_
WAJEN_BIKIN_SALLAH
Godiya ta tabbata ga ALLAH Madaukakin
sarki,Muna gode masa,Muna neman taimakon
sa,Muna neman ya kare da sharrin kawunan mu
da miyagun ayyukan mu, Tsira da amincin ALLAH
Su kara tabbata ga manzo tsira, Annabin rahama
sallallalahu alaihi wassalam, Da iyalansa da
sahabban sa da dukkan wadanda suka biyo
bayan su da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Yan uwa musulmi yau Khudbar zata magana ke
wannan halin da ibadu dake gaban mu,
Yan uwa musulmi muji tsoron ALLAH Gaskiyar jin
tsoron sa, Kamar yadda umarce, Kuma mu kara
gode masa kamar yadda ya umarce mu, Sannan
abu ne mai kyau mu dage da ambaton ALLAH A
Wannan lokachin kamar ya umarce mu da cewa
"YAKU WADANDA KUKA YI IMANI KU AMBASHI
ALLAH AMBATO MAI WAYA KUYI KUMA TASBIHI
GARESHI"
Yan uwa masu albarka muyi tseararre a wannan
lokachin (Anan ana bukatar tsere) domin suna
cikin kwanakin da Allah ya kebance dan rahama
da tausayi ga bayin sa!
Yawaita ambaton ALLAH A cikin wannan lokachi
abu ne mai matukar muhimmanci, Hasalima an
ruwaito Abi Huraira R.a ya kasance yana shiga
ko ina yana yawaita yin kabbori, Har cikin
kasuwa yana shiga dan tunasar da yan kasuwa
da masu sayyayya, Yana daga murya yana cewa
'Allahu akbar Allahu akbbar, Allahu akbar wallahu
Akbar walil lahil hamdu'
>LAYYA
Daga cikin kwanakin goma akwai wata babbar
ibadah da ake aiwatar a wannan watan, Layya
nada sharudda
-Amfani da kudin halal wajen sayen dabbar
zakuyi amfani da ita,
Ita layya Sunnah ce daga sunnar annabawa,
Annabi Ibrahim A.s da kuma Annabi Muhammad
S.a.w , Inda tayo asali shine lokachin da annabi
Ibrahim yayi mafarkin ya yanka dansa wato
Annabi Isma'il A.s, Alqur"ani yabamu labarin
cewa Ya yanka dan nasa"SAI MUKA FANSHI
YARON DA ABUN YANKA MAI GIRMA (Rago)"
Layya abu ce dake kara kusanta bawa da
ubangijin sa, ALLAH Ya umarci Manzo s.a.w da
zuwa sallar idi, Da layya kamar yadda yake fada
cewa "KAYI SALLOLI KUMA KA YANKE LAYYA
KA DAN ALLAH DA KUMA TSARKAKA WAJEN
ALLAH"
Hadisi yazo daga sahabin manzo s.a.w cewa
"Mun kasance da ranar arfa da Manzo s.a.w
yace lallai yazama tillas ga kowane gida suyi
layya"
Ashe yazama wajibi ga kowane gida suyi layya,
Malamai sunce gida guda suna iya hadawa asayi
dabba dan ayi layya!
Hakama wani hadisi da yayo ya tsoratar da masu
tabi'ar matsolanci cewa "Manzo s.a.w yace 'Duk
wanda keda wadatar yin layya baiyi ba to kada
ma yaje massallachin idi' "
Sau da yawa zakaga magidan ci a ranar jajibiri
ya sawo wancan ya sawo wanchan, Dan adafa
abinci amma ya kasa yin layya, Ita wannan sallar
ba sallah bace ta dafe dafen abinci, Sallah ce
yanka layya!
Sheik Muhammad bn fodio yace: 'Idan bakayi
layya ba, Kuma ka dafa abinci ko wannan abincin
bidi'ah ce '!!
*Layya ta hau wajibi ga kowane musulmi, baligi,
Mai hankali, Mai wadata, Mazaunin gida, Amma
kananan yara sunnah ce, Yin layya koyi ne da
Manzon rahama s.a.w.
Ibn taimiyah yace 'A ibaduh na jiki babu kamar
sallah, A ibada ta kudi kuma babu kamar layya'
Layya ana yin tane daga dabbobin ni'imah wato
sune kamar haka-
~Rakumi rakuma
~Sa ko saniya
~Rago ko Tunkiya
~Bunsuru ko akuya.
Wadannan dasu ne kadai ake yin layya!
Sau da yawa zakaga wasu na sakaci wai da
sunam suna jin kunyar yanka bunsuru ko tinkiya
ko akuya, Dan basu da halin sayen Rago, Wannan
bai dace ba, Hausawa ma suna cewa dai dai kurji
dai dai ruwa!!
Yan uwa musulmi masu albarka, Sai dabbar layya
ta cika wadannan sharuddan sannan take layya,
~Rakumi ko rakuma sai sun kai shekara 5
~Sa ko saniya sai sunkai shekara 2 zuwa ta 3
~Bunsuru ko akuya sai sunkai shekara 1 zuwa
cikin ta 2
~Rago ko tunkiya sai sun kai shekara 1 !!
Duk da akwai basu dake cewa ana iya yanka mai
wata 6, Amma wannan bai inganta ba!
Dole ne dabba ta tsarkaka daga aibi, Wato wasu
kuma sharudda kamar haka,
~Ba'a layya da mai ido daya
~Rashin lafiyar da data baiyana
~Dabba mai gurgunta
~Tsohuwar dabba marar mai marar bargo
~Mai yankakke kunne, Ko bindi ko marar hauru
da sauran illoli baiya nan nu, DUK BA'A LAYYA
DA SU!!!
Ana son dabba wadda idan ka kalle ta zakaji
wadata.
Idan ka sawo dabba sai daya daga cikin matsalar
chan ta same ta, Malamai sunce ba ba komai
abunda dai ba'a so shine kaje saye kaganta da
wannan illar kuma ka sawo.
Hikmar dake cikin layya:
1-Kusanta bawa da ALLAH Domin ciki umarni ne
Na ubangiji kamar yadda madaukakin sarki ke
cewa "ALLAH BAYA BUKATAR NAMA KO JINI
YANA BUKATAR TSARKAKE NIYA"
2-Dan samarwa mabukata, Wato rabawa
wadanda basu yi ba, Saboda rashin hali
3-Kara soyyyaya tsakanin musulmi, Duk wanda
ya dauki nama ka bashi zaiji farin ciki da kara
sonka
4-Alamace ta daga addinin Allah, Domin yin layya
daga addini ne,
5-Koyi ce da jagorori wato annabi Ibrahim A.s da
Annabi Isma'il A.s, Mu diba fa annabi Ibrahim a.s
ce masa akayi yayi layya da dansa,Kuma ya
dauki azamar yi,
6-Yin layya ko ne da alhazai, Su suna yin hadaya,
mu kuma dake gida muna yin layya.
SALLAR IDI
Sai kuma bangare na biyu, Manzo s.a.w ya
wajabta mana sallar idi, akwai hadisi daga
manzo s.a.w da yake cewa "Manzo s.a.w yazo
garin yasrib (Madina) ya iske suna yi wassani
biyu a shekara, Sai manzo s.a.w yace ku aje
wadannan ga wasu nan wato ranakun sallah"
Manzo s.a.w yayi umarni a fita a ranar sallah
zuwa idi, Har wata mata tambaye sa to ni ina
son fita amma banda hijabi sai yace kije ki aro.
harda mata masu haila suna iya fita,
IDAN RANAR JUMU'A TA HADU DA RANAR EID
Manzo s.aw. idan ranar JUMU'AT Ta hadu da
ranar Eid to kana da zabi, Ba sai kayi jumu'a ba,
Amma Abu hurairah yace mu muna yi dan samun
lada mai yawa, Anyi haka dan falala garemu,
Saboda hidimar sallah wani na'iya mantawa da
sallar jumu'ar mah,
MIYAGUN DABI'U RANAR SALLAH
Ranar sallah rana ce ta farin ciki da murna,
Wadda musulunci ya ware muna a shekaru sai
biyu wato sallar azumi wato karamar sallar sai
kuma sallar layya ko kuma babbar sallah,
A lokachin sallah ana ado sosai kuma ana
ziyartar yan uwa da abokan arziki, Ko kiran waya
da dai sauran hanyoyin sada zumunta, Sai da
kash!
Ana samun masu amfani da wannan damar suna
wuce wuri har suna afkawa cikin haramun, Kusan
yazama al'adar wasu iyaye ta kyale yayan su
suyi abunda suka ga dama a ranar sallah ba tare
da taka masu burki ba,
A ranar sallah zakaga matasa musamman yan
mata sun chaba ado sun fito, Kirjin su a waje,
Bayan su a zahiri, Duk suna murnar sallah!
Wasu kuma a ranar suke fara iya shaye shaye
musamman samari, Wasu ma matasan a ranar
suke iya zina, Anan arewa cin Najeriya musan
yadda yayan mu suka tarbiyan tu da rufe jikin su
ta hanyar hijabi, Amma abun takaici zakaga wasu
ko gyale ma basu sawa,
Suwa keda laifi??
Manyan manyan masu laifi sune iyaye, Idan aka
ce iyaye ana nufin iyaye maza da iyaye mata,
Laifin uba anan shine shine ke sawo kayan to
dole kai zaka saka ido kan yadda za'a dunka
kayan dama yadda za'a sanya su, Zakaga uba
yasawo kaya kawai ya baiwa yayan, Haka bai
dace ba sam!
Ita kuma uwa ita ce ake kai dinkin agabanta,
Wajen sanya kayan ma agabanta, Amma bata iya
tsawatarwa akan abunda ke yi na kuskure, Iyaye
ku tuna Manzo Allah s.a.w yace mana "Dukkan
ku masu kiwo ne kuma za'a tambaye ku game da
abunda aka baku kiwo"
Masu laifi na biyu sune shuwagabani, Dole ne
shugabanin ku dauki matakan gyara tarbiyar
al"ummar su ta hanyar sanya idanu aka harkokin
su, mai makon haka sun bar al'umma kara zube
Na ukku sune malamai, Malamai sune suka san
hukuncin addini, Kuma sune masu wayar da kai
ta hanyar nasihohi da khudbobi da sauransu, Dole
ne malamai su zage damtse ka'in da na'in wajen
tabbatar da tarbiyar al'umma dan samun manya
gobe na kirki,
Manzo s.a.w yana cewa '"Mata ku zauna cikin
gida jen ku kada hali inyi na jahiliyah (fita
barkata)"
Sannan manzo s.a.w yakawo hadisi mai
tsoratarwa da yake cewa "Mata 2 yan wuta ne,
Ni ban gansu ba, Idan kun gansu ku tsine masu,
Sune masu sanya tufa amma basu sanya ba, Na
biyu sune masu fitar da gashi waje basu shiga
aljannah ko kan shinta bazasu ji ba, Duk da
akwai nisa daga kaza zuwa kaza"
Abun takaici wasu yan mata har dakunan samari
suke shiga da sunan yawon sallah,
Wasu kuma baso da murnar sallah basu yin
sallah suna ji ana kira amma basu zuwa, Dukka
dai muna fatar za'a gyara.
ALLAH Madaukakin sarki ya gafarta mana ya
rahama, Ya biya mana bukatun mu, Yayi rahama
ga mamatan mu.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'a 3-Zhul-Hijjah 1438 AH
Friday 25-August-2017

No comments: