Friday, 8 December 2017

HUDUBAH MAI TAKEN ILLOLIN GIBA KASHI NA BIYU

FASSARAR HUDUBAR JUMU'A
A MASALLACI NA UKKU DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A Wannan Makon Limamin Massallaci Jumu'a Na
Ukku Dake Unguwar Area2, Tsafe Sheik Sani Na
Liman'
Yayi Hudubar Sane Akan #ILLOLIN_GIBA_KA
SHI_NA_BIYU
Godiya ta tabbata ga ALLAH ubangijin halitu, Mai
rahama mai jinkai Mamallakin ranar sakamako,
Muna gode masa muna neman taimakon sa,
Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzo tsira,
ALLAH Yayi salati ga manzon rahama da
alayensa da sahabbansa da dukkan wadanda
suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Yan uwa musulmi a yau zamu chi gaba daga inda
muka tsaya a makwanin da suka gabata, La'akari
da wannan babin (Giba) yana bukatar fadaden
bayani sosai, To hakam tasa muka ci gaba daga
inda muka tsaya.
Hakika addinin musulunci ya wajabta kare harshe
da sauran abubuwan da musulunci ya shar'anta,
Musulunci ya haramta cutar da dan uwa musulmi
ta kowace fuska!
'Wata rana manzo s.a.w yana tare da sahabbai
R.a sai ya tambayesu shin mi kuka sani game da
giba? Sai sukace (Sahabbai) ALLAH Da manzon
sa ne suka sani, Sai Manzo s.a.w yace fadar
wani abu akan wani idan bayanan, Sai sukace
koda abun da kafada gaskiya ne? Sai manzo
s.a.w yace eh koda gaskiya ne, Idan kuwa ba
gaskiya bane to laifin biyu kenan (Laifin karya,
Da kuma na giba)!!
A yanzu Giba ta zama ruwan dare, Ta inda duk
wajen dakaje zakaji ana yinta ana fadar kalamai
kan wani ko wata.
ALLAH Madaukakin yana fada mana cewa "YAKU
MASU IMANI KU NISANCI ZATO DOMIN ZATO
YANKI NE NA ZUNUBI"
Hakama madaukakin sarki na cewa "SHIN
DAYANKU ZAICI NAMAN DAN UWANSA ALHALI
YANA RAYE"
Manzon rahama s.a.w ya fada mana dan
tsoratarwa game da # GIBA yana Cewa "Bani
(Bala'i) ya tabbata ga masu cin naman
dan'umansu"
A koda yaushe muna tare da masu sanya ido
akam mu domin rubuta duk abunda muke aikata
a fili ko a boye, Madaukakin sarki na cewa "KADA
KA FADI ABUNDA BAKA DA ILMI AKANSA
LALLAI DA SAURARE DA GANI DA ABUNDA
ZUCIYA TAYI DUKKAN SU ABUN TAMBAYA NE"
Hakama madaukakin sarki na cewa "DUK
ABUNDA ZAKU AIKATA KUNA TARE DA RAQIB-
ATID"
Tunda har ga masu daukar ayyukan mu tayaya
zamu yin sakaci, Mu rika fada abubuwa kan yan
uwan mu?
Wata rana sahabbai suna zaune da 'Manzo s.a.w
sai wasu sahabbai suka ce ai wane baya cin
abinci sai yaga mutane zasu ci, Kuma baya yin
tafiya sai yaga mutane zasuyi, Sai Manzo s.a.w
yace kunci namansa!!!'
Kudiba girma irin na sahabbai, Kuma abunda aka
fada halin sane, Amma manzo ya fada masu.
Jabir bn Abdullahi ya ruwaito cewa 'Wata rana
muna zaune a wajen Manzo s.a.w sai mukaji
wani wari mai marar dadi, Mai Manzo s.a.w yace
wannan warin wadanda ake konawa ne da juta
saboda sunci naman yan uwansu musulmi, Aka
turo'
Amru bn As wata rana ya tafiya tare da sahabbai
sai suka hadu da wani mushen Jaki a kan hanya,
Sai yace wa sahabbai shin kuna iya chin wannan
naman jakin? Sai suka ce a'a sai yace:Cin
naman sa yafi sauki bisa ga cin naman dan
uwanka musulmi'
Wata rana wani sahabi ya tambayi Manzo s.a.w
cewa 'Shin miye mafita daga Giba? Sai Manzo
s.a.w yace mafita itace ka kare kanka da
iyalanka daga aikata alfasha'
Bayan giba ta baki sai kuma Giba ta zuciya,
Minene giba ta zuciya??
Abunda ake cewa giba ta zuciya itace munana
zato ga musulmi..
Munana zato ga Musulmi ko kuma gibar zuciya,
Shima giba ce da ALLAH Baya yafewa! ALLAH
Madaukakin sarki na cewa "KU NISANCI ZATO
DOMIN YANKI NE NA ZUNUBI"
Hakama Manzo s.a.w yace "Kashedin ku da zato
domin yana daga cikin karyar magana"
Akwai wurare daya halatta kayi maganar mutu,
Wato an lissafa su a cikin Giba to babu laifi...
1-Zalunci-Idan an zalunce ya halatta kaje wajen
wani mai iko kamar sarki, Ko alqali ko iyaye ko
kotu dan a kwato maka hakkinka, Zakayi hakan
ne tare da maimaita duk abunda yafaru dai
dai,Aisha r.a ta ruwaito cewa 'Matar Abu sufyan
ta kawo karar mijinta ga Manzo s.a.w cewa
abincin da yake bata baya isa dan haka tana diba
ta kara dan ya ishesu, Sai Manzo s.a.w yace
mata ba komai dan haka"
Kunga anan akwai halacci mace ta kai kara irin
wannan ta mijinta,
2-Neman fatawa, Ya halarta ka baiyana halin
wani wajen neman fatawa, Misali babana ya
cuce ni, Ko yaya na ko mijina ko matata da niyar
neman fatarwar musulunci akan yadda zaka nemi
hakkin ka.
3-Neman taimako, Neman Taimako zuwa ga wani
shugaba kama ana aikata barna a wani wuri, Ana
shaye shaye ko zina, Zaka iya labartawa
shugaba cewa wane da wane na aikata, Kuma
kafadi hakan ne dan gusar da barnar da ake
aikatawa, To wannan ba'a kiranta Giba, Koda an
kirata to ba laifi akai.
4-Tsoratar da musulmi kan wani sharri, Kafadawa
wani game da wani sharri, Misali yazo neman
bincike game da aure halin wani ko wata, To
anan zaka fadi gaskiyar abunda kasani akai ko
minene babu laifi akan haka nan!
Sai dai idan anfada maka kada kuma ka koma
kafawa ita wada zaka aura ko iyayenta, Cewa
wane ai yace man kaza da kaza akanki, To
wannan kai kayi Gibar!!
Ko kuma kaga dalibin ilmi zaije wajen dan Shi'ah
neman fatawa, To kana iya neman sa kayi masa
bayani akan halinsa.
5-Mai baiyanar da barna qarara, Babu laifi kaga
kafadawa jama'a suyi hattara dashi, Musamman
idan kaga suna kokarin shige masa.
6- Shigiya, Babu laifin idan kaga ana cigiyar wani,
Ka ambaci kamar da dole sai da ita ake ganesa,
Kamar baki, Dogo, Mai qaton kai, Mai idanu da
sauransu, Amma fa da niyar kwatantawa bada
cin zarafi ba!
To a wadannan wuraren 6 kadai ne ake fadar
wani abu game da mutun!
Amma idan shugaba ya zaluncenka bai kamata
duk idan ka zauna kayita fadar saba, Kana
zaginsa alhali wanda kake fadawa baida wani iko
akan ya kwato maka hakkinka.
Hakama wasu sun dauka idan kawai kafadi
magana bayan mutun take giba! A'a Har a gaban
mutun idan kafadi magana wada bata dace kuma
ta bata masa rai to kayi gibar sa!!
Sannan kuma akwai masu gibar karamin yaro,
Suna cewa wancan yaron kaza da kaza suna
aiban tasa, Suna fadar miyagun kalamai kansa,
To duk wannan nau'i ne na giba!!
A wannan yanayin da muke ciki koda ka kare
kanka daga aikata giba, To wani na iya daukowa
yakawo yayi a gabanka, Dan haka sai a kiyaye a
san da suwa za'a zauna.....
Idan kayi gibar wani kuma baka nemi yafiyar sa,
To ranar kiyama za'a debo ladar ka a kara masa,
Idan kuma ta kare za'a debo zunubinka a zuba
masa!!!
Ya ALLAH Ya karemu daga aikata sharruka, Ka
kiyaye mu ka tsare mu, Ya ubangiji ka biya mana
bukatun mu, Kayi rahama garemu ka kyautata
karshe mu Ameen.

©®Ibrahim Rabilu Tsafe Alzamfari. 07064282182

Jumu'ah 17-Zhul-Hijjah 1438 AH
Friday 8-September-2017

No comments: